Daudar Gora Book 2 Page 76
Lips ɗinta tai wani irin turawa tana ƙwaɓe fuska, ita ala dole taji haushi yace mata mayya, “Ni ALLAH ya kiyaye na zama mayya. Tsorona kuwa tun randa ka fara ganina mana, kuma inba tsoro ba miya maidaka Ajmaal ka dinga naɗar min sirri…”
Yanda ta ƙare maganar da yin takwaf-takwaf da fuska kamar zatai kuka ya sashi jan wata irin wawuyar ajiyar zuciya jin numfashisa na fisga, kansa har ya fara masa ciwo saboda ya gaji da surutun, itako oganniyar ya fahimci ko’a jikinta ma. Cikin nuna alamar gajiyawar har cikin harshensa ya ce, “Ashe dai ni kike jin tsoron, saboda na kasance Ajmaal duk wani sirrinki na sani?”.
Idanunta da ke rufe ta buɗe fes a kansa, cikin son dakewa ta ce, “Hu’im lallai ma tsoro fa? To kaima ai naka sirrin na a tafin hannuna basai na faɗa ba”.
“Ni ɗin?”.
Ya faɗa a fisge yana waro duk girman idanunsa kanta. Jikinta tai ƙoƙarin janyewa da ga nasa dariya na taho mata ganin yanda ya waro idanun, a nata ganin ai ya tsorata ne. Sake riƙota yay suka koma daf-daf fiye ma da ɗazun, cikin wani salon da ke neman girmar kanta ya kai hancinsa kan wuyanta yana busa mata numfashinsa. Da wani irin karyayyar murya data sata zabura can ƙasan maƙoshi ya ce, “Faɗamin wane sirrina kika sani? Na yi alkawarin zan ƙara miki da wani ma yanzu duk ki haɗa”. Yanda yay maganar numfashinsa ma sauka saman wuyanta tare da murza hannunsa wajen ciwonta batare daya fargaba babu shiri ta zabura zatai magana, rufff ya rufe bakin da tausasan pink lips ɗinsa. Ɗifff komai na jikinta mai aiki da motsin ruhinta ya tsaya cak da aikin na wucin gadi kamar yanda nashi ya kasance. Idanunsa ya lumshe a hankali da sake buɗesu kan fuskarta, kafin ya kai hannunsa baya ta ƙeyarta ya tura yatsun kan tattausan gashinta, a hankali ya fara warwaro ribbon ɗin data ɗaure gashin a tsakkiya da juya lips ɗin nasa kan nata ya mirginata suka sake komawa kan hannayensu ta ɗaya ɓarin yanzu ma suna fuskantar juna. Wannan ne karo na farko da hakan ta faru a tsakaninsu, abune kuma da bai taɓa faruwar ba, hakan ya sata shiga cikin ɗimuwa da gigita, dan da wani irin salon dake neman ɗage numfashin nata da ga gangar jikinta yake juya lips ɗin nata cikin nashi tamkar ba Shahan-shan ɗin nan ba mai tsananin miskilanci da izza da ƙasaitar mulki, wanda hatta magana wahala take masa. Murmushinsa kam abune mafi tsada ga duk wanda ya sanshi. Gaba ɗaya duk sai ta daburce jikinta ya shiga rawa, ciwon ma da ƙafar ke mata da ƙugun ta nemesu ta rasa… (Bily ki kiyayi kanki)
Da alama Shahan-shan Eshaan ya tafi, tafiya irin mai toshe kunne daga jin ko wane irin motsin sauti da ke a doron duniya, dan dukkanin takaicinsa akan waɗan nan lips ɗin masu masa tsiwa yau da alama sai ya hucesu. Ita kanta ɗalibar tasa tun zaburar farko da tai na dawowa hayyaci bata sake motsin kirki ba. Sai da taji hannunsa na ƙoƙarin shiga cikin ƙaramar rigarta ta sake zabura da ƙoƙarin dafe hannun nasa da nata tana son janye lips dinta da ya riƙe da nashi cikin kar-kar-war jiki. Babu alamar zai bata damar da take buƙatar, dan da gani dai yayi zurfi shi kam. Da sauri tasa dukan ɗan sauran ƙarfinta wajen jan jikinta baya, kamar zai riƙota sai kuma ya barta yana mai rumtse idanunsa da sukai wani irin mahaukacin kaɗawa jazur da ɗan ƙarfi. Baya ta juya masa tana mai dunƙule jikinta dake tsuma har yanzu waje ɗaya. Tunda Ummu ta haifeta tai hankali tai wayo babu wani da ya taɓa kai hannunsa inda Tajwar Eshaan ɗin ya kai yau a jikinta, kai itafa ko riga bata yarda ta saka gaban su Arfa ma dake yayunta tsabar yanda take jin kunya. Amma yau sai ga abinda batai zato ba, da ga mutumin da batai tsammani ba, wayyo ita Fhareedah ta ga takanta. Wani irin yarrrr yarrrrr take ji kamar har yanzu hannun nasa na’a jikin nata ne tsabar yanda ta firgita. Ɗaya da ga cikin filos ɗin da aka ƙawata gadon ta fisgo ta ƙanƙamesa a ƙirjinta dan ta kasa nutsarwa waje guda, da gaske ta tsorata tsoro irin wanda batajin ta taɓa shigarsa a rayuwarta, sai kawai wasu hawaye masu ɗumi da bata san na minene ba suka shiga rige-rigen sakko mata a kan fuskarta.
Ajiyar zuciyar da take ja mai tafiya da kamar shashshekar kuka-kuka ta sakashi buɗe lumsassun idanunsa da sukai wani irin shanyewa sosai, akan bayanta data juya rigar ta ɗage sosai saboda tattareta da yayi ya sauke su. Ya ɗan rufe ya ƙara buɗewa yana mai ƙarema bayan nata fari sol kallo. Wani irin harbawa zuciyarsa ta sakeyi da ɗan ƙarfi lokacin da idanunsa ke sake sauka kan wannan dai tawadar ALLAHr babba da ke a ɗan sama-saman bayan nata ta gefen kafaɗar dama. Da sauri yake ɗan girgiza kansa alamar hakan bazai yuwuba kama ce kawai da ga ALLAH. Ta inama hakan zata faru? (Kai noo.. noo.. ba haka bane) ya faɗa a cikin ransa da kaushi sosai yana ɗauke idanun nasa da ga wajen. Sai ma ya miƙe a matuƙar kasalance, zama yay ya ɗan bata baya, cikin muryarsa dake a matuƙar sarƙe ya furta, “Ga wani sirrin nan nawa na baki ki haɗa ki adana min”.