Daudar Gora Book 2 Page 32
Tana tsaka da ɓarawon barcin da ya sace ta bayan ta idar da sallar da take tsaiwar yi duk dare domin miƙa kukanta ga UBANGIJI taji kamar numfashinta na fita a fisge, firgigit ta farka da ƙoƙarin kai hannunta saman hancinta, sai dai aikin gama ya gama dan ya riga ya shaƙa mata abinda ke cikin handkherciff ɗin. Duk yanda taso sake yunƙurawa hakan ya gagara sai ma jikinta dake saki baki ɗaya. Daga haka bata sake sanin inda kanta yake ba.
Jikinsa na ɗan ɓari ya sakata a babbar jakar hanun nasa tare da zuge zip ɗin. Bai tsaya ɓata lokaci ba ya saɓeta kasancewarsa ƙaƙƙarfan mutum babu alamar da zai tabbatar maka mutum ya ɗakko. Gashi dama Iffah ta rame sosai duk da dama ba wata mai jiki bace can. Sai dai kuma duk da hakan ƙarfin haline kawai irin na masu busashshiyar zuciya dan sumar da itan da yay jikinta duk ya saki ta sake nauyi. Sai da yay musu sallama da sanar da su ya kwaso kayan dattin wajenta ne bisa umarnin Tajwar Eshaan sannan ya wuce.
Kamar yanda al’adar take duk wani hadimi da karfe huɗu tayi zai fara gudanar da aikinsa in har yana cikin hadimai masu kula da tsaftar masarautar. Musamman ma masu shara da tsaftace irinsu garden barga da sauransu. Yauma hakance ta kasance, hadiman duk sun tashi domin kama ayyukansu, kowa ƙoƙarinsa ya kammala kafin sallar asubahi. Swimming pool ɗin garden ɗin gabashi dake kamar ta bayan
sashen Shahan-shan gab, babban swimming ne da masu aikin tsaftace ruwan cikinsa suka kasance har su huɗu, kowace kusurwa da mai gyarawa. Sukan saka raga domin tace duk wani datti daya shiga ciki, tare da sake ingantashi ya fita fes yana bada kalar blue mai ɗaukar ido ko daga nesa. Aikinsu suka fara a nutse, tare da yima juna magana jefi-jefi, can wanda ke a bangon yamma ya zabura tare da ƙwala ƙarar da tai amsa kuwwa zuwa kunnen duk hadiman dake aikinsu suma gab da wajen. A take ƴan uwansa sukayi kansa suna tambayar lafiya. Jikinsa na rawar karkarwa yay musu nuni da cikin swimming pool, kallonsu suka maida wajen zukatansu na dukan tara-tara, dan basu mance tsautsayin da ya taɓa faruwa ba da har yay sanadin rasa ran Miran Nayyar (ƙani ga Marigayi Tajwar Haysam). A tare suma suka zabura jikkunansu na sake shiga mazarin rawa.
“Tabbas mutum ne mun shiga uku!!”.
Wani ya faɗa a cikin sauran hadiman da ihun wancan ya jawo hankalinsu. Sake daburcewa duk sukayi, an rasa wanda zai yi hoɓɓosan kai agaji ko neman agajin, gashi motsin da suke gani anayi a cikin ruwan ya fara lafawa alamar wanda ke cikin yana sake ƙasa. Wani da yazo kusan a ƙarshe-ƙarshe ne ya zabura zai afka, da sauri wani ya rikoshi yana girgiza kansa. “Wannan bashine mafita ba, ayi azamar sanar da jami’ai gudun kar mu aikata kuskure tunda bamu san wanene ba. Duk wanda ya kai shekara arba’in da biyar baya anan yasan miya faru a dalilin irin wannan kuskuran”. Sun gamsu da jawabinsa, duk da wasu labari kawai sukaji dan sannan girmansu bai kai ba, wasu ma ba’a haifesu ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci jami’ai suka iso wajen, hakama mazan masarautar dake ƙoƙarin tafiya masallaci sallar asubahi. Rashin sanin wanene a ciki yasa shugaban jami’an ya hana a shiga kai tsaye, sai dai tuni an gama dasa na’urorin da zasu iya fiddo koma wanene. (Dan tun rasa Miran Nayyar da masarautar tayi Tajwar Abdul-majeed ya tanadar da na’urorin domin tsaro). Tayi ƙasa sosai ga swimming pool ɗin da girma sosai, cikinsa kuma anyi style kamar wani sashe-sashe da suffar ado. Hakan yasa akaja lokaci mai tsawo kafin a samu nasarar samota, zuwa lokacin har an idar da sallar asuba.
Kasancewar tsirarun mutane da Tajwar Eshaan ne kawai suka sami damar yin sallar asubahin ya bada mamaki har Tajwar Eshaan ɗin yasa akai tambayar ko wani abu na faruwa ne haka?. Waɗanda suke a masallacin duk basu sani ba, dan haka suka tabbatar da babu komai, sai dai ko makarace ta kawo hakan. Baiji ya gamsu ba, amma sai bai musa ba ya miƙe ya fito Sayeed Fayzul-haq da ya zama kamar amintaccensa yanzu biye da shi. A falo Sayeed ya dakata, shi kuma ya nufi bedroom domin shiryawa ya shiga grm. Dai-dai nan kiran waya ya shigo ta landline.