Daudar Gora Book 2 Page 84
A hankali yay ƙoƙarin kwantar da ita domin sauka ya samu mafita amma ta ƙanƙamesa ta na sake sakar masa wani sabon kukan da ko muryarta ma ba’a iya ji tsabar yanda ta gama galabaita. Ji yay kawai murmushi mai sanyi ya suɓuce masa, sake riƙota yay yasa a cikin jikinsa yana hura mata iska a kunne cike da soyayya da ƙaunarta da ke neman fallasa kansu a zahirinsa. Ajiyar zuciya ta cigaba da saukewa jikinta na saki kaɗan-kaɗan, da ga haka wani wahallen barci yay awon gaba da ita. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da ita a hankali sannan ya sauka a gadon.
Cikin ƴar sassarfar da a zahiri bazaka taɓa gani ba, dan babu abinda ya canja a salon tafiyarsa ta ƙasaita ya nufi bathroom, ƙarƙashin shower kawai ya shiga, babbar gaba ɗaya ya kunna ma kansa tare da dafe bangon glass ɗin da aka zagaye wajen shower ɗin kamar wani ɗan ɗaki. Duk da sanyin da garin ya ɗauka na hadarin da aka haɗa ya ƙare da isaka da ɗan yayyafi ya baje dana ruwan baya jinsa ma. Cikin ƙanƙanin lokaci ruwan yay masa sharkaf, tattausan yalwataccen gashin kansa duk sun kwanta masa a goshi har wasu na ɗan taɓa saman idonsa saboda ɗan tsayin da suke da shi. (She’s my everything. Ta daban acikin daban ƙololuwa!….) Kawai yake iya maimaitawa a zuciyarsa hakwaransa cije da lips ɗinsa kamar zai hudasu kawai ya huta. Sai da ya kwashe kusan mintuna bakwai a ƙarƙashin shower ɗin sannan yasa hannu ya danne makunar yana sauke numfashi a jajjere. Har lokacin hannunsa ɗaya dafe da bangon glass ɗin. Jin atshawa na taso masa sannan ya buɗe idanunsa da sukai wani irin jajir da ƙanƙancewa. Sanin in har ya fita da wannan sanyin a jiki zazzaɓi salamu alaikum ya sashi sake kunna shower ɗin, sai dai yanzu ruwan ɗumi ne saɓanin ɗazun. Sumar kansa ya shiga yamutsawa a kasalance ruwan ɗumin na ratsashi da ƙyau, da ace zai iya kuwwar tattaro hankalin mutanen duniya baki ɗaya zai faɗa musu itace komansa, idan yace komai, komai da komai yake nufi akan komai. Sake jin kiran salla ya sashi ƙarasa komai a gurguje ya fito..
Yana fitowa a kanta ya fara sauke birkitattun idanunsa da launinsu ya zama abin firgitarwa ga mai kallo. Tuni barcin da ya ɗauke ta ya ƙara nisa, barcin da shi a karan kansa yasan na wahala ne kawai. Janyewa yay ya cigaba da takowa cikin ɗakin sannu a hankali kamar mai sanɗa, dan gaba ɗaya jikinsa babu wani ƙarfi kona sisin kwabo. Sai dai jarumtarsa ta ɓoye komai bayan canjawar launin idanunsa baka isa fassara yanayinsa ba. A gurguje ya busar da kansa domin rage laimar cikinsa ya shirya cikin jallabiya mai taushi fara tas, ya ɗaura baƙar alƙyabba irin ta sarakunan Saudiya da mayafi a kansa tare da daɗaɗan ƙamshi kamar ba sallar asubahi zai fita ba. Gaban gadon ya tako a hankali, barcin kam da nauyi ya ɗauketa, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci a matuƙar wahalce takeyinsa, dan sai yamutsa fuskarta da yake ɗan gani a hasken ɗakin da yake dimmm take ga ajiyar zuciya da take ta faman saki a jajjere. Idanunsa ya ɗan lumshe ya sake buɗewa a kanta yana sakin guntun murmushi da jan jikinsa baya a hankali ya fice fara gabatar da salla kafin ya dawo su ɗora daga inda suka tsaya dan yasan sabon daru kam zai fuskanta. Shi kuma ko a yanzu badan yana jin tausayinta ba sake zuwa mata zai a yanda yake jin kansan nan.
★Ana idar da salla ya baro massalin, dan gaba ɗaya hankalinsa na gareta saboda yasan tana matuƙar buƙatarsa kusa da ita da taimakonsa a wannan gaɓar. Yanda ya barta haka ya dawo ya sameta. Yanzun ma baiyi wani motsin da zata farka ba har ya kammala zame kayan jikinsa ya canja da ƙananu. Bathroom ya nufa ya haɗa ruwa na musamman sannan ya dawo gareta. Kai tsaye ya kunna wutar ɗakin da ta haske ko’ina ko allura kuwa ka yarda kaga abunka.