Daudar Gora Book 2 Page 80
jami’an mu ya ga wani a suffar ɓadda kama ya fito ta wata ɓarauniyar hanya da muma bamu san da ita ba a gidan nan. Munbi diddigin masu bin hanyar a tsahon kwanakin nan daya tilasta jinkirinmu, mun samu mutane huɗu sai dai har yanzu bamu tabbatar da fuskokinsu ba kasancewar a shirin ɓadda kama suke fitar. Amma hakan ba matsala bane saboda hanyar tabbatar da su ɗin su waye tana a hanunmu muna kan sake tabbatarwane gudun samun kuskure. Albishir dai da zamu bayar akan shi wannan case ɗin a yanzu haka wanda ya samar da dafin macizan yana hanunmu. An kamosa ne kuma a safiyar yau”.
A karan farko Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ya saki wani malalacin murmushi da ya nema sumar da Miran Arshaan da ke jin kamar ya rumtse ido ya gansa a sashen sa ko clinic wajen Miran Jasim ko ma wajen boka Barbushi shi ma bai san ina yafi so yaga kansa ɗin ba. Sayeed Fayzul-haq kam kansa kawai yake faman jinjinawa ransa na mamakin waɗan nan abubuwa abin kamar wani shirin film. Amintaccen hadimin Tajwar Eshaan kam abun ya masa daɗi, musamman ganin murmushi mafi tsadar gani a fuskar shugabansa adali, sannan koba komai a su kansu ma amintattun hadimansa suna fatan kowaye ɗin kodan wahalar da suka fuskanta ta kusan wata guda a kurkuku. Shi dama ya daɗe daji a ransa Zawjata-almilk bazata iya aikata abin nan ba sai da jagorancin wani sheɗanin da ya fi ƙarfinta. Dan haka kawai yake jin ƙaunarta matuƙa musamman da ya fahimci wani abu ɓoyayye da ke tare da shugabansa game da ita duk da yana ƙoƙarin ganin ya danne. Amma kuma shi a yanzu babu wanda ya kaisa sanin wanene Tajwar Eshaan, koba komai barci ne kawai ke rabasu sai ko idan ya shiga ciki ko ya yini bai fito a bedroom ba. Kuma ko’a hakan tabbas tabbas sai ya gansa a yinin sama da sau biyar. Zai iya cewar da ga matarsa a yanzu sai shi ko a mafi ƙololuwar ganin Tajwar Eshaan ɗin.
Wani irin kirari ya shiga jeroma shugaban jami’ai, tare da jinjinar ban girma na ƙoƙarin sa da yawun Shahan-shan da bayan murmushi babu alamar zaice wani abu. Magana da ga bakin amintaccen Tajwar Eshaan tamkar kai tsaye ne da ga bakin sa, dan yana cewa ne da say ɗin sa bawai raɗin kansa ba. Sannan koba komai shima a idanunsa Tajwar Eshaan ɗin ya saki murmushin nan da zai iya rantsuwa bai fi a karo na ƙalilan kenan ya taɓa gani ba. Hakan na nufin da gaske Shahan-shan ɗin ya yaba da ƙwazon jami’an tsaron gidan koda bai furta ɗin ba.
Jiƙewa iya jiƙewa jikin Miran Arshaan ya gama yi da zufa. Ga wani irin hajijiya da idanunsa suka fara gani. Kaɗan ya saci duban Tajwar Eshaan da babu alamar hankalinsa a kansa yake, hakama Sayeed Fayzul-haq. Yawu ya haɗe masu kaurin da har yanajin suna kamar ɗaɗa masa maƙoshi. Da ƙyar ya iya jarumtar cigaba da zama har shugaban jami’an tsaro ya gama ya fice. Babu alamar Tajwar Eshaan zai sake cewa wani abu akan batun, hakan yasa shima Sayeed Fayzul-haq haɗiyewa ya ɗakko zancen Miran Jasim da iyalansa, sai ɗansa dake a sashen Malikat Haseenat har yanzu. Ba ƙaramin dauriyar danne tashin hankalinsa yay wajen saka musu baki ba gudun kar Tajwar Eshaan ya harbo jirginsa. Dan ya mugu-mugun sanin hatsabibancin yaron nan, babu abinda ya baro a halin ubansa sai ma finsa taurin kai da yayi. Tattaunawar ta ɗan jasu wani lokaci dan har gab da magrib sannan suka tashi….
A bala’i bala’in matsanancin tashin hankali Miran Arshaan ya nufi clinic, yaji daɗin samun Miran Jasim da ke tambayarsa lafiya ganinsa a firgice shi kaɗai. Maimakon amsa masa sai ca yay, “Kasa a sallameka da ga clinic ɗin nan a daren nan”. Cikin kallo
mamaki Miran Jasim ya ce, “Kamar ya nasa a sallameni, kai bakaga yanda shegen yaron nan nawa ya fasan kai ba. Ga wuyana tsabar yanda ya nema karyashi sai da aka samun wannan abun”. Ya kare maganar da nuni da abin wuyansa. Tsaki Miran Arshaan yayi yana ji kamar ya sake shaƙesa shima. “Shaƙar da Husam ya maka ba komai bace akan wacce ke tunkaro rayuwarka”. Ya ɗan ƙara waw-wai-gawa alamar gudun kar wani ya jisu. Cikin sake ƙasa da murya ya cigaba da faɗin, “Idan ka bari ka sake awa biyu anan nadamace ta har abada zata zama abokiyar rayuwarka in har ma matsiyacin yaron nan ya Barka da ran naka kenan”. Yana ƙare faɗa ya ficewarsa da ƴar sassarfa dan dama yay amfani da lokacin shiga sallar magrib da akayi ne…..
Bayan idar da sallar isha’i koda ya nufi sashensa maimakon ƙarasawa ciki sashen Malikat Haseenat ya nufa ta ɓoyayyar hanya. Tayi sallamar wutiri kawai sai ganinsa tayi. Ba yau ya saba mata irin wannan zuwan ba na sirri, sai dai yafi yinsa a bayan sallar asuba. A nutse take dubansa bayan shafa addu’ar data taƙaita cike da kulawa. Shima sai ya taso a hankali da ga zaman ƙasaitar da yay a bakin gadonta ya dawo inda take kan lallausan carpet ɗin dake fes babu datti sai ma tashin ƙamshi da yake da ɗaukar ido na sabunta. Ga taushi matuƙa da ko’a ido zaka iya fahimtar hakan. “Barka da dare Jadda-ti”. Ya faɗa a can ƙasan maƙoshi ya na kaiwa kwance bisa carpet ɗin ya ɗaura kansa kan cinyarta ya wani lumshe idanunsa da a kallo ɗaya ta fahimci damuwar dake tattare da shi a cikinsu tama ƙaru fiye da ɗazun. Murmushi ta saki mai sanyi a ranta tana faɗin, (Yau kuma ƴan shagwaɓan ne a kusa haka), a zahiri kam hanunnta kawai ta ɗaura kan ƙyaƙyƙyawar baƙar sumar sa siɗik ta fara ɗan tausa masa kan kaɗan-kaɗan. Idanun ya sake lumshewa da ƙyau har yanajin barci-barci na ɗibarsa. Tsahon mintuna kusan uku sannan ta magantu cike da kulawa.