Daudar Gora Book 1 Page 13
Cikin girmamawa Babiy ya gaidashi duk da zasu iya zama kusan sa’anni da shi. Shiko ya amsa yana hura hanci irin na masu dama ta mulki a hannu. Umarni ya bama Babiy akan ya ɗanɗana zumar, Babiy da yasan babu wani abu na razani ko shiga dogon tunani kafin ɗanɗanawar kansa tsaye ya kai hannu ya ɗauka cokali dake bisa tire a hanun hadimin dake biye da dattijon nan. Tunda dama haka ba sabon abu bane garesa duk sanda ya kawo sai ya ɗanɗana ɗin. Tulun farko ya kwancema baki kasancewar a ɗaure bakin yake da ganyen ayaba, yasa cokalin nan ya ɗibo zumar da bismillah ya nufi bakinsa………✍
………Haniniya da ƙarar takun sawayen wani farin ingarman doki ta saka Babiy sakin cokalin da yake shirin kaiwa bakinsa ya miƙe domin ceton kansa kamar yanda Dattijo nan da hadiman dake tare da su suma sukai nasu waje. Tuni tulunan zumar uku da Babiy ya kawo sukai nasu gefe suma, gaba ɗaya zumar ta kelaye a wajen. Cikin daka tsawa dattijon nan ke duban hadiman da suka biyo dokin domin kama shi…
“Wane mara hankalinne yay sakacin daya kunce?”.
Su dukansu jikunnansu rawa yake, cikin ƙarfin hali shugaban hadiman dake kula da barga ya zube ƙasa yana mai girgiza kansa. “ALLAH ya ƙara maka tsahon rai an gama masa wankane za’a maidashi na rantse maka”. Dattijon ya cije baki mai nuna alamar takaici, “Na baku mintuna goma kacal ku madashi shashashu kawai”. Miƙewa hadimin dattijon yayi cike da girmamwa dan dama sauran sunata ƙoƙarin ganin sun kama dokin ne, bama su kaɗai ba hadiman da yawa sun ƙaru saboda bahagon dokine da babu ma iya controling nashi sai Tajwar Eshaan. Horarran doki ne daga horonsa, da abinsa ya dawo ƙasar ruman, dokin yafi kowanne doki tsananin ƙarfi a masarautar. Shiyyasa idan har sukai sakaci ya ɓalle kowa sai ya jigata kafin a kamashi da ƙyar,kafinma kamashin sai an samu wanda sukaji raunika da yawa. Akwai randa irin haka ta taɓa faruwa baƙaramin jigata mutane yay ba harda masu karaya a hadimai, kuma duk iya wahala da jigata babu wanda ya iya kama dokin har duhun magriba yayi dan da yamma al’amarin ya faru. Kowa yayi laushi an rasa in za’a kama sai ga Tajwar Eshaan ya fito sallar magrib, abu mafi ban mamaki daya saka masarautar yin shiru na sakanni uku kiran sunan dokin kawai yay sai gashi gabansa, ya girgiza jikinsa tare da yin haniniya sannan ya koma kan ƙafafunsa ya tsaya cak tamkar bashiketa jigata mutane da hargitsa wajen ba. Wannan abun mamaki ya saka dukan hadiman da suka zube saman gwiyawunsu kawunansu a ƙasa a lokacin kasa haƙuri sai da suka saci kallon dokin dama Tajwar Eshan ɗin da hirami daya yafa a kansa ya rufe rabin fuskarsa…..
A ɓangaren Iffah gaba ɗaya idanunta sun kasa barin ƙofa, babban burinta kawai dawowar Babiy taji zuma ta isa hanun Shahanshan. Sai dai shiru kakeji har akai sallar juma’a bai shigoba. Ko abinci babu yanda Ummu batai da ita tai zaman ci ba amma taƙi, Hanash ma sai da ya mata maganar tazo suci kamar yanda sukanyi duk juma’a tunma su Fariha nada rai amma tace batajin yunwa. Ƙyaleta sukai dan sun kasa gane minene ya hanata nutsuwa waje ɗaya.
Babiy bai shigo gida ba sai bayan sallar la’asar. Azabure Ummu ta miƙe tana kallonsa. “Innalillahi wa inna’ilaihirraji’un. Abu Hanash haɗari kayi?”.
Kai Babiy ya girgiza mata yana kaiwa zaune da ƙyar. “Ke dai bani ruwa na fara sha”.
Kafinma ya rufe baki Iffah da itama jikinta ke rawa ta kawo masa ruwan, dai-dai nan Hanash ya fito daga ɗakinsa cikin shirin fita ƙwallo. Shima a ruɗe yay kan Babiy ɗin yana jera masa tambaya. Babiy ya ajiye kofin ruwan yana mai kallonsu gaba ɗaya. “Kunga ku kwantar da hankalinku babu abinda ya faru daga masarauta ne. Wani bahagon dokine fa ya kunce al’amarin tamkar yaƙi, hatta da zumar dana kai ba’a mora komai a cikinta ba ma”.
Ummu da Hanash suka shiga jera salati, yayinda Iffah taji wani ƙududun baƙin ciki ya tokare mata maƙoshi, hakan na nufin bataci nasara ba sai ma Babiy daya dawo da raunika. Jitake kamar taga Tajwar Eshaan gabanta ta shaƙesa da hannayenta har sai ya bar duniya saboda tsabar tsanarsa. Har Hanash ya gama yima Babiy dressing ciwukan batace komai ba, daga ƙarshe ma ɗaki ta shige ta shiga faman kaikawo na tunanin abu na gaba. Dan tayi alƙawarin bazata taɓ haƙuraba sai ta kai *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed_* ƙasa zata samu salama game da rasa ƴan uwanta.
Sam a wannan dare Iffah bata wani isashen barci ba saboda ƙullawa da kwancewa aka shiri na gaba. Abinda ta gama ƙullama zuciyarta yasata shirin fita a gidan da hantsi da dalilin cewar zataje wajen Ikram duba mamanta bata da lafiya bazata jima ba. Ummu tayi kamar bazata barta ba amma taita mata magiya harta amince da sharaɗin karta jima, kuma dolene ta rufe duk jikinta. Ta yarda da hakan saboda tana son fitar. A gurguje tai shirin fitar, tare da lalubo wayar Arfa a cikin kayansu. Koda ta haɗa batteryn ta kunna tayi sa’a tanada caji, dan haka ta loda number da take buƙatar kira tana mai addu’ar ALLAH yasa akwai kuɗi ma. Addu’ar tata bata amsu ba, dan haka ta tura wayar cikin jikinta bayan ta kashe sannan ta fito tai sallama da Ummu ta fita bayan ta amsa kuɗin taxi. Sai da ta fito daga cikin anguwarsu gaba ɗaya sannan ta tsaya ta sai kati, koda ta loda sai ta sake gwada kiran lambar ɗazun. Cikin sa’a kuwa aka ɗauka, jimm sukai su duka kafin ta katse shirun da sallama. Daga can aka amsa a noƙe alamar rashin sanin dawa ake tare. Fahimtar hakan ta saka Iffah bashi amsa tunkan yay tambayar.
“Sir! Kana magana da Fareedah bint Zayy……”
“Serious?”.
Ya faɗa cikin katseta da alamar zabura tun kan ta ƙarasa faɗa. Baki ta ƙyaɓe a ƙasan zuciya tana jan tsuka, a zahiri kam sai ta saki murmushin da har sautinsa ya kai cikin kunnensa. Cike da sake ƙanƙan da kai tace “Tabbaci Sir. Ina buƙatar muhaɗune yanzu yaya za’ayi?”.
“Kai! Iffah! Ke ɗin dai?…”
“Bazan samu damarba ko……?”
Cikin sauri ya katseta. “No ba nufina kenan ba, kawai na shiga al’ajab ne. Amma bara na ajiye tantamar tawa gefe dai. Inaga zanzo na sameki gida kawai…”
“A’a sir”.
“Miyasa?”.
“Ba buƙatar hakan, mu haɗu kawai”.