Daudar Gora Book 2 Page 4
Ni a ganina ɓacin rai ko damuwa bashi ne zai zame mana mafita ba. Mu zauna mu tattauna yanda abinda ya dace kafin lokaci ya ƙure. Ban san miyasa Mammah ta ɗauka al’amarin nan da rashin muhimmanci ba. A yanda nake ji a zuciyata da tuni labarin wata akeyi ba yarinyar nan ba. Dan banga dalilin da zaisa ace wai sai anyi bincike za’ai mata hukunci bayan komai data aikata a bayyane yake, wannan tamkar muna nuna rashin muhimmancin ran yaronmu ne ma ai…..”
“Gaskiya kam Arshaan Akhi”. Miran Jasim ya tari numfashinsa da sauri, cikin nuna ɓacin rai shima ya cigaba da faɗin, “Ni kaina komai na kasa fahimta musamman akan ra’ayin Mammah. Sai nake ganin bata damu bane? Ko kuwa tafi son yarinyar sama da gudan jininta? Inba hakaba minene na waɗan nan sharaɗin marasa tushe? Bayan komai a bayyane yake. To gashi tace sai anyi bincike, amma dai-dai da cctv footage an nema an rasa tabbacin komai shiri ne. Inada yaƙinin komai sai dai yarinyar nan ta shirya kafin ta shigo masarautar nan. Dan binciken mu ya nuna ta aurensa ne dama domin ɗaukar fansar ƴan uwanta guda biyu, shiyyasa ta kwantar da kai ta shiga jikinsu musamman Mammah da Akia Ammarah da a yanzu suke nuna goyon bayansu kan cigaba da rayuwarta sai kace sun manta matsayin wanda taso halakawa a gare su…
Maganganunsu sake hargitsa Malikat Bushirat suke da tunzurata. Tuni jin zafin Malikat Haseenat da tsanar Daneen Ammarah ya sake bunƙasa a ranta. Dama kullum Jasrah cikin munana Daneen Ammarah ɗin take a wajenta yanzu bisa huɗubar Miran Arshaan, dan tafi kawo mata zancen duk motsinsu a masarautar fiye da kowa, musamman daya kasance ra’ayinsu ya babanta da nasu akan hukunta Iffah. Yanda take sake kumbura jira suke kawai suji tace wani abu, amma kasancewar ta mace mai bahagon hali dama fahimta ko uffan da suke so bata tofa ba, sai cika take dai tana batsewarta ita ɗaya. Duk yanda suka cigaba da fanfatan kuma batace ɗin ba har lokacin samun damar ganin Tajwar Eshaan yay a gareta, dan tunda abin ya faru suma ɗin basu samu ganinsa ba kasancewar akwai doka mai haɗe da babban tsaro akan ganin nasa ga duk wanda ya kwana ya tashi a daular ta ruman, su kansu bisa tsayawar Malikat Bushirat ɗinne da itama sau ɗaya take da hurumin ganinsa a rana zasu ganshi yau ɗin.
Duk wani motsi da shiga da fitar jama’a a ƙarƙashin saka idon masu tsaron sashen yake a yanzun. Tako ina ka waiga cctv camaras ne. Su kansu ma’aikatan cikin sanya ido suke a kowane motsin tsakaninsu dan a yanzu kowa bai yarda da kowa ba ake. Sun sami tarba daga ƙwararren likitansa daya kasa ya tsare, yana hakane kuma bisa umarnin Malikat Bushirat ɗin. Cikin girmamawa ya gaidasu, batare da damuwa da yanda suka amsa masa cike da isa da ƙasaita ba ya jagorancesu zuwa ɗakin da aka warewa Tajwar Eshaan ɗin domin jiyya. Ɗakine tamkar asibiti, dan komai zaka samesa na aiki ingantattu da kowace ƙasa zata iya alfahari da shi. Dan ƙasar ruman na ɗaya daga cikin ƙasashe masu ƙwararrun likitoci da duniya ke alfahari da su tako wane fanni. Hakan yasa hatta shi kansa Shahan-shan dan yana ciwo bai ƙetare ƙasar haihuwarsa, kai sai ma dai su azo tasu ƙasar neman lafiyar saboda ingancin su….
Zaune yake a gadon marasa lafiyar bayansa jingine da tausasan filo da jikin gado da aka ɗago, duk da ya ɗanyi rama ƙyawun haibarsa da kwarjini na manne da cikar kamalar fuskarsa. Yayi fayau da shi da ƙara hasken daya bayyana bakin kwantacciyar sumar kansa data kumatunsa zuwa haɓa, light blue ɗin kayan jiyyar da suma suka ƙara fitar hasken fatar tasa tar-tar ga mai kallo sun masa ƙyau kamar ya saka ne domin ado. Sai manyan idanunsa da har yanzu fatarsu ke a ɗan kumbure alamar dai yana cikin halin jinya. Duk da jin an shigo bai motsa ba idanunsa nakan lap-top ɗin da yake sarrafawa cike da nutsuwa da ƙasaita.
Daga Miran Arshaan har Miran Jasim sukai turus alamar mamaki, dan sam zukatansu basu ayyana musu samunsa a haka ba musamman yanda likitansa yaƙi cewa komai game da zungurar da ƴan jarida ke masa akan son sanin halin da Tajwar Eshaan ɗin yake a yanzu. Saboda tun washe garin da suka tattauna da ƴan jarida basu sake cewa komai ba akan yanayin jikin nasa. Malikat Bushirat da hankalinta gaba ɗaya ke akan gudan jinin nata ta ƙarasa garesa fuskarta ƙawace da murmushi. Sai da taja kujera ta zauna a gefensa kaɗan ya ɗan ɗago saboda shigar ƙamshin turarenta cikin hancinsa….