Bakon Lamari 18
Hassan ne ya fito yana wa Ummah magana wanda shima ta koma kanshi da faɗa kamar zata dake shi ya girgizakai kurum yay ficewar shi daga gidan.
Haka Ummah ta ƙaraci faɗace faɗacen ta tayi ɗakinta duk abun duniya ya isheta.
Minti Goma Hassan ya dawo da baƙar leda a hannunsa ya faki Idanu ya faɗa ɗakin Amatullah wadda ta buɗe shi yanzu ganin Hassan yasa ta saki ajiyar zuciya.
“Yaya kiyi haƙuri da halin mahaifiyar mu Ɗazun nan ta gama ce mana kada wanda ya taimakeki Wanda ni kuma naga hakan ba daidai bane yanzu kike buƙatar taimako Ga wannan kici zan fita aiki inna dawo zan tawo miki da Kuɗi”
Da yake yana jan adaidai ta sahu.
Amsa tayi tana masa godiya bayan ya miƙa mata ya fita.
Ta buɗe ledar Bread ne da indomie bata ci da yawa ba ta naɗe ta aje agefe ta rafka uban tagumi.
Ameerah ce ta faɗo gidan a gigice tana kiran Amatullah.
Nana ta dubi Ameerah da rashin kunya tace.
“Tana ɗakin icce Kuma sai na gayawa Umma kin shigo mana gida”
Ameerah bata kula Nana ba tayi ɗakin ta tura tana cewa.
“Yanzu naji baƙin labari Bakin Baffa wai jiya Alhaji ya buɗe miki Ƙofa Kin dawo gida ya Allah yasa ba auren kine ya mutu ba”
Ameerah ta faɗi cikin Kuka.
Tagumi Amatullah tayi tana share hawaye.
“Ameerah wallahi Imran yace na dawo gida Jiya haka na tawo nan cikin dare Ga Ummah taƙi fahimta ta”
Duka ta kwashe yadda sukai da Ummah ta gayawa Ameerah wadda take kuka kamar itace Amatullah Ɗin Rungume juna sukai suna Kuka.
Ameerah tace mata.
“Allah ya kawo Miki mafita Amatullah haƙiƙa Kin bani tausayi ina ma ina da dama dana taimaka Miki amman Ba komai taso Muje gidan su Nafisa akwai wata mata dake kai ƴan aiki koza ta samar Miki yafi miki wunin gidan Kya rage takaici dan koda kin zauna takaici ne zai kashe ki”
Haka suka tashi suka Fita gidansu Nafisa ƙawar suce Nafisan dan haka daga nan gidan su Nafisan suka ɗauketa suka tafi gidan matar wai ita sabuwa mai kai ƴan aiki.
Ameerah ce taima sabuwa bayani wadda sai da tayi ƙwallah dataji halin da Amatullah ke ciki tai kuma Ala wadai da halin Ummah.
“Bani da aiki mai tsoka a ƙasa amman akwai wani anan Jambulo Gidan Alhaji Idi mai kwano Idan zaki anjima sai na kaiki gidan Tun safe ne ake zuwa har Sai magari ba gida ne Gidan karamci”
Da sauri Amatullah ta ɗago tana cewa.
“Zanyi mama nagode”
Haka suka gama magana da sabuwa sannan suka tawo gida Ameera nacewa Amatullah zata na riƙe mata Iman har ta dawo amman sai ranar da ba makaranta.
Koda ta koma gida Ummah sai da tai mata tas akan ta fita yawon zubar mata da mutunci agari.
“Ummah Kince ba zaki bani ci da sha ba to zan zauna Yunwa ta kashe Ni shiyasa na ɗauki Ameerah muka fita yawon Neman aiki”
Jin furucin hakan yasa Ummah ɗaukar mayafi taje ɓangaren su Ameerah dan ta ciwa Ameerah Mutunci sai dai bata sami Ameerah ba sai ƙannenta wai Ita sunje airport dasu Surayya zasu ɗauko AHMAD sai anan Ummah taji ma maganar zuwan nasa.