Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 98

Sponsored links

Wani irin mikewar zabura tayi kamar wadda aka dawoma da dukkan karfinta dai-dai da dawowar Tajwar Eshaan akin. Fashewa Iffah tai da kuka da durkushewa gaban Malikat Bushirat da ta mike tsaye a zafafe. Ta riko duka kafafunta tana kukan da fadin, “Ammie nasan zaki fadukkan bayani na, kuma zakimun adalci a cikin dukkan abinda ya farun nan. Nima ba laifina bane tirsasani sukayi da mun barazanar karar da ahalina dama ku musamman ke da kike mahaifiya ga adalin shugabanmu. Ni kuma a shirmena idan na bashin za’ai saurin kaisa ga likita kafin ma dafin macizan yay tasiri. Ki yafe min Ammie nayi kuskure da wauta ki yafe min

Gaba daya Malikat Bushirat sai ta sake mutuwar tsaye. Eh lallai yau taga masifa, anya yarinyar nan mutum ce kuwa? Shikam mai gayya da aikin yay wata irin tsaiwar da ko bai fito fili yace komai ba Malikat Bushirat da kanta ta hango abinda ta hango a cikin idanunsa da ke tsaye kyam akan Iffah da ke a gurfane gabanta.Tabbas idan tai wani abu a yanzu akwai matsala,zakuma tayi kuskuren da yafi na yarda da shigowar yarinyar nan masarautar nan. Hadiye abinda yay mata tsaye a makoshi tai da kyar, ta rankwafa ta kamo kafadun Iffah ta mikar da ita tsaye. (Ya ALLAH hawaye fa share-share a fuskar Iffah kamar gasket). Bata da zabin daya wuce rungumeta itama tana matsar kwallan karya ta shiga fadin. “Ban san haka bane Ibnati miyasa kika ki fahimtar da ni da ban miki irin wannan mummunan zaton ba ai. Kiyi hakuri ki gafarceni”……….

“Ammie nagode sosai, Nagode da kika fahimci abinda naketa son ki fahimta tun tuni.Fhareedah yarinyar kirki ce mai cike da tarin alkairai daban-daban, kuma nasan zaki sake

tabbatar da hakan anan gaba. Na miki alkawarin aiki tare da ita har sai duk wani markiyinmu ya bayyana batare da shi kansa ye sani ba. Ki cigaba da mun addu’a ke dai,gaskiyar danki na gab da fitowa zahiri ga kowa.Dan yanzu haka dukkan wasu bincike akan cases din nan suna’a hannuna, hatta wanda yay tushen bada madaran, da wanda ya sakata a ruwa duk sunzo hanun hukuma. Kallonsa tai da wani irin sauri, sai kuma ta hadiye tana mai kankame hanunnsa a cikin nata. Idanunta ta lumshe hawaye sukai wani irin zubowa. “Ashe zanga wannan ranar, wanna ranar zatazo gareni haka Saiful-malik?”. Ta fada cikin subutar baki

Ko kadan Tajwar Eshaan bai fahimci kalaman nata ba, ya fassarasu ne akan nuna farin cikinta na zataga wannan raar da za’ai walkiya halin wanda batai zato ba ya fito. Sai kawai ya saki murmushi da kai hannu yana share mata hawaye. “Zaki gani Ammie. Ai dama komai yay farko zakiga karshensa na zuwa. Ki cigaba da mun addu’a ke dai indai nasarorin ne yanzu kika

fara gani. Sai kin zama mafi kololiwar uwa da zatai alfahari da haihuwar da daya tilo tamkar dau abu insha ALLAHU”

Godiya a sake mata da dan lallashi, hakama harda durkusawarta. Kafin ta wani kananna de ma Malikat Bushirat ido a kaikaice ta sakar mata gwalo. Tajwar Eshaan na juyiwa ta fuske kalar tausayi. Hannunta ya kama a hankali yana mai kallon fuskarta ya sakar mata murmushin nan nasa mai narke zuciyarta. Murtani ta maida masa da dan saka hannu ta kare fuskarta ita a dole taji kunya ne. Duk Malikat Bushirat na kallonsu. Suna ficewa ta zube kasa yarafff wani irin mahaukacin jiri na dibar idanunta. Sai kawai ta fashe da kuka tana kiran sunan Uwa.

Tantabaru biyu iyayen soyayya da alkawarin kam suna fita ya duke kasa ya bata bayansa alamar ta hau. Idanu ta waro masa waje alamar mamaki. Ya dan juyo yana kada mata kai da lumshe idanu. Babu yanda ta iya ta tattare rigarta kadan ta hau tare da makalkale masa wuya dan sam bata iya gardama ba. Takun nan nasa yake a hankali cikin izza da kasaita har zuwa sashensa tana a bayansa kwance luff mamakinsa na neman kasheta, duk wanda yasanshi a Shahan-shan din sa bazai taba mafarkin abinda yake mata yanzu zai iya ba.Koda suka shiga elevator ma bai sauketa ba sai boye fuskarta da tai a wuyansa. Aiko gaba daya numfashin da take busa masa ya nema birkita masa lissafi.Maimakon ajiyeta a daki da ya shiga sai kawai ya wuce da ita bathroom ya direta ta bude idanunta. Da sauri ta kallesa a dan rude gain inda ya kawosu. Sai kawai yay wani luuu da idanunsa cike da basarwa ya danne makunnan shower ya sakar musu ruwa a kansu mai dumi. Babu shiri ta zabura ya rikota a hankali, jikinsa ya matsota ya rungume ruwan na cigaba da sauka a kansu.

 

Kusan mintuna uku suna a hakan kafin ya bude idanunsa ya sauke a kanta yana mai kai hannunsa saman veil din ta ya shiga warwarewa a hankali. Tanaji tana gani ya raba jikinta da kayan da suka gama jikewa sharkaf shi ma ya cire nashi. Jikinsa ta fada kawai nata na rawa ga wata matsananciyar kunyarsa na ratsata. Sosai hakan da tai yay masa dadi, dan ya samu damar sake gain tawadan ALLAH din nan ta bayanta yanda ya kamata, yanda har sai da ya haddace ta. Ita kam har aka kammala wankan bata yarda ta bude idanunta da ta rufeba..

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button