Daudar Gora Book 1 Page 61
Barrister na ƙoƙarin shiga layin gidan Abu Moosa wata baƙar mota na ficewa. Babu wanda ya damu da ganinta a cikinsu, suka ƙarasa kutsa kai har ƙofar gidansa. Ganin gidan rufe daga nesa baisa sun kawo wani abu a ransu ba duk suka fita. Abu Zainab ne ya ƙarasa har jikin ƙofar. Kansa tsaye ya kai hannu ya fara knoking, amma har tsahon mintuna biyu babu alamar motsin mutum.
Juyowa yay ya ɗan kalli su Kaka dake kallonsa. Cikin sarewa ya girgiza musu kai. “Banajin fa akwai mutum a gidan nan, dan babu wani motsi”.
“Kara dai bugawa”.
Cewar Barrister cikin bashi ƙwarin gwiwa. Kai Abu Zainab ya kaɗa ya cigaba da bugawa, maimakon a buɗe nan sai ƙofar makwaftansu ce ta buɗe. Wani matashin saurayi ya fito. Abu Zainab ya maida hankalinsa garesa suka gaisa. Kafinma ya tambaya saurayin ya bashi amsa.
“Ai banajin akwai kowa gidan nan. Saboda yanzu babu jimawa matar gidan aka ɗauke a mota harda ƙaton akwati”.
Da mamaki Abu Zainab ya ce, “Kana nufin yanzun?”.
“Eh, dan banajin sunma rufa minti goma. Ta kuma yima mahaifiyata sallama akan zata koma garinsu ne. Harma mukayi mamakin hakan ganin duka rasuwar mijinta bai wuce kwanaki goma sha biyar ba”.
Godiya Abu Zainab yay masa jiki a saɓule ya koma gasu Kaka. “Waifa kunji babu jimawa tabar anguwar nan. A yanda tacema makwaftansu ma ta koma garinsu ne”.
Wai ni naga sai faman moso kike, kinma kasa bani labarin yanda kukai da Akia akan zancenmu na jiya. Kuma naga wucewarku ke da ita ɗazun zuwa sashin Mamma (Malikat Haseena)”.
Cike da zolaya ta ɗan hararesa. “Ko kuma dai ƴan leƙen asirinku sun sanar maka ba”.
“Leƙen asiri kuma? Haba sai kace dai ku. Kudai matan masarautar nan ne dai da baƙwa iya rayuwa sai dai ƴan leƙen asiri. Amma mu maza miya haɗamu da wani leƙen asiri kamar marasa aikin yi”.
Ta ɗan dara kaɗan da taɓe baki. “Muma ɗin ba kowa ne yake hakan ba kamar yanda kuke zargi. Niko waya dameni a daular nan dahar zan damu da saka wani bibiyarsa. Ko lamarin Zaki addu’a ce tamu a garesa kawai”.
“To ALLAH yasa hakan. Yaya zaman naku ya kasance?”.
“Zama an samu nasara. Dan inama Akia bayani a take ta amince, ta kumace muje sashen Mamma itama muji ta bakinta. Alhamdullah sai aka dace itama zancen ya ƙayatar da ita. Na taƙaice maka zance a yanzu haka ma mun zauna da ita yarinyar. Insha ALLAHU zuwa gobe ma zata koma sashenta. Sai dai abu ɗaya ne fa Mamma bata amince da shi ba”
“Sake kai wata Zawjata-almilk turakarsa. Acewarta za’a ƙara jinkirtawa aga abinda yarinyar zata samo. Sannan za’a sakema duka Zawjata-almilk ɗin sabon horo akan kasancewar su Zawjata-almilk a wannan karon”.
(Wata sabuwa kenan, wannan tsinanniyar tsohuwar ko) ya ambata a zuciyarsa. A fili kam fuskarsa ya kawata da sabon murmushi da faɗin, “Woow wannan tsarin yayi, shiyyasa Mamma ke daɗa birgeni. Hakan ma wani mataki ne da zai taimakemu matuƙa. ALLAH kuma yasa mu dace”.
“Amin dai Abu Harith. Dan gaskiya a wannan gaɓar ina tsoron a ce abinda ya faru ya sake maimaita kansa. Saboda zuwa yanzu hankalin manyan ƙasashen duniya ya fara dawowa kan ƙasar ruman. Dan ma ana shakkarmu ne da tuni wani zancen ake ba wannan ɗin ba. ALLAH dai ka bayyana gaskiya ka kuma wanke wanda ake neman disashewa saboda son zuciya”.
“Amin Meera. Amma ko yanzu ɗin ma akwai abinda baku sani ba. Shahan-shan na ɓoyewa ne kawai dan karya tashi hankalin kowa. A wata mai kamawa shugabannin manyan ƙasashe bakwai na africa zasu kawo ziyara ƙasar ruman. Bisa jagorancin shugaban ƙasar Nijeriya, bama raba ɗayan biyu akan wannan al’amarin ne kuma”.
“Ki kwantar da hankalinki, dan ALLAH kuma kar kowa yasan wannan, dan na sanar miki ne kema saboda na yarda da ke”.
Badan hankalin nata ya kwanta ba ta jin jina masa kanta kawai. Cigaba da kwantar mata da hankali yay cikin kwantar da murya har barci ɓarawo ya kwashe ta. Sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sannan ya zare jikinsa cikin sanɗa ya fice zuwa ɗayan ɗakin dake jikin wanda suke kwance da waya a hannunsa……
Dukan matakin shawarar da Sir Fawzan ya bata shi tabi, dan tunda sukai bankwana da Daneen Ammarah tai shirin barci ta sakama ƙofarta key. Ta fara da buɗe Watsap, sannan ta lalubo number Ajmaal. Cikin sa’a kuwa yana online, wani farin ciki ne ya ratsata. Taja kakkauran numfashi da godema ALLAH.
_Assalamu alaikum_
Ta fara turawa da fatan samun amsa zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Tsahon mintuna kusan goma babu alamar zama a buɗe saƙon. Sake tura sallamar tayi a karo na biyu. Ta dasama wayar ido kamar mai irgan fitan numfashinta. Kamar a mafarki taga an buɗe, tai kasare tana jiran taga an amsa sai dai shiru har kusan wasu mintuna goman. A yanzu kam zuciyarta ta sosu, dan duk yanda take buƙatar abu ga mutum ta tsani a wulakantata. Ta cije lips da ƙarfi tana danne fushin dake son mata tasiri.
_Wa’alaikissalam_.
Aka amsa mata a bazata. Nannauyar iska ta furzar, itama ta buɗe saƙon ta share. Da ƙyar ta iya danne zuciyarta mintuna bakwai suka cika.