Fulani Page 3 Hausa Novel
Shattima ya tambaya yana dora kafa daya saman daya. Baba Adamu ya kara yin kasa da kansa.
“Ita ce ta bukaci sani, wannan dalilin ne yasa ta maido da ni gurinka saboda ta rika sanin halin da na ke ciki”
Murmurshi Shattima yai mai sauti ya shafa kansa.
“Amman Baba Adamu ba ni da ikon yin sirri da kai? Ko ruwa na sha sai ka fadawa Hajiya? Ana rayuwa haka?”
Ya tsosa lips dinsa, yana kallon Baba Adamu, Baba yake kiransa duk kuwa da kasancewar karkashina yake sai dai ganin dattijo ne wanda ya isa ace ya haife shi be zai iya kiran sunansa hakan nan kawai ba.
“Yanzu ga shi ina son ganin yayana amman ba ni da dama saboda ka fadawa Ammy, ni kuma ba son shiga na ke gidan ba daga ita har Mai Martaba ba barin yi min maganar aure suke ba”
Ya fada yana daga kafadunsa. Baba Adamu ya kalleshi cikin Ladabi ya ce.
“Ranka ya dade suna son kai auren ne, kai kanka za ka fi kima da daraja da aure”
“Haba dai Baba Adamu kamar ba kasan ni ba? Aure nawa zan yi Fisabilillahi? Mace shida ina aure suna mutuwa yanzu idan na kara ta bakwai kenan waya sani ko ita ma iyayenta su rasa ta, ni fa tsoro mana ke kar a fara min zargin maita”
Ya fada yana mikewa tsaye. Baba Adamu ya daga kai yana kallonsa.
“Ranka ya dade ba maita ba, kalmar ba da ka furta a bakinka ina ganin kamar be dace ba, waye be san kaddarar Allah ba?”
“To ka bincika min wace uwar ce ta son rasa yarta da zata aurawa Omar a samo min ita”
Yana fadar hakan ya nufi upstairs yana murmushi. Baba Adamu ma Murmushi yai duk da kasancewar duk mace da ta auri Shattima mutuwa take wata tana amarya wata bayan ta yi wata hudu zuwa kasa, Maimuna ce kawai tai shekara da wata biyar har ta haifa masa yan uku, bayan ita ya auri Basira ta rasu da wata daya, sai dai hakan ba shi zai saka yarima Omar auren ko wace mace ba a ganinsa sai wacce iyeyensa suka zaba masa ko kuma shi yake ganin ta dace da shi…..
WASIM RAU dan sarkin maharba kuma jikan sarkin matsafa na garin GARUK. Mutum ne mai son busar sarewa da zaman dajin, be fiye son harbin ba, duk kuwa da kasancewar shine gadonsa, ba shi da tsoro sai dai ban tsoro.
A yau ba saman dotsi yake busar ba kamar yadda ya saba, a saman ice ya hau yana busa sarewarsa, cikin natsuwa da kwanciyar hankali yake busar, ba mutum kadai ba ko aljani idan ya ji busar sai zuciyarsa ta sosu. Lumshe ido yake yana budewa shi kanshi busar dadi take masa domin tana saka shi nishadi da walwala, idan ka cire abinci da ruwa da rai baya iya rayuwa sai da su to busar sarewa ce abu na biyu da yake kauna a rayuwarsa, busa ce mai dadi kuma mai daidai da yanayin garin da ya hada hadari da iska mai dadi….
AHMAD ASHIRU UNCE A A matashin sarauyin da bashi da aikin yi ba dan be yi karatu ba, sai dan aikin a Nigeria ya zama sai wane da wane, sai mai hanya da gata sai kuma wanda Allah ya tsago da rabon abincinsa a gabnatin jiha ko ta tarayyah, a gurin yayarsa yake zaune wacce ta tsaya masa bayan raye uwa da uba, ita ta zame masa tamkar uwa duk wani fadi tashi na karatunsa da hudimar rayuwarsa ita ce take masa duk kuwa da kasancewar ita ma din ba wani abun hannu ne da ita ba, sai dai tana sa’ar siyarda kayan masarufi a cikin gidanta sana’ar ta karbeta sosai a ciki take ci ta ke sha har ma tai ma mijinta wata hidimar kasancewarsa karamin lebara ne wata….