Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 113

Sponsored links

Ita kuma kasancewar zuciyarta a kusa take tana musu ta’aziyya tana share hawaye da handkherciff. Sai hakan ya ƙara mata kima a idon iyalansa. Yayinda ƴan uwansu kuma da basu san komai na ke jin zafin ganin Iffahr da fassarashi matsayin leƙen wani asiri dan a yanzu wasu a cikin ahalin masarautar su kuma suna ma Iffah kallon wata ƴar kaɗafin Tajwar Eshaan ce tunda har ta tsira daga kisan gillarsa.

Kamar yanda Iffah tai tunani labarin zuwanta sashen Sayeed Khairul-Bashar ta’aziyya har ya isa kunnen surukarta dama na jikin Tajwar Eshaan irinsu malikat

 

 

Haseenat da su Daneen Ammarah. Dan tana fitowa kiran Daneen Ammarah ya shigo wayarta. Bata ɗaga ba, aka kuma sake kira nan ma dai ta share kamar bataji ba. Sai da ta koma sashenta da kusan mintuna goma sannan tai kiran Daneen Ammarah ɗin back. A bugu biyu ta ɗaga, Iffah ta taɓe baki cikin rashin damuwa tai sallama da fara gaishe ta. Da kulawa Daneen Ammarah ta amsa. Iffah na jiran jin ta mata batun fitarta sai Daneen Ammarah ta jeho mata tambayar da bata da alaƙa ma da fitar.

“Ibnati na kiraki ne akan Abni, shirunsa na tadamin hankali matuƙa, gashi yana ƙara harzuƙa mutane ƙasa, kinga dai yanda ƙasar nan ke sake rikicewa. Mu dukanmu mun nemesa a waya amma bamata shiga, na fara zargin anya ma yana cikin masarautar nan?”.

Murmushin takaici Iffah tayi, amma a zahiri sai ta danne ta fara magana cikin kwantar da murya. “Wannan shine tunani na nima Mamy, sai dai ban san yanda zanyi ba ganin ku manya bakuce komai ba.”

“Shirun na dole ne Ibnati, bazaki gane babbar sarƙaƙiyar dake cikin masarautar nan ba ne. Amma tabbas akwai matsala, akwai kuma gagarumin al’amarin dake ɓoye amma yana son bayyana kansa a wannan gaɓar…..”

Cikin zumuɗi Iffah tace, “Mamy minene shi dan ALLAH?”.

“Humm Fareedah kinyi ƙarama da yawa ba yanzu ba. Ke dai kawai abinda nake so da ke shine ki taimaka ki bincika min idan Abni yana a gidan nan…”

“To Mamy, amma dai zaiyi wuya tunda kunce idan yana cikin damuwa kulle kansa yakeyi baya kuma sauraren kowa. Sai nake ganin ni taya zai saurare ni”.

Murmushi Daneen Ammarah tayi mai sauti. “Rashin saurarenmu bashi ke nufin kema bazai saurareki ba Ibnati. Ke dai gwada sa’arki mu gani”.

Iffah dai ta jita ne kawai, amma sai bata sake musawa ba sukai sallama…..

Miran Jasim ya sauke wayar dake a kunnensa bayan gama sauraren abokin wayar tasa, yanda fuskarsa ta canja daga farin cikin dake shimfiɗe a kanta kafin wayar yasa Miran Arshaan sake maida hankalinsa garesa. “Wani abu ya sake faruwa ne?”.

“Zai dai faru”.

Cewar Miran Jasim ɗin a fusace yana miƙewa. Miran Arshaan da maganar ta dakesa ya miƙe zumbur shima. “Ban gane mi kake son cewa ba Jasim Akh?”.

Kamar bazai tanka masa ba sai kuma yaja kakkauran tsaki. “Harun Al-rashid ne dai akan waccan maganar banzar ta ranar, duk yabi ya tashi hankalinsa yana cigaba da damuna nima, tun abin bai tasiri a raina ba har ya fara, wai Barrister da suka bama aikin can kan ɗan iskan can ne ke cigaba da musu bayani dai kan Barrister Abdallah bai mutu ba dai da gaske.”

“Wai suna nufin shi ya tabbatar da hakan kenan?”.

“Abinda ke cazamun kai kenan, na rasa wane shirme ne kuma hakan? Taya wanda bomb ya tashi da shi ace bai mutu ba?”.

“To amma fa kuma maganarsu fa abin a duba ce Jasim Akh. Dan koni naji shakku a randa bomb ɗin nan ya tashi amma jami’an tsaro suka tabbatar babu wani alamar an rasa rai……”

“Amma shine kai shiru?!”.

Miran Jasim ya katsesa a zafafe. “Mi kake so nayi bayan wanda nayi to? ina son ka tuna tun a ranar na kawo maka wannan zancen amma ka nuna min cewar zata iya yuwuwa ƙarfin tashin nakiyar ya cillashi wani waje ne shiyyasa basu gansa ba. A kuma shekaran jiya da suka kawo maganar na kuma ƙoƙarin maka nuni ka kalli zancensu a shirme”. Shima Miran Arshaan ɗin ya karɓa masa a nasa zafin.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button