Daudar Gora Book 1 Page 6
Daƙuwa tamata cikin gatsina fuska. “Ungo naki nan Fareedah, yo bandama lalacewa mizanyi da wannan faratun mai kama da jar tsada tuzurin banza”.
Hanash ya tsuke fuska yana kallon Iyyani. Murmushi Iffah tayi tun kafin ya faɗi abinda ke bakinsa. Dan dama inhar suka haɗu da Iyyani sai ta hasalashi take jin daɗi shi da Arfa akan ƙinyin aure, duk da bawani shekarune da shi ba, dan ashirin da shida ne kawai, Arfa nada ashirin da uku, Fariha nada ashirin da ɗaya. Iffah nada goma sha takwas….
Iffah ta dire masa abinci da ruwa ta sake kaiwa zaune kusa da shi sannan ta dubesa. “Akhi yasu Babiy suke?”.
Ya nisa a hankali bayan ya dire moɗar ruwan daya sha. “Duka lafiya suke. Suna gaisheki ke da su kaka. Duk da suma dai nan da kwana kusa zamu ma dawo nan ɗin muma. Yanzu haka nazo duba can tsohon gidanmu ne dan asan gyaran da za’ai masa”.
Sosai ta kafesa da ido ita da Iyyani. Kafin cikin ƙarfin hali Iffah tai magana. “Amma Yaya su Babiy basa ganin rayuwa zata mana wahala anan sakamakon bamu sababa sam. Sannan ayyukansu dake acan miye makomarsu? Da karatunmu muma?. Abinda ya faru ya riga ya faru, tunda hannayenmu bazasu iya maidosu ba, mi zaisa zukatanmu bazasu cigaba da haƙuri ba. Barowarmu cikin Daular ruman tamkar munji tsorone, ko sake sakin rayuwarmu a hanun waɗanda kansu kawai suka sani…….”
“Tsoro halak ne Iffah. Bama muba mafi yawan masu yara mata sunata barin daular ruman a yanzu domin tseratar da ƴaƴansu daga auren jeka nayika. Karatun ƴammata yana neman tsayawa cak, kowace na tsoron fitowa ta zama nama a hanun hadiman daular ruman. a yanda lissafin yake a yanzu an rasa mata goma sha huɗu fa, a tunaninki kafin ƙarewar wannan shekarar ba’a rasa fin hakaba duk da bawai ya cigaba da auren bane.”
Wasu hawayene masu ɗaci da ƙuna suka silalo ma Iffah, tai saurin saka gefen mayafinta ta share tana murmushin takaici. “Niko a ganina gudu bashine mafita ba, muryoyinmu ya kama mu ɗaga wa duniya kowa yasan halin da muke ciki, idan har a ƙasar Ruman babu wani sama da nasa mulkin ai a sauran ƙasashen duniya akwai wanda suka fisa…”
“Humm Iffah ke yarinya ce har yanzu.”
“Sosai kuwa Hanash. Shiyyasa bata gane komai sai abinda yanzu take zuwa da shi”.
“Humm Iyyani kenan”.
Iffah ta faɗa a yanayin jin raɗaɗi a maƙoshinta. Su duka kallonta sukai, sai dai ta ɗauke kanta gefe tamkar bata gansu ba. Daga haka babu wanda ya sake cewa komai har tsahon wani lokaci. Iyyani ce ta canja hirar da wani abu daban har Hanash ya kammala.
Tare da shi suka fita wajen duba tsohon gidan da kakaninsu da suka haifi Babiy ne suka rayu a ciki, dan sudai tunda suka taso a cikin birinin daular ruman suka san kansu duk da a ɗan gefen gari suke acan ɗin ma. Sai dai su shigo cikin ƙauyen Jumna a matsayin duba kakannin nasu. zuwa yanzu su duk sun rasu, shiyyasa gidan ya kasance babu kowa. Duk ma ya rusa ya fita hayyacinsa dan ginine na jar laka tamkar yanda duka gidajen ƙauyen suke. Sun ɗan jima acan suka dawo, sun iske kaka ya dawo shima daga fitar da yay tun ta safe gona ɗebo sassaƙe-sassaƙen magunguna. Ƙara zaman tattaunawa sukayi iya su uku, ita dai Iffah bata cewa komai. Daga ƙarshe ma tashi tai ta shige ɗakin kwananta. Bata sake fitowa ba sai da kaka ya neme ta. Sassaƙe-Sassaƙen magungunan daya ɗibo ɗazun ne a gabansa, kowanne ya ɗauresa daban-daban. Ya turamata babban robar da suke ciki… “Zaki fara amfani da su Iffah, bana son kiyi wasa dan ALLAH. Waɗannan kuma hayaƙine, a kowacce duhun magriba ki tabbatar kinyi turarensu, wannan kuma a ruwan wanka ne, da kin idar da sallar asuba ki zubasu cikin ruwa kaɗan ki cire kayanki ki tabbatar duk jikinki ya samu”.
“Tofa kaka wannan ɗin kuma duk na miye?”. Iffah ta tambaya cikin nuna mamaki.
Idanu ya tsiramata na kusan mintuna uku tamkar mai nazari, sai kuma ya ɗauke kansa da wani yanayi mai wahalar fassara. “Faruwar ƙaddararmu bashi ke nuna baza’a sake jarabtarmu ba. Idan jiya ta shuɗe da ɗaci zata iya yuwuwa yau ɗinmu da dariya zata kasance, sai dai sanin mike a gobenmu al’amarine mai girman gaske, damin gaibunmu ce ita ALLAH ne kaɗai masanin mi zaizo.”
Kallon juna sukai ita da Hanash, Iffah ta ɗan ɗage kafaɗa cikin yanayin ban fahinta ba, shima sai ya kaɗamata idanu alamar shima hakan take. Atare suka maida dubansu ga kaka. Amma sai ya kauda kansa alamar baya buƙatar kowacce irin tambaya daga garesu. Iffah ta jinjina kai kawai alamar ko’oho. Sai kuma ta miƙe tana mai faɗin, “Ni dama fa na yanke shawarar zanbi Akhi mu koma. Tunda dai naji sauƙi gara naje na koma makaranta anata wuceni a darasi”.
Ba karamin waro idanu Hanash yay ba, zaiyi magana kaka ya dakatar da shi ta hanyar yin murmushi da kaɗa kansa. “Ita rayuwa rubutacciya ce tunkan halitta, an rubutatane da alƙalamin da ba’a goge rubutunsa, babu wani hannu daya isa gogeta koda da ƙarfin iko. Dole ne sai anyi hakan, ko muna so ko bama so mashin nan sai ya isa inda aka aikashi. Domin ita *KIBIYAR AJALI! SULKE BAYA TARETA SAI TA GITTA*”.
A rikice Hanash ya tari numfashinsa. “Kaka bana gane dunƙulallun zantukan nan naka, ka fito fili dan ALLAH ka sanar mana mi kake son faɗa…”
“Hanash! Lokacin faɗar baiyiba ai, nima kurman baƙin kawai na gani, fassarar sai UBANGIJI”.
Sosai Hanash ya sake tsare fuskar kaka da idanu, kamar yanda itama Iffah tai tsai tana kallon nasa. Su dukansu sun jima da sanin kaka mutum ne hatsabibi, dan kuwa mahaifinsa gawurtaccen masanine da azamaninsa akan kallesa tamkar matsafi ko wani mai gani har hanji, sai dai kasancewar bai ajiye buzu ya zauna akan iya wannan al’amarin ba yasa ake shakkar faɗa, yana bada taimako na magani akan abubuwa daban-daban musamman harkar aljanu komai ƙarfinsu da shaiɗancinsu. Sannan yana sana’arsa ta saƙa kayan kwalliyar doki. Kaka ya gaji abubuwa da dama a garesa, sai dai shi ya watsar da harkar bada maganin dan shima dai a karan kansa yana ta’allaƙa sanin mahaifin nasa da bokancin, duk da dai bai fito fili ya bayyana hakan ba kuwa, amma rashin maida hankali akan abinda ya shafi hakan zaisa ka zargi ko haka ɗinne. Akwai kayan aiki na mahaifinsa da yawa a killace a wani waje da shi kaɗai ya sani, kuma tun bayan mutuwarsa shi ya tattare su ya killace su…………✍