Daudar Gora Book 2 Page 82
Aliy sai yazam bashi da shi lokacin da aka haifesa amma sauran yan uwansa na baya duk sukazo da shi, maƙiya sai suka riƙe wannan hujjar a lokacin da za’a naɗashi sarki suka shigo da wata magana mai ban tashin hankali data girgiza masarautar nan baki ɗaya, har sai da ta kai anbi diddigin jinin Aliy da mahaifinsa. Wannan al’amari shi kuma sai ya riƙesa, bayan hawansa mulki duk wanda aka bincika bashi da tambarin sai an masa da wata alama da ke tabbatar da a cikin masarauta aka masa da hujjojin masu ƙarfi a rubuce. Idan aka haifi jariri kuma bayan yankan cibi shine abu na biyu da ake masa idan har babu shi…”
Idanunsa da ya zuba mata tun fara maganar ya ɗan motsa kaɗan zuciyarsa na wani irin bugu da sauri-sauri. Amma a zahiri bazaka taɓa fahimtar a wane yanayi ya ke ba. Murya acan ƙasan maƙoshi ya sake furta, “An cigaba da samun masu tambarin da yawa ne? Ko wanda akai mawa ne suka fi rinjaye bayan farawar?”.
Shiru na wasu sakkani Malikat Haseenat batace komai ba, sai kuma taja ajiyar zuciya. “I to ni dai a yanda na samu labari a ɗan binciken tarihi wani lokaci akan samu yawaytar masu shi, wani lokacin kuma sai kaga anata haihuwar marasa shi, al’amarin kamar yana tafiya a ƙarni-ƙarni ne, amma kaga tashi kaga”.
Babu musu ya miƙe kamar yanda ta buƙata, da taimakonsa ta hau wheelchair ɗinta, kai tsaye inda ƙaton hoton kakansa Tajwar Abdul-majeed ke manne kamar ka masa magana ya amsa ta nufa. Yatsanta manuniya ta kai a saitin fuskar hoton ta shafa, zuuu ƙaton frame ɗin hoton ya shiga wani naɗe kansa kamar ana naɗe tabarma da ga sama yayo ƙasa. Ƙofa ce ta bayyana, bai wani nuna mamaki ba dan ya riga yasan da kofar nan tun ba yanzu ba, dan shi wannan sashe da Malikat Haseenat ke rayuwa yanzu a ciki asalinsa sashen kakansa ne Tajwar Abdul-majeed, shiyyasa akwai sorrika masu yawa a cikinsa da ita kaɗai tasan da su sai wanda kuma taso ya sani. Da taimakonshi ta shiga yana biye da ita a baya. Ɗakine madaidaici mai ɗauke da tarin littattafai kala-kala. Gurin yayi ƴar ƙura alamar bawani shigarsa ake akai-akai ba. Kekenta ta wulwula zuwa bangaren arewa tana bin jerin manya-manyan littattafan wajen da kallo, shi dai yana tsaye da ga tsakkiyar ɗakin yana binta da kallo a ƙasaitance. Juyowa tai ta yafitoshi da hannu, cikin takun nan nasa na izza da ƙasaita ya nufeta. Littatafai biyu masu girma da tudu sosai-sosai ta nuna masa. “Ciro min su”. Hannu ya kai a hankali yana ɗan yamutse fuska ya cirosu, duk sunyi ƙura, amsa sai ta shiga karkaɗesu, yanda ƙurar ke tashi sama ya sashi ja da baya har sai da ta kammala. Ƙara yafitosa tai da hannu ya sake dawowa gabanta, ta kamo tattausan hanunsa cikin nata ta ɗaura masa littattafan. “Wannan zasu taimaka maka samun duk amsar da kake nema, duk wanda ke cikin zuri’ar nan da aka haifa da tambarin ko akai masa akwai bayaninsa anan. Ka kula da ƙyau suna da muhimmancin da ba kowa yasan inda suke ba a cikin wannan masarautar”.
Kai ya jinjina mata yana lumshe idanunsa da buɗewa a kanta……
Taso share umarninsa na ta samesa bayan sallar isha’in amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai. Sai ma ta samu kanta da yin sabon wanka da canja kayan jikinta zuwa wata ƙyaƙyƙyawar abaya mai laushi da santsi kalar fari da akaima adon manyan fulawa da golden mai ɗaukar idanu, ga stones taji farare da duk inda ta motsa sai sunyi ƙyalli kamar wani diamond. Samun kanta tai da nutsuwar naɗa veil ɗin ya zauna ɗam a kanta har wani ɗan gashi siriri data zubo ta gaban goshin na reto a fuskarta. Tayi ƙyau matuƙa, dan ko maƙiyinta sai yaji ta burgesa kasancewar Iffah yarinya ce mai shiga rai, ga ta ƙyaƙyƙyawa komai nata dai-dai da ita. Yau dai har an ɗauki turarurrukansa za’a bulbula sai kuma aka fasa. A cikin wanda tai shopping akai amfani da su, sai kuma aka koma dai aka saka nasan ƙaɗan. Yanda tayi haɗin sai ya bada wani irin ƙamshi mai sirrin da ko shi mai gayya mai aikin da wahala ya iya gane ainahin nasa ƙamshin. Taku take a nutsenta kamar wata ƴar wahainiya. Bedroom ɗin jiya ta nufa dan tafi tunanin samunsa a can duk da bata da tabbas…..