Daudar Gora Book 2 Page 155
¡kirani yake sanarmin ya fahimci Zayyan ya kamu da soyayyar matar aurensa ta sati biyu dan haka a karo na farko yana son nayi wani abu, ya kuma tabbatar min ba shirka bace kamar yanda nake dauka dan shi ba mushiriki bane. Komai sai da ya zayyane mun, dan haka na dauka alwashin bibiyar al’amarinta har sanda zata haihu kamar yanda mahaifina ya bani umarni. Shi kuma ya sakashi baro cikin Jumna dan yace ya tabbata za’a iva zuwa nemansa, za kuma a nemesa a ko’ina dan haka yace yaje cikin Dahab City din inda bazasu taba tsammanin zasu samesa a kusa da su din ba, wannan ne dalilin dawowar Zayyan wanna gari, su kuma su Abbas ya sakasu dawowa cikin gidanmu yanda mutane zasuyi tunanin suma sun gudu. Haka kuwa akayi, bayan tafiyarsa da kwana biyu shi da matarsa da yaransu uku sai gashi anzo nemansa. Sai dai iya bulayi basu samesan ba, da ga baya dole suka hakura. A wannan dan tsakanin Abbas ya kamu da rashin lafiya ta kwana hudu kacal ALLAH yay masa rasuwa. Wannan mutuwa ta gigitamu matuka,hakama matarsa da Zayyan. A wajen zaman gaisuwar Abbas da Zayyan ke zuwa a sirrance ya hadu da Abu Musa, wanda shine silar masa hanyar kai zuma cikin masarauta dama abokinsa ne na yarinta. A tsorace yazo ya sanarma mahaifina abinda Abu Musa yazo masa da shi. Sai yay murmushi tare da kwantar masa da hankali tare da bashi kwarin gwiwa saboda wani hasashe da yace yayi akan hikimar cigaba da zuwan nasa masarautar. Duk da shima yana da mai kawomasa duk wani rahoton da yake so na cikin masarautar, a haka nema muka san samuwar cikin Fhareedatu, wanda kuma yay dai-dai da samuwar ciki na hudu ga diyata matar Zayyan itama. Abubuwa sun cigaba da kai da kawo har zuwa ranar haihuwa, a lokacinne kuma mahaifina yasa na shirya yin abinda ban taba yi ba. Wato aiki da kayansa. Alhamdullah sai kafin ma nai wani yunkuri sai ga kiran mahaifina da ga masarauta wai zasuyi aiki. Da farko banyi niyyar zuwa ba dan shi mahaifina bazai iyaba saboda ciwo, amma sai ya zaunar dani yay min bayanin komai dama ban hasaso ba. Tunda dama ni nayi shirin shiga masarautar ne kawai na dakko abinda za’a haifa na fito kamar yanda ya sani sai a yanzu kuma labari ya canja. Bani da ikon bijirema umarninsa, kamar yanda shima bashi da ikon bijirema kiran masarauta dan haka na shirya zuwa kamar yanda ya umarceni tunda a duk abinda ya sanin banga shirka ko wani tsafi a ciki ba. Ina cikin shirin tafiya masarautar a dai-dai lokacin sai ga labarin haihuwar Fhareedatu da ga bakin amintaccen mahaifina. Wannan shine ya zaburar dani zuwa a gaggauce. Lokacin dana iso bokanyar ta riga ta gama shirya komai da su basuyi zato da tsammani ba ma, amma duk da haka nai iya kokarin da zan iya na mata kiranye da hadata ita da yan kayanta na Koreta a cikin masarautar kamar yanda mahaifina duk yace nayi. Ni nasan a korar da mahaifina yasa nai mata bazata iya ta dawo ba, amma kuma sai zuciyata keta faman mini kikawo. Idan uwar masu gida bata mantaba, nine na fadi cewar yarinyar ta rasu a lokacin da nasa a kawota gareni na dubata”.