Daudar Gora Book 2 Page 57
Bayan kamar mintuna ashirin da tafiyar Iffah sannan shima ya mike, zuwa lokacin ruwan ya tsagaita sai ɗan yaf-yaf da akeyi ga garin ya ɗauki wani irin sanyi mai ratsa ɓargon jiki. A hankali ya lumshe idanunsa ya buɗe a kan sararin samaniya da tai wani irin fayau, ga garin yay luf-luf ƙamshin ƙasa na ratsa hancinan mutane. A kan lips ya shiga furta addu’ar nan ta bayan saukar ruwan sama.
*مُطِرْنَا بِفَضْلِ اللهِ وَرَحْمَتِهِ.*
_Mutirna bifadlil-lahi warahmatih._
(An yi mana ruwa saboda falalar ALLAH da Rahamarsa).
Kafin ya cigaba da tafiya cikin takun nan nasa na ƙasaita da izza tamkar mai irga steps….
★★…..
Tunda ta dawo ɗakin kaikawo kawai take faman yi hankali a tashe. Duk nacin son sanin wanene Ajmaal ɗin da takeyi bata kawo a ranta zai zama shi ɗin ne ba. Tunaninta kawai ya kama Ajmaal ɗin ne kodai wani abu da ba shi take zato ba yana mata yawo da hankali ne. Ji take komai ya kwance mata, komai ya ƙare mata. Ta sadaƙar dan tata ta riga ta ƙare kawai. Yaya akai hakan ta kasance, yanzu komai daya wakana tsakaninta da Ajmaal da Shahan-shan ɗin ne kenan? Kai ina impossible, taya hakan zai kasance ma? Miyasa sir Fawzan zai mata hakane? Miyasa? Miyasa ya rabbi shike nan ita kam.
Yanda take yi dolene ya baka tausayi da dariya. Ƙululu taji cikinta ya murɗa kamar mai jin gudawa. Ta kai hannu ta matse cikin ƙirjinta kamar zai tarwatse dan tashin hankali da tsabar ruɗanin da take ciki…..
“Nace na gama da ke ne?”.
A wani irin haukace ta ɗago ta kalla ƙofar jin sassanyar muryarsa bazata a cikin kunneta, shi ɗinne dai tsaye hannayensa duka cikin aljihun wandon jikinsa. Sam bataji shigowarsa ba, koda yake a buɗe tabar ƙofar tsabar ruɗani. Tafiya ta farayi da baya-baya, jin zata ma iya sakin gudawar a wajen sai kawai ta sake kwasa da gudu tai hanyar toilet.
idanunsa ƙasa-ƙasa a kanta. Da wani irin sauri ta buɗe idanunta da ɗagowa ta kallesa tana sakin nannauyar ajiyar zuciya saboda shock da furicin nasa ya sakata. Sai kuma ta kaudar da kan gefe dan salon kallon nan nasa birkita ta yake. Muryarta can ƙasa-ƙasa ta jinjina masa kai.
Ya faɗa a fisge kamar wanda akaima tilas. Tsabar yanda take jin kusancin nasu kamar zata shiɗe a hankali ta ce, “Uhhm”.
Ɗan sake matsawa yay gareta dab har tana iya jin saukar numfashinsa a kan fuskarta. Jin saukar yatsunsa kan haɓarta ruf ta rufe idanunta da ƙoƙarin riƙe rawar da jikinta ke neman farayi. Ya ɗan lumshe idanunsa dake yawo akan fuskar tata yana ƙoƙarin shanye murmushin dake taso masa. A bazata kawai taji saukar lallausan lips ɗinsa saman goshinta ya manna mata sumba mai lafiya da har sai da ta saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfi. Batare da ya sake cewa komai ba ya ja da baya ya juya ya bar ɗakin fuskarsa shimfiɗe da murmushin da duk sonshi da basar da shi hakan ya gagara. A ransa rayawa yake (Damisar takarda ga tsoro ga ban tsoro)
Da kallo ta bishi har ya fice, ta sauke ajiyar zuciya da kaiwa zaune jagwab kamar wadda tasha gudu ta gaji, sai faman matse jikinta take waje guda amma yaƙi daina tsumar dole ta kai kwance na wani ɗan lokaci, badan taji ƙarfi ba dai ta miƙe tai sallar ganin lokaci zai shige….