Kannywood News

Jarumi Kuma Mawaƙi, Musa Gombe ya Angwance da Amaryar sa Banupa

Sponsored links

 Kannywood News

Jarumi Kuma Mawaƙi, Musa Gombe ya Angwance da Amaryar sa Banupa.

Ango da Amarya

Nupe Day

Jarumi Kuma Mawaƙi Musa Muhammad Musa, wanda aka fi sani da Musa Gombe ya auri masoyiyar shi kuma rabin ran shi. Sun sha soyayya wadda ba ta wuce tsawon shekara daya ba.
Jarumin dai Bafulatani ne dan asalin jahar Gombe ne, ita kuma Amarya Salma kuma Banupa ce ƴar asalin jahar Neja.
Masoyan guda biyu sun hadu da juna ne a lokacin da suke yi wa ƙasa hidima, watau bautar ƙasa (NYSC). Inda daga bisani soyayya ta qullu a tsakanin su kuma har abin ya kai su ga yin aure.
Anyi shagulgula da dama tun kafin ranar auri aure. Ayin Fulani Day, wato rana ta musamman da aka ware domin Fulani. Wanda hakan ya na da nasaba da ainihin nuna ƙauna da soyayyar al’adar ahalin Ango.
Sannan kuma anyi Nupe Day shima kuma anyi haknne domin martaba asali da kuma nasarar dangin a

Bayan haka kuma an gabatar da gagarumin wasan kwallon kafa wanda jaruman Kannywood da kuma mawaƙan Kannywood suka hadu a gefe guda domin fuskantar bangaren ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Abdul Amart.

Bayan haka kuma an daura auren ne a ranar asabar, wanda ya yi daidai da 17 ga watan Satumba na 2022. Ai dai daura auren Musa Muhammad Dan Musa da amarya e shi Salma Abudaziz Chado  ne da misalin karfe goma na safe, a masallacin Murtala da ke Kanon Dabon Nigeria.
 
Daurin auren ya samu halartar manya-manyan jaruman kannywood da mana, mawaƙa, ƴan uwa da kuma abokan arziki

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button