Furar Danko Page 7 Hausa Novel
“Babyna in dai hakan zai sa ki huce ina tare da ke”.
“Thanks you sweet Papa..”
Ta faɗa tana ɗan rungumesa da sumbatar hannunsa sannan ta miƙe, yatsu biyu ta ɗaya masa alamar bye ta nufi ɗakinta dake acan gefe part guda kamar wata mai aure, sai dai duk a cikin sashen iyayen ne. Murmushi yake da binta da kallo har ta ɓacema ganinsa. Bata zauna a ƙayatacen falonta da ya gama tsaruwa ba ta nufi bedroom kai tsaye. Ɗaki ne haɗaɗɗen gaske kuma ƙato. Dan bayan ƙaton gado da wardrobe kusan rabin bango da mirror akwai set na kujeru da aka shirya tsaf tamkar falo anan ma, sosai ɗakin ya haɗu tare da amsa sunansa ɗaki kamar na macen aure. Cikin yamutse fuska take bin dattijuwar dake ta saka turaren wuta a burners kusan kashi uku da harara, sai kuma cikin faɗa da masifarta ta daka mata tsawa. “Da uwar mi kike a ɗakin da baki gama min ba har na shigo….?”
“A gafarce ni Aunty (Duk da zata iya haifarta ta kafama duk wani ma’aikaci dake gidan dokar kiranta aunty komai tsufarsa). Bayi na tsaya wankewa da ƙyau har jikin bangon da kikace”.
Kakkauran tsaki ta ƙara ja da ƙarasa shiga ɗakin, saman gadon da aka lailaye da bedsheet mai shegen ƙyau fari tas ta jefa wayarta, itama ta faɗa ta kwanta tana mai wargaza fillos ɗin da aka gama wahalar tsara mata yanda take so, har ta lumshe idanu ta buɗe, a gadarance ta ce, “Kimun farfesun kifi mai yaji da kunun tsamiya, biyar nayi ki haɗamin ruwan wanka. Idan kikai min kalar haukan wancan ranar wlhy bazaki gane kanki ba a hannuna fitar min anan banza ƙazamiya sai wani tsamin zufa kike”..
……..Idanun dattijuwar cike da ƙwalla ta amsa mata da girmamawa. A haife ta haifeta, bama ita ba har wadda ta fita, amma sam bata ɗaga ƙafa wajen cimata zarafi. Wai a hakan ma
itafa da sauƙi, dan a kaf masu aikin gidan ita kawai ta yarda ta shigo mata ɗaki ta gyara kota dafa mata abinda zata ci, hatta key ɗin ɗakin ita kaɗai ta bamawa amma ko momynsu bata da shi. Rigarta ta kama ta shinshina, babu abinda take sai ƙamshi amma ta ce mata tana warin zufa. “ALLAH ya shiryeki ƴarnan” ta faɗa cikin tausasawa tana ɗauke ƴar ƙwallar da suka cika mata ido. Dan duk da wulaƙancin da Lulu ke mata tana ƙyautata mata, zata iya cewa duk abinda ta samu na cigaba a aikin nan nata sanadin Lulu ne, ba ita kawai ba hatta ƴaƴanta dake ƙauye da ƴan jikokinta suna ci da ga alkairin Lulu, barta dai da shegen rashin mutunci, dan in har zakai lissafin masifaffun mutane a rayuwa to indai Lulu batazo ta farko ba tazo ana biyu. Bata da kirki sam, kuma bata ragama uban kowa sai Daddy da Uncle Yousuf, wani lokacin ma Uncle Yousuf ɗin ne ya ɗan fi cin nasararta, dan shi har faɗa yakan ɗan mata da nuna mata kuskure idan tayi, amma Daddy shi komai tayi ma dai-dai yake koda kuwa ba dai-dai ɗin bane ba….