Tabarma Kashi 5
Ɗaya daga cikin yammaci ne wadda ke jerin yammacin da albarkar ubangiji ke sauka daga sama zuwa ga bayinsa dake rayuwa a doron qasa sanadiyyan haduwar hadari da samuwar saukan ruwan
sama,kama daga mutane dabbobi aljannu da sauran halittun dake qarqashin ruwa saman bishiyu da sauran bingiren da idanuwa basa iya ganinsu,raunin hankali,nakasa da kasawa irin ta abun halitta ya yiwa hankali shamaki da fahimtar wanzuwar wadan nan halittu dake kewaye damu masu tarin yawa,wanda kowanne yana qarqashin kulawa da tasarrufin ubangiji,bai gaza ba dai dai da qiftawar idanu wajen rabon arziqi ga bayinsa,da kuma isarwa da kowanne bawa gwargwadon rabon da ya kasance mallakinsa ne.
A dai dai wannan lokacin,cikin qawataccen gidan abincin,muhalli me daukan hankali,sanyaya zuciya da bawa ruhi nutsuwa, sakamakon yadda aka qawata wajen da wani irin tsari mai ban sha’awa da burgewa,kwatankwacin yadda zai ja hankalin abokan kasuwanci suji basu qagara ko gajiyawa da zuwa kashe yunwa da qishirwarsu a wajen ba.
Saman kujerun dake zagaye da teburan dake jere a wajen bisa tsari na rukuni rukuni,daga hannun damanka bayan ka shigo wajen zaka iya hangenta
Kyakkyawar matashiya,fara sol data mallaki wani irin hasken fata,irin farin da ko makaho ya shafa yasan natural ne,wanda ya cakuda da tsantsar kulawa tsafta da kuma hutu,yake kuma nuni da zurfin gogewa da wayewa da mamallakiyar fatar ke da shi.
Idan har kayi hanzari ko azarbabi zaka iya kiranta da doguwa,saidai kaso me yawa na tsahon nata babu shi sakamakon murjewar da jikinta yake dashi da ya shanye tsahon ya maidashi moderate. Wasu irin manyan idanu gareta amma kuma a russune suke,wannan ya boye girman idanun nata,kai tsaye ba zaka ce suna da girma ba har sai idan taso fidda girman nasu ne. Siraran labbanta masu kalar pink sun dace hancinta mai tsaho da tudu wanda ya hade da kwantacciyar eyebrows dinta dake bisa tsari kamar an zanata.
Sanye take da wata tattausar exclusive atamfa da bata tara tarkacen kaloli ba,hatta da zanen jikinta bai wuce dayan biyun ba,kalolin da suka dace da yanayin jikin da aka raɓawa atamfar,dinkin doguwar riga ne daya bude sosai daga qasa,daga sama kuma ya zauna mata cas kamar a don ita aka halicci atamfar dama dinkin gaba daya. Ta lullube kanta da wani madaidaicin mayafi wanda yayi mata aikin mayafin dama dankwalin da bata damu da daurashi ba,sai kwantaccen gashin daya kwanta daga gaban kanta,wanda duk bayan minti daya zuwa biyu take sanya zara zara yatsun hannunta tana jan mayafin tana sake rufe gaban kanta da kyau.
Wasu lafiyayyun plate shoes ne a qafarta,mahadin qaramar handbag dinta ta kamfanin saint laurent dake ajjiye tsakiyar table din dake gabanta wanda ta gagara zama a kai.
Duk da daya hannun nata wayarta ce a ciki,amma hakan bai hanata harde hannayen nata a qirji ba, kyakkyawar fuskar nan babu digon fara’a ko daya akai,sai dan qaramin bakinta da take dan motsawa kadan kadan,alamun dake nuni da cewa a matuqar qagauce take da tsaiwarta a wajen.
Ba ita kadai ba,koda kaine a wajen wala’alla ka shiga sahun masu tayata ginsa da tsaiwar,sakamakon yadda idanu sukayi yawa a kanta a wajen. Duk da cewar wannan din ba shine karo na farko ba a rayuwarta ba,ba koma. Sabo ko baqon abu bane cikin rayuwarta ba,amma a yanzun da komai ya canza cikin rayuwarta,al’amura masu yawa suka kutsa cikin rayuwarta suka kuma shude da abubuwa masu yawa da matuqar muhimmanci a wajenta ya sanya komai ya sauya……ya dasa mata tsanar kowanne kalar kallo da zai fito daga qwayar idanuwan da suka kasance mallakin ƊA NAMIJI,idan ka dauke mutane hudu rakkin dake da matsanancin muhimmanci cikin rayuwarta.
Har yanzu guri daya idanuwanta suke kalla ba tare data barsu sun gusa da kallon gurin ba ko sau daya,nisan taku masu dan tazara ne a tsakaninsu da budurwar data zubawa idanu,wadda ke tahowa gurin da mabanbancin yanayi tsakaninta da wadda ke a tsayen ta kasa zama, idanuwanta cikin nata tana sake karantar zallar tsanar data yiwa wanzuwarsu a gurin harta iso
“Am very sorry bestie……” Ta fadi a taqaice cikin son kaucewa ganin yanayin fuskarta,ta miqa hannu ta gyara mata zaman kujerar dake bayanta,sannan ta mayar da dubanta gareta
“Have a seat” ta fadi mata suna hada idanu. Tsareta da ido tayi na wasu sakanni,ba tare data shirya ba dariya ta qwace mata,tasa hannu tana qoqarin rufe bakin
“Afifa…..” Ta buda baki ta kirayi sunanta da wata irin murya me zaqi da laushi,fararen manyan idanunta na ragaita saman fuskar wadda ta kira da afifan
“Kiyi haquri ki daina kallona da manyan idanun nan naki haka,sai ki saka na daburce,kiyi haquri ki zauna,mintuna kadan zasu kawomin na gaya musu sauri mukeyi” jimmm tayi na wasu sakanni sai kuma tasa hannu ta matso da kujerar dab da ita ta koma da baya ta zauna.
Hirarrakin mutanen dake zaune daura dasu ta fara shiga mata kunne tana haura mata ka,duk da cewa ba suna magana bane da sauti sosai,zamanta tsakiyar halittun da a wajenta suke masu ban tsoro yasa takejin kamar a kunnenta ake maganar,sai tasa hannu taja jakarta ta fara kici kicin fiddo earpiece ta maqalawa kunnenta ko zata samu sassaucin jin muryoyin da bata qaunar jin irinsu.
Tsaf afifa ke karantar ta,ta zuba mata idanu tana kallon yadda gaba daya walwala tayi qaura daga kan fuskarta,kamar wadda ke zaman waqafi cikin kurkuku.
A nutse ta sanya earpiece a dukka kunnuwanta bayan ta sadar dashi da wayarta,tana jin feeling na insecurity a tattare da ita. Duk da taqi yarda idanuwanta su kalla kowanne sashe na wajen,gudun yin tozali da mugayen halittun MAZA dake wajen,amma all her body tana jin akwai wani ido dake karakaina saman jiki da fuskarta,bayan idanuwan da suka jima suna kallonta na mafi yawan mazan dake zaune a wajen.
Cikin wani irin coolness take latsa wayarta,ranta yazo mata iya wuya,tayi watsi da hirar da afifa keta qoqarin sanyata yi akan dole dole. Rashin samun hadin kan SÃAHAR din ya sanya afifa kama kanta bisa dole,tana zuge zip din jakarta order dinsu ta iso,waitress ta ajjiye tray din a tsakiyarsu cikin nutsuwa da girmamawa,tana kuma basu haquri na delay din da aka samu