Daudar Gora Book 2 Page 161
*Bazan iyaba, nace bazan iyaba uwa. Wihy why, kinji na rantse, bazanyi asarar wahalata ba. Sai dai ni da ke duk muyi mutuwar kasko”
“Kece da danki zakuyi mutuwar kasko, kuma dole ki bamu jinin Ajlaan madadin sauran ayyukanmu da baki cika ba!!”.
“Har abada, har gaban abada jinin Saiful-malik yafi karfinki azzalumar mushirika. Nima da kike gani hatsabibiyar kainace uwa, dan tun kafin ke gwanace a iyawata!!”
“Kin san da iyawar taki miya hanaki iyama kanki sai da taimakona. Butulu ke wacece, har wacece ke nace ta-kurya? Har mi kike takama da shi? In ce dai Ajlaan ne ko? Kuma mune muka samar miki da shi a lokacin da kike neman samuwarsa do rufe (Wa’alaikissalam šALLAH ne kadai ke badawa da hanawa a lokacin da yaso, ga kuma wanda yaso. To ki rubuta ki ajiye mune zamu shafe babinsa da tarihinsa, kamar yanda muka shafe na ubansa da kakansa a doron duniya.Idan kin isa, Kin cika sunanki tsagera mu zuba!!!!”
Bat uwa ta bace a akin kamar tashin guguwa. Wani irin fashewa da kuka Malikat Bushirat tai cikin ihu da fisgo duk abinda ya tare mata gaba ta dinga ratsawa da kasa. Jikinta want rin jiljigar rawa yake na masifa, da ga karshe ma kawai sai ta yanke jiki ta fadi dan jini ya balle mata sosai saboda raunikan da ta jima kanta a dalilin fashe-fashe.ā¦
Bayan idar da sallar magrib dunbin al’ummar dake cikin masarautar ruman suka shaida daurin auren Zayyan ibn Abbas Jumna. Da amaryarsa Ammarah bint Abdul-majeed Aliy Qutb, akan sadaki mai darajar gaske, inda Kaka ya zama waliyyin ango, Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majee
d Aliy Qutb ya zama waliyyin amarya. Ba mutanen daular ruman bane kawai suka girgiza, masarautar ce gaba dayanta ta girgiza da wanna al’amari na bazata. Duk da ana cikin dunbin jimami na abubuwan da suka faru a kotu yau, babu wanda yay zato ko tsammanin faruwar abinda ya farun kamar haka ba. A take sabon topic ya sake barkewa a saman wanda dama aka yini anayi har
a cikin hadimaiā¦
Tun bayan sallar la’asar da suka shigo da su Kaka bata koma ba tana a sashen nasa. Dan sanda zasu fita domin gabatar da sallar magrib har zata bisu itama Malikat Haseenat ta dakatar da ita. Kasancewar sallar magrib da ake kira ita da shi babu wanda yacema dan uwansa komai. Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke a bayan fitarsa sallar, sai kuma ta shiga wanka dan a karo na farko tun bayan samuwar cikinta yau ne take jin zazzabi a jikinta. Doguwar riga mara nauyi kawai ta saka ta tada salla, bayan ta idar ta zauna komai na dawo mata daki-daki kamar wani shirin film. Kuka sosai tayi fiye da wanda tayi a dazun, a haka kunnenta ya tsinkayi shelanta sake aura auren mahaifanta guda biyu da kaddara ta hada. Kuka ta sake rushewa da shi har kanta na mata ciwo batare da tasan dalilinsa ba. Shin farin ciki ne ko sabon rudani, da kyar tai sallar isha'”i ta zame akan abin sallar ta kwanta…..
Tana kwance a wajen cikin yar takurewar sanyin zazzabin da take ji ya shigo dakin da sallamar nan tasa ciki-ciki. Bata motsa ba har ya karaso gabanta, jin tsaiwarsa a kusa da ita ya sata bude idanun a hankali ta sauke kansa. Kallon juna suke kamar yau suka fara ganin kansu, kafin itama ta fara janye nata idanun ta mike a hankali. Ganin yanda take dan layi na wandda jiri ke kwasa ya sashi mika mata lallausan farin hannunsa sol mai dauke da dogayen farata. Nata ta daura a hankali cikin nasa, ya dagata gaba dayanta ta mike tsaye a gabansa. Yanda yake binta da kallo kamar sabuwar halitta ya sake raunana mata zuciya, sai kawai ta sakar masa wani shagwabebben kuka da fadawa jikinsa ta kankamesa. Bashi da zabin da ya wuce amsarta hannu biyu shima ya kara matseta a jikin nasa yana mai lumshe idanunsa dake cike da so da kaunarta. Kuka take sosai dake sake sukar zuciyarsa, sai dai baice mata uffan ba har kusan tsahon mintuna uku suna tsayen. Sai da yaji ya daina jin dumin hawayenta dake sauka masa a kan kirji ta koma sauke ajiyar zuciya sannan ya dagota. Mayafin da tai rolling ya warware, yaja hanunta a hankali ya zauna a bakin gado ita kuma ya daurata a saman cinyarsa.
“Shi kukan baya isa ne”.
Ya fada a fisge fuskarta a cikin tafukan hannunsa. Fuskar ta sake kwabewa zata saki wani sabon kukan ya girgiza mata kai da fadin, “Please bana son gani kuma, kin cika shagwaba fa”. Shaaa hawayen suka zubo dan ta kasa rikesu, sai kuma ta turo masa baki gaba. Murmushi yayi a zuciyarsa, tare da matso fuskarta dab da tashi ya tura yatsunsa cikin gashin kanta ya zare ribbon din data dauke gashin a tsakkiya ya shiga yamutsa mata shi yana goga mata hancinsa kan nata, lips din ta sake dan turowa, shiko ya samu damar hadesa da nashi kirif. Iya kokari yayi na ganin ya tsaya iya hakan, sai dai zuciyarsa gaba daya taki bashi hadin kai. Sai kawai ya zarce da abinda gangar jikinsa ke tsananin bukata da kwadayi, da ga haka labarin ya canja da salo mai matukar nauyi dake kara tabbatar musu yanda suka narke a so da kaunar juna mai tsananin gaske.