Daudar Gora Book 2 Page 120
lafiya, sai dai tasha matukar wahala kafin ALLAH ya kawo haihuwar. Ta haifo yarinyarta mace kyakykyawa, sai dai babu ta inda take kama da ita sai tambarin tabon tawadar ALLAH da zuri’ar wannan gida ke da ita, bamu san mahaifinta ba kuma balle musan ko da shi take kamar. Mun amsheta hannu biyu, sai dai zagaye take da addu’ar neman kariyar UBANGIJI da ga sharrin uwa. A randa aka haifi yarinyar a ranar ALLAH ya
kawo wani mai magani.
Malikat Haseenat ta saki murmushi mai ciwo.Tare da fadin “kin san wani abu?” kai Iffah da ke sharar hawaye ta girgiza mata. Malikat Haseenat ta sake sakin murmushi. “Mai maganin nan hatsabilin kansa ne, dan kira daya yayma uwa a randa ya cika kwana uku a masarautar nan a take ta bayyana gabansa
gaban kowa wujiga-wujiga. Ya tabbatar mata shi ba azzalumi bane, da sai ya wahal da rayuwarta ta yanda bata isa sake numfashi a duniya ba, amma ko’a yanzu bazai kyaleta ba sai ya nakasa rayuwarta ta yanda bazata kara tunanin cutar da
Wani ba. Ya sakata ta warware duka wani tsafi data aikata zagaye damu batare da mun sani ba, sannan ya bude dukkan surukanta a gabanmu yay mata korar wulakanci da gargadi
mai tsaurin gaske. Sosai ta dinga kuka da neman gafara da tabbatar masa ta zubda
makaman yakinta bazata sake ba a barta taci gaba da rayuwa damu amma yaki saurarenta.
Majiya karfin hadimai aka saka suka kwasheta zuwa can tsakkiyar dokar jeji mai tsananin rintsi da hadari suka jefar da ita. Wannan shine mafarin barin uwa tare damu, sai dai kuma a
wannan dare ALLAH yay ma jaririyar da Ammarah ta haifa rasuwa, washe gari shima
Shahan-shan Abdul-majeed yabar duniya sakamakon bugawar zuciya da saran macijin da aka rasa tushensa, sai kuma ya kwana da tashin hankalin abubuwan da Uwa ta dinga sakasu sunayi na shirka da yanda bayan ya tsawatar wasu suka zagaye sunayi ciki harda dansa
Jasim. Abdul-majeed ya rasu, uwa ta shude,jinjirar Ammarah ta koma. Haysam ya zama
Shahan-shan. Bayan duk faruwar wadan nan abubuwa da shudewarsu zukata suka hakura
abubuwa suka fara komawa dai-dai. Saurayin nan da Ammarah ta shirya gabatar mana matsayin miji ya dawo da burin aurenta duk da ba’a boye masa komai da take ciki ba. Yace yaji
ya gani, dan ko a baya da ya janye jikinsaJasim
a samesa da gargadin karya sake zuwa an mata aure. Bayan kuma yaji an saketa dan auren kwata-kwata na sati biyu ne ya sake dawowa amma aka hana mishi ganinta ma kwata-kwata.
Ammarah taso bijirewa, dan har lokacin bata dawo dai-dai ba, amma naita lallabata da mata
nasiha ni da yar uwarta hatta hakura aka daura aure. Sai dai sam auren bai wani je ko’inaba ta
fito, sakamakon wata sabuwar kaddarar data afka mata, a duk sanda mijinta zaije gareta sai a
sauya halittar matancinta ta koma ta namiji.Dole babu yanda zaiyi ya rabu da ita ta dawo
gida, daga nan bata sake aure ba, daga nan bamu sake jin labarin uwa ba, daga nan bamu
sake jin labarin bawan ALLAHn nan da ya taimake mu ba akan Uwa ba, daga nan Jasim ya
nuna mana ya tuba, sha’anin mulkin Haysam ya cigaba da tafiya a tsaftace dan a masa
gargadin nisantar duk wan mushiriki akan al’amurin mulkinsa..
Hawaye sosai Iffah takeyi na tausayin Daneen Ammarah, da tausayin su Malikat Haseenat dan labarin nan ya matukar girgizata, al’amari haka
kamar a wasan kwaikwayo, wannan wace irin duniya ce mai cike da son zuciya. Kowa burinsa
ya kasance a sama, mai nasara bisa nasarar dan uwansa, kai kai rayuwar gidan sarauta dabance,
dabance a cikin duk wani rikicin gidaje da zuri’arsu. YaYanda Iffah ke kuka sai Malikat Haseenat ce ta koma lallashinta. Sai da ta
tabbatar ta samu nutsuwa sannan ta mikar da ita. “Hafida-ti, kinga tashi ki tafi dare yayi maybe ma mijinki nacan na jiranki”.