Auren Shehu Hausa Novel Page 1
Kwance ya ke a rigingine kan ciyayi irin wannan ciyayin da ake kira “carpet grass” Hannayen sa biyu tallabe da ƙoƙon kansa, cikin nazari yake duban taurarin da ke jere reras suna sheƙi bisa sararin samaniya.
Babban lambu ne mai ɗauke da ɓangare biyu, ɓangaren bishiyoyin ‘ya’yan itatuwa, bishiyar mangoro, gwaiba, yazawa (cashew) da dai sauran su, sai kuma ɓangaren da ke ɗauke da kujerun hutawa. In ka ɗauke kukan tsuntsaya babu sautin da ake ji kasancewar dare ya fara tsalawa, kusan ƙarfe biyu ne.
Sanye yake cikin rigar saƙa irin na fulani, kan sa ɗauke da rawanin da ya zaga har kewayen fuskar sa hakan ya sa fiye da rabin fuskar shi ɓuya. Kasancewar shi na daya daga cikin masu gadin daddare na gidan, kusan kullum ya kan kai biyu a nan cikin lambun, yayi kwanciyar sa ya na mai nazari, hakan ba ƙaramin nishaɗi ya ke saka shi ba.
Gefan sa ƙatuwar sanda ce wacce ake kira da gora, ta korar shanun sa ce duk da kuwa rabon shi da rugar su wacce ake kira “Rugar Shehu” ya kusa shekara.
Jin dirar mutum tare da haushin karnukan gidan lokaci ɗaya ya sanya shi yin zumbur ya tashi zauna ya na mai duban in da ya ke kyautata zaton mutum ne ya diro cikin gida. Jin shiru babu wani motsi sai na haushin karnuka ya sanya ya tashi tare da jan sandar gorar shi kai tsaye bakin bishiyar da ke kusa da katangar lambun ya nufa, idan ya ke kyautata zaton koma menene ya diro nan ne hanyar shi.
Tun dirowar ta take ƙoƙarin janye niƙabin ta da ya maƙale jikin reshen bishiyar da ya mata tsani. Ƙoƙari ta ke iya ƙarfinta don ta ga ta ciro amma ina, gashi ta san mutukar ba ta samu ta shige ciki ba lalle masu gadi za su kama ta yau, don kuwa haushin karnukan yau ya fi na kullum. Jin ta ku a bayan ta ya sanya ta juyawa da sauri, ganin ya ɗaga sanda ya na shirin runtsuma ma ta aka, ta runtse idanu ta na mai faɗin
Cak ya tsaya, hannun shi na rawa tsabar firgici na ganin kyawun halittar Allah, tabbas kyau dai babu irin wanda bai gani ba a Rugar su, amma sam bai taɓa ganin wacce ta firgita shi ba kamar wannan halittar da ke gaban sa.
Fuskar ta ya bi da kallo, wanda rashin niƙab ya ba shi wannan damar, domin kuwa jikin ta rufe ya ke da hijabi tun daga sama har ƙasa. Kamar yanda ya ke nazartar taurari haka ya tsinci kan sa cikin nishaɗi yayin da ya shiga nazari akan fuskar ta.
Baka ce, irin wannan bakin mai shek’i kamar jikin tarwaɗa. Tsayuwar hancin ta da ya zo dab da ƙaramin bakin ta ba ƙaramin ƙarawa doguwar fuskar ta kyau yayi ba……
Jin shiru ba ta ji saukar gora kan ta ba ya sanya ya ta buɗe manyan idanun ta, hakan ba ƙaramin sake rikita shi ta yi ba ganin fararen idanun ta bisa kan shi har sai da ya ɗan ja da baya ya na mai tasbihi ga ubangijin sa, domin ya tabbatar wannan halittar da ke gaban shi ba mutum ba ce.
Ta na mai duban shi cike da tsoro musammam ganin mutum mai faɗi da tsayin da tun da ta zo duniya ba ta taɓa ganin irin shi ba, daɗin daɗawa gashi yanayin shigar shiri irin na waɗannan mutanen da suka saka Nijeriya a gaba ko kuma Fulani masu garkuwa da mutane, wannan tunanin tare da jin taku da haushin karnukan da ya ƙaru, wanda hakan ya tabbatar ma ta masu gadin sun kusa shigowa lambun ya sa ta sakin niƙab din ta na mai ɗage hijabin ta yanda za ta sami damar sauri, ta yi amfani da damar gushewar tunanin mutumin da yayi kasake ya na duban ta, ta bi hanyar da zai sada ta da kitchen da sauri, hannu na rawa ta ke ƙoƙarin fidda ɗan mukulli da ta ɓoye cikin dan wando da ke sanye jikin ta.
Har tuntuɓe ta ke garin waige domin tabbatarwa ba ya biye da ita.
Allah ya taimake ta ƙofar ya buɗu, kasancewar ta sababbiya a harkar, cikin sanɗa da lalube ta ke tafiya domin wutan lantarkin kitchen din a kashe ya ke, sai dai hasken farin wata da yake ratsowa ta taga. Ba ta tsorata ba sai da ta jiyo muryar masu gadi daga cikin garden, ta na mai roƙon Allah ya sa ba asirin ta ba ne ke shirin tonuwa ba, ta bi ta falo ta shige ɗakin ta cikin rawar jiki. Dan tun da take fitar dare ba ta taɓa shiga tsaka mai wuya kamar na yau ba.