Daudar Gora Book 1 Page 95
Suna yin ɗan nesa kaɗan da masu tsaron ƙofar Iffah ta zare hannunta da sauri tana ɓata fuska. Bai ko juyo ya kalleta ba balle ya nuna alamar yasan mitayi yay gaba abinsa cikin takunsa na nutsuwa da tsantsar ƙasaita tamkar baya son taka kafafun nasa. Da ƴar hararar ƙasan ido ta bisa tana ƙunƙuni a zuciyarta. (A haka dai kamar na wani limamin masallacin Saudiyya, sai dai zuciyar ko kafiran farkon ƙarni haka suka gansa suka barsa. Wanda duk zai iya salwantar da rai yay barci lafiya babu ko ɗar ai ya dace ka kirasa da duk sunan daya zo maka a rai dan ya cancanci haka). “Ni zanyi maganinka da izinin ALLAH”. Ta faɗa a zahiri fuskarta na nuna gaskiyar ɗacin da zuciyarta ke mata.
Shiru yay yana kallon inda ya saba iske shayinsa, wayam babu komai, ya kai zaune a kujerar cikin alamun gajiyawa, a gefe kuma tsaurin idon yarinyar da ƙarfin halinta na masa kaikawo. Shan wannan shayin ya zame masa jiki da in bai sha ɗin ba sam bama yajin daɗi, har ma yakan tsinta kansa a wani
yanayi da shi kaɗai ya barma kansa matsayin sirri duk da abun na matuƙar damunsa. Har yayi yunƙurin dauriyar sharewa tunda ya ɗan sha wani amma jin abinda yake gudun na taso masa ya sashi furzar da zazzafar iska, babu shiri ya danna alerm ɗin dake isar da saƙon kira ga amintattun hadimansa. Cikin mintunan da basu wuce uku ba ko sai ga ɗaya daga cikin su ya iso. A gabansa ya zube cikin tsumar jiki yana mai ambaton…
“ALLAH ya ƙara ma Shugabana tsahon rai da ingantacciyar lafiya, umarninka shine abin jirana”.
A zuciya ya amsa da Amin, a zahiri kam babu alamar zai tanka kamarma bashi ya bukaci ganin hadimin ba. Tsahon mintuna uku ƙasaita da izza irinta saraki na dawainiya da shi kafin ya motsa lips ɗinsa a hankali cikin bada umarni.
“Miya hana a kawo shayi?”.
Hadimin ya ƙara ƙasa da kai jikinsa na ɗan rawa. “Umarni ne daga Zawjata-almilk”.
(Umarni?!) Ya maimaita kalmar a zuciyarsa cikin ƙara ƙanƙance idanunsa. (Shi kam ya zaiyi da yarinyar nan ne? Mai kama da alja…..) Ya sake ayyanawa a zuciyarsa batare da ya ƙarasa ba. Sai kuma ya kalla hadimin ya ɗauke kai. “Ina buƙatar waninsa”.
Da sauri hadimin ya ƙara gurfana yana amsa masa ransa fal mamaki da al’ajabin wannan sabon al’amari.
Fuskarsa gwanace wajen shanye sirrin dake bayyane, amma yanda ya yatsinata da lumshe idanu a yanzu zai tabbatar maka akwai magana tattare da shi.
Duk yanda taso nuna halin ko’in kula kan abinda ya farun yanzu hakan ya gagara. Dan mayataccen ƙamshin turarensa daya bambanta da wanda ta saka duk da suma nasa ɗinne ya mugun addabarta. Takai hanunta kan hanci yafi sau biyar, sai ta shinshina sai kuma ta janye tana laɓe baki. Hakan kuma bai hana anjima ta sake maidawar ta shinshina. Daga ƙarshe da taga abin na neman zama mata ɗan kaɗafi sai ta faɗa toilet ta wanke hanun da sabulu, amma dan mayata yaƙi ya daina sai da ta ɗauka ɗaya a cikin turarrukan datai amfani da su na ɗakin tasa a hannun sannan ta daina ji.
Littafinta ta ɗauka domin cigaba da nazari, sai kuma ta tsaya cak, wani tunani ne yazo mata a zuciya, dan haka ta miƙe zaraf tana ɗaukar wayarta data gani tare da littafin alamar duk ma wanda ya kawota tare da su ya kawotan. Kamar yanda ta saba idan zasuyi magana tai dawnlording sabon WhatsApp app, sai da ta daidaita komai sannan ta lalubosa. Baya online gashi kuma tana buƙatar yau suyi magana ne bawai saƙo take son ajiye masa ba. Sai hakan ya sata jin babu daɗi har walwalarta ta ɓace. “Kona masa flashing?”. Ta faɗa cikin sigar tambayar kanta. Kan ta daga alamar gamsuwa, ta fito a watsap ɗin. A karo na farko tai dailing number ɗin cikin shakku. Harta katse ba’a ɗaga ba, damuwarta ta kara bayyana. Harta sake komawa watsap ɗin ta fito ta sake danna kiran. A hankali ta sauke ajiyar zuciya har ana iya jinta daga can. Tai sallama cikin yar muryarta dake nuna zumuɗin jin an ɗaga, sai dai ba’a amsa mata ba gashi kuma tanajin alamar ana saurarenta.