Furar Danko Page 6 Hausa Novel
Shigowarta a fusace katafaren falon gidan ya saka duk wanda ke ciki ɗagowa ya zuba mata idanu. A tsakkiyar falon ta tsaya tana harare-harare da cika da batsewa kamar wata kububuwa.
“To aunty masifatu, lafiya kika shigo kina kumbura da ga dawowa kuma?”. Ɗaya da ga cikin wanda ke a falon ya faɗa cikin taɓe baki. Kamar mai jira a taɓata a fusace ta ce, “Shi ɗan uban waye a ƙasar nan da aka aikashi ɗakkoni? Miyake taƙama da shi?…”
Kusan a tare suka shiga kallon-kallo, sai dai kafin wani ya bata amsa Dattijo mutumin dake a kujerar zaman mutum ɗaya da jarida a hannu ya miƙa mata hannu, “Kinga zo ki zauna naji miya faru Baby na?”.
“Daddy babu maganar zama a fara faɗa min uban waye shi?, dan sai na wulaƙanta rayuwarsa a gidan nan wlhy, sai yayi dana sanin shigowa gidan nan yin aiki, idan kuma bazaku faɗamin ba ALLAH duk wani ma’aikaci da ke a gidan nan yau sai ya bar gidan…”.
Sun san zata iya aikatawa, kaɗan daga aikinta kuma babu abinda Daddy ɗin nasu zaiyi saboda makahon son da yake mata a gidan. Ƴar budurwar da zata iya kai shekaru goma sha bakwai ce ta bata amsa da “Aunty Lu! Uncle Yousuf ne ya kawo shi, sabon driver ne ko sati biyu ma bai yiba fa, dan bayan wucewarki Abuja da kwana biyu ya kawo shi. Ni kaina baimin ba saboda naga yana da girman kan tsiya, ƙyawun fuskar tasa ne inaga ke ruɗarsa bayan baida ko sisi matsiyaci Mtsowww!!…..” Ta ƙarasa maganar a hankali cikin ƴar sassarfar harshe saboda hararar da dattijuwar matar dake gefen Dattijon nan ta watso mata. Wanda yay maganar farko ne a shigiwarta ya ce, “Wai miya miki ne? Bai je ya ɗakkokin ba?”.
“Bamunje ba ta masa ihu. Shiko yay tahowarsa. Kuma na faɗa mata Uncle Smart baya san ihu amma tayi” yaron nan da suke tare ya shigo yanzu ya basu amsa yana tuttura baki shi a dole yaji haushin abinda tayi. Duka ta kaima yaron ya ruga da gudu, cikin zafin rai da masifarta tace, “An masa ihun waye shi. Daddy wlhy yau idan banci uban guy ɗin nan ba babu zaman lafiya a gidan nan!”.
Cikin sauri dattijon ya miƙe yana girgiza kansa, cike da damuwa ya iso gareta. Hannunta ya kama murya a tausashe yace “Kinga Baby yi haƙuri zauna kisha ruwa ki huta. Ni da kaina ma zan ɗauki matakin dan bazan taɓa zama da wanda zai saɓa miki ba a gidan nan ko wanene shi. Har mi akai akayi wani driver banza can da zai ɓata miki rai irin haka. Haba dai cool down my heartbeat ɗin Daddynta yanzu zan nema Yousef ɗin ma ya dakatar da shi”.
Yanzu kam babu musu ta yarda ta zauna ɗin, sauran yaran duk sai suka shiga taɓe baki. Hakama mamansu tsaki ta ɗan ja a hankali tama miƙe tabar falon. Shiko Daddy ko’a jikinsa ya shiga lallashinta da kalaman ban haƙuri masu sanyaya zuciya gareta tamkar itace uban shine ƴar. Ruwa ma da aka saka mai aiki kawowa da kansa ya tsiyaya a kofi ya bata a baki. Kaɗan tasha ta kauda kai tana faman huci. Sake matsota yay jikinsa ya kwantar mata da kai a kafaɗarsa yana shafa bayanta. Ajiyar zuciya ta dinga saukewa kamar wadda ta fito daga tarnaƙin yaƙin duniya, sai kuma zuwa can ta ɗan ɗago. “Daddy kar ka kira Uncle Yousuf ɗin ban san a sallemsa yanzu, sai na rama abinda yay min. Aikin sati biyu zai min ALLAH sai na wajiga rayuwarsa sannan na masa korar da kare ma sai ya fisa daraja”.