Daudar Gora Book 1 Page 97
Alhamdullah dawowar Kaka da tsayuwar daka akan lafiyar Ummu yasa jikinta ƙarayin sauƙi har tana ɗan yin magana. Wani lokacin ma idan suna ƴar hira takan ɗan saka bakinta musamman idan akan Iffah ne da a mafi yawan lokuta take faɗo musu a zukata. Bawai halin da suka shiga kansu Babiy ya mantar da su ita bane, a koda yaushe tana manne a rayukansu, suna kuma binta da addu’a da cigaba da baza kunnen saƙon mutuwarta kamar ƴaƴansu na baya. Duk da dai ga Iffahn na nan shafe wata na uku kenan a daular ruman ɗin.
Yau ma kamar kullum Ummu da Iyyani na a tsakar gida suna aiki wanda kusan Ummu ce keyinsa duk da bana kirki bane. Kaka ya fita tun ɗazun wajen jana’izar mutuwa da akayi ta wani tsoho. Sauri-sauri Ummu ke ƙarasa aikin saboda rana ta ɗaga gata da zafi sosai kasancewar su yankinsu akwai sahara, danma suna ɗan samun sassauci dalilin ruwa ne zagaye da ƙasar tasu. Sai dai kuma zaman Dahab City (Daular ruman) kamar a tsakkiyar ƙasar ta ruman yasa su sunfi samun zafin yashin fiye da sanyin ruwan daya mamaye wasu jahohin dake a gaɓarsa sosai.
Sallamar da akayi ta saka Ummu amsawa tana mai duban ƙofar gidan, Iyyani ta fito tana faɗin, “Inaga mutanen Abbunku ne da basa ƙarewa. Gashi kuma bai dawo ba har yanzu ko yaya zamuyi kenan?”.
“Nima shi nake tunani Iyyani, kona leƙa na gani tunda ba’a sani ba ko baƙon mai muhimmanci ne?”.
Har Iyyani ta buɗe baki zata bama Ummu amsa sallamar Kaka ta katseta. “To Alhamdullah gamashi nan”. Iyyani ta faɗa tana kallon Ummu. Cikin fara’a kaka ya shigo, hakan yasa bayan sun masa sannu Iyyani ke tambayarsa ko lafiya?. Fuskar tasa da murmushi har sannan ya ce “Bani abun zama kedai yaron nan ne Zakariyya makwafcin su Jumimah”. Ya kare maganar da kallon inda Ummu take.
“Ah Masha ALLAH, ALLAH yasa muji alkairi to”. Iyyani ta faɗa tana ɗakko masa abinda ya buƙata har da ruwan sha ma a kofi…….
Iffah kam dake ta faman tsuke fuska ita a dole taji haushi ta jawo rigar ɗazun ta maida a saman gown ɗinta ta fice. Isowarta falon dai-dai isar da sakon Tajwar Eshaan akan sake dafa masa shayi a bakin hadimin nan ga masu dafa abinci. Kai tsaye mamaki ya bayyana ƙarara a kan fuskarta. Amma sai ta dake babu alamarsa a zahiri taima hadiman wani kallo ta ɗauke kai.
Ba ƙaramin razana da ganinta a cikin kicin masu girkin sukai ba. Dan hakan zai iya zamar musu rasa aikinsu. Sai dai yanda tai kicin-kicin da fuska ya sasu kama kansu, kwarjininta da gizagonta na kere yawan shekarunta. Jikinsu har rawa yake lokacin data buƙaci ganin kayan shayin da Tajwar ɗin ke amfani da su. Daki-daki take binsu da kallo cike da nazari, sai da ta gama tsaf kafin ta juya garesu fuska a tsume. “Idan ina buƙatar wasu bayan waɗan nan a yanzun fa?”.
Cikin mamaki da tsoro suka sanar mata za’a kawo da gaggawa.
“Ina buƙatar zama da mai kawowar”.
Ta faɗa a gadarance da juyawa ta fara haɗa kalar shayi da salon dabararta batare da tayi amfani da wanda ake dafa masan ba. Wannan duk cikin shirinta ne na son ƙuntata ma zuciyar Tajwar Eshaan a cewarta. Cikin lokaci ƙalilan ta gama kasancewar ba wani mai yawa bane, ta juyesa a haɗaɗɗen butar shayi tare da haɗa komai na buƙata tai ƙoƙarin ɗauka. Da sauri hadima ɗaya ta miƙe ta amsheta. Bata musaba wajen bata dan dama ba sanin inda zata samesan tai ba.
Hadimar tai tsaye a dai-dai ƙofar ƙaramin falon alamar iyakar ta kenan. Iffah ta fahimci haka, sai kawai ta amsa batare da tace komai ba. Ba tsoro ko shakkar haɗuwa da shi take ba, abinda zai farunne idan ta shiga kawai take tunani. Tsahon minti biyu kafin tai ƙundunbalar shiga dan a ganinta wannan wata dama ce ta biyu a gareta, cikin takunta na nutsuwa da dakewarta ta tura kai bayan ƙofar gilashin ta zuge da kanta batare data tabata ba……