Daudar Gora Book 2 Page 88
Idanu ya lumshe a hankali. Ji yake kukanta na wani irin sukar masa zuciya. Itama kanta malikat Haseenat ɗin wani irin tausayin Iffah’r ne ke ratsata. Ita tasan ba lalaci bane ko raki kawai. Dan zuri’ar su Tajwar Eshaan ɗin fitinannun mutane ne da indai mace taje hannunsu basa iya mata ta sauƙi. Shiyyasa mafi yawansu basa iya zama da mace ɗaya, sannan suna aure da wuri gudun faɗawa halakar zina duk da akwai bijirarru a cikinsu da kan ringa aikatawar. Amma ita a karan kanta ta daɗe tana mamaki akan Tajwar Eshaan da ya nuna baya buƙatar aure tun a shekaru fara girmansa, hakama yanda ya kai har shekarun da aka masa auren fari na sata jin waswasin ko yana neman matan banza ne ko baida isasshen lafiya. Dan tasan duk wanda ya kasance jinin zuri’ar wannan daula baya iya kauda kai ga mace irin hakan da ya nuna shi.
Shiru Malikat Haseenat tai kawai tana kallon Iffah da ta koma ta kwanta, hanunta ta riƙo cike da lallashi ta ce, “To ya isa haka kukan kinji yarinyar albarka. ALLAH yay miki albarka. Ya jaddada rahama a gareki da yalwataccen farin ciki na har abada. ALLAH ya sa ki cigaba da zama haske mai haskaka wannan zuri’a”.
A saman lips ya amsa da Amin. Yayinda Malikat Haseenat tai amfani da wayarta tai kiran Daneen Ammarah. Wani irin yamm ya dinga ji a jikinsa jin Mammah na bada umarnin Daneen Ammarah ta shigo. Sai yaji kamar kasancewar su a waje guda yau wani abu ne mai girman gaske. Da ƙyar ya iya dauriyar cigaba da tsaiwa a inda yake har ta shigo ɗakin. Itama yanda take yi ɗin kamar wadda ta daburce. Sam taƙi yarda ta dubi inda yake kamar yau ne rana na farko da suka kasance ƙarƙashin inuwa ɗaya. Koda ya gaisheta kamar yanda ya saba cike da jarumtar danne nasa yanayin shima a hankali ta amsa masa batare da ta dubesa ba.
Ita dai Mammah hankalinta nakan Iffah ne bata san mima sukeyi ba. Sai da taji tsaiwar Daneen Ammarah kusa da ita ne ta ɗago. Daneen Ammarah da idanunta ke akan Iffah wani irin tashin hankaline ke ƙoƙarin mamaye fuskarta amma tana dannesa. Muryarta a ɗan sassauce ta furta, “Mike damunta haka?”.
“Ɗanki ne”.
Malikat Haseenat ta bata amsa a dunƙule. Ta fahimta dan haka bata sake magana ba sai da Malikat Haseenat ta ce, “Kamamun ita ta tashi zaune da ƙyau. Sai ki sake haɗamun ruwan ɗumi da waɗan nan turarrukan”. Kai kawai Daneen Ammarah ta jinjina ma Mammah, ta matsa ta kama Iffah ta tayar, kuka take sosai tana rirriƙeta amma Malikat Haseenat ta ce mata ta barta so take ta zauna ɗin sosai. Ba yanda zatai haka ta zaunar da ita ta zame jikinta batare da ta sake yarda ta kalla sashen da Tajwar Eshaan ya ke ba ta wuce bathroom abinta. Shima sai kawai yaji zaman ɗakin bazai yiwu masa ba. Dan haka ya fito abinsa yana mai satar kallon Iffah da ke kuka da mutsu-mutsun kasa zama da ƙyau. Kai tsaye Gym ɗinsa ya nufa. Jallabiyar jikinsa ya zame ya canja da sport wears ya shiga motsa jiki da zafi-zafi kamar wanda ake tunzurawa…..
★Da ƙyar Iffah ta iya kai kanta bayi da taimakon Daneen Ammarah. Ashe ɗazu ba ƙaramin taimako yake mata ba da yake ɗaukar ta a komai. Sosai hankalin Malikat Haseenat da ita kanta Daneen Ammarah ɗin ya sake tashi da yanda tafiya ma ta gagari Iffah. A bayin ma duk yanda taso ganin ta nutsu a cikin ruwan ta kasa zama. Sai faman rirriƙeta take da magiyar “Mamy dan ALLAH ki fiddani, wlhy da ciwo sosai”.
Kwantar da kanta Mamy tai akan ƙafarta tana shafa kanta cike da lallashi dan tana zaune ne a bakin kwamin. “Yi haƙuri to ba’a magana a bayi zai daina”.
“Mamy bazai daina ba ƙarawa yakeyi”.
Tunda kaf yaran randa aka kawosu garesa washe gari ake zuwa a ɗauki gawarsu sun rasa ransu. Ɗaga Iffah tai da ga ruwan, ta ɗaure fuska sosai babu alamar wasa tattare da ita, “Ki tsaya a duba ko kinji ciwo ne a wajen, dan wannan zafin da kike ta ambata dole zai kasance akwai damuwa Ibnati. Idan kuma aka bar mace da irin matsalar nan yana lalatata koma ya taɓa mata brain. Ko kina so ki samu matsala a brain ɗin ki?”.
Da sauri Iffah ta jinjina mata kai alamar a’a tana hawaye. Daneen Ammarah ta haɗiye murmushin da ke taso mata dan ta mata hakane dan ta tsoratar da ita dama kawai. Ai ko sai gashi ta yarda ta duba cikin sauƙi amma fa ta ɓoye fuska cikin tafukan hanunnta, wani irin matsanancin kunyar Mamyn na ratsa ɓargo da jinin jikinta. Amma sai take jin inba itan ba bazata taɓa iya nunama wani ba sai ko Ummu ko su Arfa da suna raye.
Rasama abin cewa Daneen Ammarah tayi, sai kawai ta miƙe jiki a saɓule cike da tausayin Iffah. Tabbas dolene ta dinga kuka, a hakan ma sai taga dauriyarta, dan in har watace tofa sai duk masarautar nan sun fahimci halin da ake ciki. Fitowa tai ta samu Malikat Haseenat da ke zaman jiran fitowarsu. “Mammah akwai matsala fa gaskiya, dole a nema likita dan yarinyar nan taji ciwo bana wasa ba”.