Hausa Novels and Stories

Makauniyar Kaddara Complete Hausa Novel

Sponsored links

*Page 1*

…………..“Inada tabbacin wannan itace tashar da zaki iya samun motar duk wani gari da kike buƙatar zuwa”. Mai napep ya faɗa dai-dai yana samun wajen fakin, da ɗan karkato kansa yana duban yarinyar dake a baya zaune.

Batace da shi komaiba. Sai ƙoƙarin kwance haɓar zaninta da takeyi jikinta na rawa. Ta miƙa masa ɗari biyar ɗin dake a ƙudundune saboda uban ƙullin da tasha a cikin zani. Baki ya buɗe kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan fisgi ƙudundunanniyar ɗari biyar ɗin daga hannunta yana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa.

A yanzu ɗinma batace da shi komaiba, sai hawayen dake famar zarya daga idanunta zuwa kumatu.

Tsohuwar ɗari biyu guda biyu da naira talatin a sama ya miƙa mata fuska a tsuke.

“Nagode”.

Ta faɗa a karo na farko tana amsar kuɗin. Batare da ta jira amsarsaba ta fito daga Napep ɗin tana kalle-kalle da ƙoƙarin sake maida kuɗin daya bata a haɓar zani ta ƙulle kamar ɗari biyar ɗin ɗazun.

 

A kallo ɗaya zaka iya fahimtar ƙarancin shekarunta. Dan kuwa bazata wuce shekaru sha huɗu ba. A tsarin halitta batai kama da mai taɓin hankaliba, amma a yanayi zaka iya kiranta da mai ƙarancin hankalin. Duk da kuwa babu wani datti ko makamancin hakan a kaf illahirin jikinta.

 

Ƙara kai hannu tayi ta share hawayenta a karo na babu adadi, cikin rauni da alamun tsoron dake tattare da ita ta furta, “ALLAH gani gareka. Da kai na dogara, a gareka kuma nake buƙatar taimak……”

 

“Ƙanwata ina zakije?”.

 

Karaɗin wani kwandasta ya katseta batare da takai ƙarshen addu’arta ba. Kallonsa tai da jajayen idanunta dake a kumbure saboda kuka tace, “Danya”.

 

“Danya? Ƙanwata sai kinyi ƙarin bayani, dan nikam bamma taɓajin sunan wannan garin ba”.

 

Shiru tai alamar nazari, ‘Gaskiyar kwandasta ɗin nan. Danya dai garinsu motama bata shiga sosai. To amma idan bata mantaba lokacin da zasu taho da Hajji Lanti bayan sun fito daga Danya a mashin, a Gozarki suka kwana, washe gari kuma daga Gozarki sukazo kusada, anan suka sami motar Katsina’.

 

“Wai kodai bakisan ina kika dosa bane ƴammata?”.

 

Kwandasta ɗin nan ya sake katseta. Da sauri tace, “Kusada zanje”..

“……Kusa da kano, nesa da birnin katsina” kwandasta ya faɗa cike da barkwanci. ita dai batace da shi uffanba, sai ma faman waige-waige da takeyi, har yanzu akwai tsoron ko wani zai iya biyo bayanta tattare da ita.

“Kinga ga motar da zaki hau can ta kaiki Gidan mutum ɗaya. Inada tabbacin daga can zaki samu motar kusada ƴar ƙyaƙyƙyawa”.

“Nagode sosai” ta faɗa tana ɗan risinawa. Daga haka tai gaba da sassafa batare data sake bi takansa ba.

Tana isowa motar daya nuna mata ko jiran ba’asi bata tsaya yiba saboda jin kwandasta ɗin motar nata faman faɗin, “Charanci, kankia, Gidan mutum ɗaya, Tsanyawa, Bichi, har kano.

Can baya ta shige inda wata mata ke zaune ita da yaranta biyu da bazasu wuce sa’annintaba. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya dasa hannu ta gyara ɗan labulen jikin gilashin yanda take fatan ko su Hajiya biyota sukayi bama zasu iya ganinta ba. Duk da hakan kuma roƙon ALLAH take a ranta ALLAH yasa motar ta cika da wuri su tafi.

Addu’ar tata kuwa ta amsu. Dan ko cikin ƙanƙanin lokaci motar ta cika. Ita dai tana duƙunƙune cikin hijjab har kanta. Ko wanda ya shigo ya zauna a gefenta bata kallaba sanda ya shigo. Ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jin motar ta ɗaga alamar zasu bar cikin tashar.

 

Sunyi tafiya mai ɗan tsayi data tabbatar sunbar cikin birnin katsina ta tsinkayi maganar kwandasta na ambaton kowa ya bada kuɗin mota. Ciro kanta tai daga hijjab ɗin bayan ta kunto kuɗin data ɗaure a haɓar zaninta na canjin mai napep. Jin matarnan mai ƴaƴa na tambayar “Nawane gidan mutum ɗaya” ya sata tsaida hankalinta tana jiran amsar kwandasta ɗin itama.

 

“Ɗari huɗu ne kuɗinki hajiya”. Ya bata amsa yana amsar kuɗin na kusa da shi.

 

Matar tace, “Haba ɗana adai duba. Wlhy jiya a ɗari uku-uku mukazo. Yaran nanma ɗari bibbiyu na biya musu”.

 

“Ai jiya kikace hajiya. Jiya kuma ba yau bace. Dan haka kuɗinki keda yaranki dubu da ɗari biyu ne”.

 

Zatai magana wani dake can gaba yay saurin amshewa. “A’a fa gaskiya ɗari uku ne, ni kaina ɗazun nan da safe nazo a haka”.

 

A take rigima ta kaure tsakanin kwandasta da matarnan da mutumin da yay maganar da safe yazo a ɗari uku. Da ƙyar dai aka tsaya akan ɗari uku da hamsin.

Ita dai yarinyarnan dama bata tanka ba. Ta miƙa masa ɗari huɗun da mai napep ya bata canji.

 

“Ƙanwata ina zakije?”.

 

A taƙaice tace, “Gidan mutum ɗaya”.

 

Canjin hamsin ya miƙo mata. Batare datace komaiba ta amsa ta maida a haɓar zaninta. Sai dai bata koma cikin hijjabinba tabi ayarin masu kallon hanya. Kasancewar motar mai lafiya ce bayan sallar la’asar kaɗan suka iso gidan mutum ɗaya. Danma sun ɗanyi tsaye-tsaye a hanya na sauke mutane.

 

A gidan mutum ɗayarma dai a rikicen take. Dan ba taɓa yin tafiya irin haka ba sai wannan karon. Sanda zasu tafi kuwa hajji Lanti ce tai musu komai. Da ƙyar ta samu ta tambayi wani yaro mai saida biredi inda zata sami motar kusada. Shine ya nuna mata. Tai masa godiya.

Ta iske ƙananun motoci kusan huɗu dake jere a kan hanyar da yaron yace mata itace hanyar kusada. Lokacin da suka tafi su tun daga cikin kusada suka shigo motar katsina.

 

“Ƴammata kusada ne?”.

 

Wani tsamurmurin saurayi ya faɗa yana nufota. Saurin ɗaga masa kanta tayi alamar eh. Cike da jin daɗi yace, “Yauwa taho muje, dama mutum ɗaya muke nema”.

 

Har cikin ranta taji daɗin hakan. Ya nuna mata jar motar data gama fita hayyacinta. “Yauwa shiga nan. Bayin ALLAH a matsa mata mu kama hanya ko”.

 

Cike da mita fasinjojin suka shiga muskutawa dan sama mata waje. badan wajen zai wadacetaba ta shiga ta zauna. Sai dai kasancewar ta mai ƙaramin jiki yasa bata takuraba matuƙa. Sai dai waɗanda ta tarar a ciki sunata faman mita sukam an takura musu. Direban ya cika haɗama da son kuɗi. Yanda direba bai tanka musuba itama bata tanka ba. Sai dai acan ƙasan ranta daɗi takeji zata koma gida taga Babanta da su Yaya Tinene, duk da su ba son ganinta sukeba.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button