Bakon Lamari 7
A hankali sautin ƙarar shigowar Motar shi cikin gidan ke kaɗa mata hanjin Cikinta, Daga cikin Ƙirjinta Kuwa dokawa yake da ƙarfi wanda In mutum yana kusa da ita tsaf zai ji sautin dokawar da Ƙirjin nata yake.
Tun Bayan fitar Ameerah daga gidan take zaune a falo ita ɗaya gaba ɗaya tsoron dawowar Imran gidan take wanda hakan ya zame mata al’adar Rayuwarta Koda yaushe In ya fita Tana cikin Raha da Nishaɗi amman da zarar Ya dawo to duk wani Ɓurɓushin Farin cikinta Gushe wa yake yi.
Tsayin watanni tara kenan da auran su da Imran amman har zuwa wannan lokaci ta Kasa samun farin ciki kamar ko wace mace acikin gidan Mijinta.
Curewa take a waje ɗaya tana haɗe jikinta tamkar mai jin sanyi, A hankali Taji sautin shigowar sa cikin Falon bada ban tayi da gaske bama da bazata ji sallamar tashi ba.
Sosai Abin ya bata mamaki amman sai ta wuce taje tayi yadda yace Ɗin daga bisani ta dawo Har ya wuce waje abin mamaki ba wannan Motar daya Shigar da ita gida ya Shiga ba ashe akwai wata a waje mai kyau sabuwa ya buɗe mata gidan gaba ta shiga ta zauna Yaja suka hau Titin Rijiyar Zaki inda anan layin Rumfar shehu gidan su yake.
Sai da ya tsaya a wani Store yasai kayan abinci aka shigar dasu Motar sannan ya shigo suka ja Suna tafiya ita bata ce mai ba shi bai ce mata ba har suka ƙarasa layin.
A bakin Ƙofar Gida Yay parking bata jira shiba ta ɓalle murfin ta fita wajan ƙatuwar tabarmar Su Alhaji Babba ta ƙarasa wanda Suke zaune suna shan Iska sallama tayi agaban su ta tsugunna tana gaishe dasu.
“Ma sha Allah! Amatullah kece da wannan Lokaci barka barka da zuwa naji daɗin Ganin ki Allah ya ƙara zaunar mana dake lafiya, Koke fa da kika kwantar da hankalin ki”
Aranta tace Alhaji ba zaku gane yaran ba, Nidai zan cigaba da haƙuri.
Nasiha sauran ƴan uwan mahaifin nata sukai mata kafin ta miƙe tabar wajan ta nufi Cikin gida.
Babban Gida mai sassa da dama acikin sa wanda ya haɗe ƴaƴa da jikoki sashin su ta shiga da sallama a bakin ta.
Umma tana zaune tana bawa Baba ayaba a bakin shi ta ɗago cikin sakin fuska take amsa wa Amatullah Sallama.
“Kece da wannan daran dafatan dai lafiya?”
Amatullah ta dubi Ummah da mamaki sannan tace.
“Tare dashi muke yace ne nazo na duba Jikin Baba”
Bata kai ma da rufe bakinta ba Umma ta miƙe tsaye tare da Nufar Ƙofar Gida da sauri Amatullah ta riƙe Hannun Ummah tana gyaɗa mata kanta.
“Ummah yanzu fa zai shigo Gidan Dan Allah ki Koma ki zauna”
Ta Doke hannun Amatullah tana cewa.
“Cikani Dan ubanki so kike Su hure masa kunne a waje ko? Su roƙe mashi Kuɗi a banza”
Amatullahi ta sunkuyar da kanta cikin takaicin Halin Ummanta batace Mata komai ba Umman na ƙoƙarin Fita Imran ɗin ya shigo.
“Lale maraba da zuwan ka Imirana daman yanzu take cewa tare kuke”
Ya zauna a saman dardumar daya gani a shinfiɗe cikin jin kunya yake cewa
“Eh Muna tare dasu Alhaji ne muna gaisawa”
A take ilahirin annurin fuskar Umma ya ɗauke dan bata ƙaunar wani ya raɓi surukin nata bare yaci arziƙin sa.
Tana ƙoƙarin yin magana ƙannen Amatullahi Hassan da Hussaini suka soma shigo da kayan abincin daya siya a hanya Bakin Ummah kamar Gonar auduga.
Sai albarka take shiwa Imran wanda yake ta sakin murmushi mai tarin ma’anoni da yawa.
Sam Ummah bata tambayi Amatullahi yaya zaman su da Mijinta ba bare ta jata ajiki ta shigar da ita ɗaki su ɗan zanta irin na ɗa da mahaifi sai ma mayar da hankalinta kan Imran datai suna ta hira.
Ganin Haka yasa Amatullahi taja Jikinta zuwa wajan Babanta wanda yake kwance.
Ta ƙarasa wajansa ta zauna tana kallon shi shekara Kusan Biyar yana kwance ga matsalar ƙafafu da basa takawa ga matsalar Idanu damma yau an masa aikin Idon wanda aka sanya masa glass a idanun nashi ba wani tsufa yayi ba, Amman lalura ta saka girma ya hau masa da wuri.