Hausa Novels and Stories

Rabi Danja Hausa Novel Page 3

Sponsored links

Rabi dake tsaye tana ta tintsira dariya jama’a suna kallon ta suna ganin ƙarfin halinta, Tsohuwar nan ma kallonta take ita a tunaninta ma Yarinyar taɓaɓɓiya ce, wasu a wajen suna Rabi ta birge su da tayi haka wasu kuma da suka san Rabi suke jin haushinta suka hau zagin ta, suna ai zata aika tayi wanda yafi haka ma.

Rabi kuwa zuwa tayi ta kamo hannun Baraka ta ce “Bari na taimaka miki Baba”, Baraka kuwa washe baki tayi tare da faɗin “yawwa Ƴar albarka kin kyauta min kuwa”, tiryan-tiryan ta damƙi hannun Baraka suka nufi hanya, Baraka taita kwantanta mata hanyar da zasu bi, kamar abin arziƙi suna tafiya sannu a hankali kamar makaho da ɗan jagora, sai da ta je inda ba mutane sosai Rabi ta buɗe murya ta kurma ihu tana faɗin “ga Balo mahaukaci nan mu gudu Baba”, ai jin haka yasa Baraka gudu tana yi tana harɗewa ga ido a rufe ƙasa ta cika shi, janta Rabi take tana faɗin “gashi nan saitin bayanki fa ki ƙara gudu kar ya kamo ki kuma Alkur’ani duka yake”, ai nan take Baraka ta ƙara gudu akan nada, gata a mulmule ƙatuwa, dariya sosai gudun yake bawa Rabi, sai sai batayi yadda Barakan zata ji, “na gaji Yarinya Alkur’an ban iya gudu ba…”, dai-dai nan ta afka wata ƙatuwar kwata mai tsananin ɗoyi da hamami, kuma a ƙalla zurfin kwatar yakai saitin ƙwanjin ta, “Wayyo Alllah na shiga uku ni Baraka ina ne nan?”, ta faɗa tare da ɗago hannunta ta kai hancinta dan tabbatar da inda ta faɗa, Rabi kuwa dariya ta hau yi harda faɗuwa da riƙe ciki, “Baba kwata ce Alkur’an kike cikinta gata nan” cewar Rabi da ta kasa riƙe kanta dan dariya.

Jin sautin dariyar da Rabi take mata yasa ta ce “ke dan Uwar ki ni kikewa dariya, na zaci ke ƴar arziƙi ce ashe ƴar iska ce ke”, tana faɗa yana ƙoƙarin ganin ta fito, zagin da tayiwa Rabi shiya tsaida dariyar da Rabi take ta kafa mata ido kana ta ce “ni kika zaga Baraka?”, “na zage ki dan ubanki shegiya mara kunya, wato har sunana kike faɗa dan fitsara inaa kika kai Baban da kike ƙira na da shi”, aikuwa jin ta ƙara zagin ubanta ya sa ta hasala ta hankaɗa Baraka tare da faɗin “Ba’a zagin Uwata ko Uba na a zauna lafiya, kuma ni na watsa muku ƙasa ke da kishiyar ki”, Baraka dake cikin kwata wannan karon babu inda kwatar bata ɓata ba har fuskarta saida ta shiga, ta ɗago da fuska duk kwata ta fashe da kuka ta ce “amma wallahi Allah ya kwashe miki albarka, tsinanniya matsiyaciya gantalalliya kai wannan wadda ta haifo ki Alkur’an ta cuce ni”, “au ƙara zagar min uwa zaki Baraka kinsan dai ga halin da kike ciki zan iya ƙara auna ki ciki”, ganin mutane suna tawo wa yasa Rabi barin wajen ta ruga a guje ta koma wajen faɗan Baraka da Biba dan ganin ya Biba ta kasance.

Baraka kuwa masifa take a kwata ita a tunaninta Rabi tana wajen bata san ta bar wajen ba, sai zage-zage take tana nuna saitin da take jin muryar Rabi, tana a haka har mutanen nan suka ƙaraso suna ganta a haka ganin tana nuna waje tana auna ashar yasa sukai tunanin mahaukaciya ce ɗaya ne ya ce “baiwar Allah ki fito a cikin kwatar nan mana”, “yawwa bawan Allah dan Allah kama Yarinyar nan idan na fito naci Uwarta, ita ce silar kasancewa ta a wannan hali”, mutumin kallon wajen yayi yaga ba kowa ya ce “baiwar Allah ai bakowa a wajen ke kaɗai muka taras”, “to wallahi guduwa tayi amma da wata Yarinya nake tare, nan ta basu labarin komai, “anya ba aljana ce ta miki haka ba kuwa, ƙaramar Yarinya ba zata aikata abinda kike faɗa ba, nan take tsoro ya kama ta bayan ta fito suka taro mata ruwa ta wanke idonta ta sheƙa sauran a jikinta kwatar wata ta wanku wata bata wanku ba tayi musu godiya ta nufi gida a tsorace dan tabbas duk mai wannan halin sai dai Aljanin.

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button