Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 2

Sponsored links

Yau kwanakinta uku cif a cikin ɗakin da aka garkameta mai tsananin duhu da bata iya banbance dare da rana, sai ɗan hasken da kan leko ta window dake can sama karami na hasken rana ko wutar lantarki. Ta matuƙar zama wujiga-wujiga da fita a hayyacinta dalilin ƙin cin abincin da ake kawo mata sau ɗaya a kowane yini, sai madara. Tun a ranar farko ta gama fahimtar akwai babban ƙuli da ya kamata ta fara fahimta kafin zuwan wannan lokacin. Zuwa yanzu ta gama fahimtar su Miran Jasim sunyi amfani da ita ne, sunyi amfani da ita duk da itama da wannan ƙudirin a ranta. Sai dai kuma cika baki ne kawai, ta fahimci a hakanne a randa ƙaddarar dake tafiya da rayuwarta ta yanzu ta tabbata. Dole ta kira hakan da ƙaddara, dan inba ƙaddara ba babu ta yanda zata iya cutar da waninta mai bautar ALLAH da hanunta. Ƙwarai da gaske tanajin zafi, matuƙar zafi na rasa ƴan uwanta guda biyu a dalilin auren Shahan-shan. Hakan kuma shine ya zama sanadin komai na jin kangarewar zuciya da ƙudirin da babu tabbacin iya aiwatar da shi. Komai ya nema canja mata a lokacin da tai tozali da fuskarsa, bata san dalili ba ta dingajin kamar shi bazai iya kasancewa mai cutarwa ba, ta dinga jin dole akwai abinda yake ɓoye da ya kamata ta sani, sai dai a lokacin data gama shirinta tsaf akan hakan ƙaddara ta sake sauyata, komai ya nema rushewa a zuciyarta batare da riƙe wata makama mai ƙwaƙwarar hujja ba ta yanke hukunci ga wanda bata da wata hujja ko shaida akansa, wanda maimakon ya bada umarnin ɗaukar mataki a kanta ya nuna mata hanyar kuɓuta ta hanyar bata umarnin zubar da madarar da bata san yanda akai takaita gareshi ba. Amma kash, da alama ƙoƙarinsa na kubtar da ita bai tabbata ba. Dan gashi maƙiyansu da alamu suka nuna shirinsu bana yau bane sun gama cin nasara, nasara biyu a lokaci ɗaya, kaudashi da kaudata itama batare da ta san mi taci burin son sani ba. Sai ma sake tsunduma a duhuwa tayi. Dole ta kira gaɓar da suna duhuwa, dan tanada tambayoyi masu ɗunbin yawa akan kanta ma. Mafi girma a ciki sune taya Ajmaal ya zama Shahan-shan? Wake halaka matansa idan har ya kasance ba shi bane? Miyasa bai iya cewa komai bayan shine keda hakkin cewar? Da gaske ta rasa iyayensu suma da ɗan uwanta tilo daya rage kokuwa duk cikin shirin su Miran Arshaan ne?…. Shi kansa Sir Fawzan tana da bukatar sanin wani abu a kansa. Sai dai ta yaya? Ta wace hanya? Duk yanzu bata sani ba. Zafafan hawayen da a kwana ukun nan bata taɓa gwada sharewa ba suka sake zubowa masu zafi. Ta lumshe raunanan idanunta murmushi mai ciwo na suɓuce mata. Fuskarsa take kallo a kan allon zuciyarta a lokacin da yake sakar mata murmushin da har abada bazai taɓa zama mai gogewa ba a tarihinta. Siririyar dariya da tafin dake shiga kunnenta a bazata ya saka ɓacewar murmushin kan fuskar tata da buɗe lumsassun idanun nata lokaci guda..

 

Kanta ne ya sara da ƙarfi, da sauri ta maida su ta rumtse sakamakon hasken daya ratsasu mai kaifi, yau kwananta uku tana a cikin duhu, dolene karfin idanunta ya samu rauni a lokacin da aka samar da haske cikinsu. Duk yanda taso sake buɗewa ta kasa, dan har cikin kwakwalwarta taji shigar kaifin hasken na bazata. Ta cije lips a hankali tana mai ƙoƙarin ganin ta riƙe hawayenta da son danne tasirin raɗaɗin dariyar izgilancin da bata san daga wanda take fita ba. Sai dai zuciyarta na bata Miran Jasim ko Miran Arshaan ne. Bata da ƙarfin tashi daga kwancen da take, dan haka tai jarumtar sake buɗe idanun nata sannu a hankali a karo na biyu, zuciyarta na ambaton (Hasbinallahu wani’imal wakil). Da ƙyar ta iya tsaidasu akan Miran Jasim dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya bisa kujerar da basai tayi wani tunani ba da ita aka shigo masa. Raɗaɗi idanun ke mata, gasu a kumbure jajur amma haka tai jarumtar cigaba da tsaidasu a kansa harya gaji dan kansa daga dariyar yay shiru..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button