Daudar Gora Book 1 Page 49
“Ya ALLAH wannan wace irin magana ce haka? Miyasa zatai irin wannan tunanin akan ɗanta. Bana jin Eshaan zai taɓa aikata makamancin hakan. Kawai dai akwai abinda yake ba daidai ba”.
“Sosai kuwa. Amma insha ALLAHU ta sanadin yarinyar nan kowa sai yaci ƙaniyarsa. Dan haka kawai nakeji a jikina ita ɗin haske ce a wannan daula. Tunda har gashi ta karya tarihin farko na azzalumai”.
“Haka muke fata, dan muma an tattauna akan hakan sosai jiya da yau a fada. Kusanma issue ɗin da ake kai kenan kawai yanzu a majalissa. Sai na kisan hadiman can”.
“To ALLAH ya dafa mana mu da ku, ya kaimu ranar da zamu ga iyakar wannan al’amari”.
“Amin my meera”.
Yay maganar da wani salon kashe ido mai cike da soyayya da kaunarta. Murmushi tayi itama tana miƙewa, “Bara na kimtsa kafin ka kammala ko”.
Kai ya gyaɗa mata idanunsa narke a kanta.. Tana juya baya ya bita da wani irin matsiyacin kallo mai ma’anoni da yawan gaske yana tsuke fuska da jan tsaki……
Kamar yanda Malikat Bushirat suka tattauna da Jasrah batai ƙasa a gwiwa ba tana idar da sallar asuba ta fita daga sashenta cikin badda kama zuwa sashen Malikat Haseena. Kasancewar ta sanarma Daneen Ammarah tare suka nufi ɗakin Malikat Haseena ɗin. Itama tasan da zuwan Malikat Bushirat ɗin. Dan haka basu ɓata lokaci ba suka fara tattaunawa dan ta samu ta koma kafin gari yay haske. Da farko dai malikat Haseena ta kakkawo musu dokokin masarautar masu tsari dangane da haɗa Shahan-shan da Zawjata-almilk kai tsaye ba’a turakarsa ba. Sai dai bayanin da sukai mata da nusar da ita abinda suke son tabbatarwa yasa itama ta amince. Sai dai da sharaɗin komi ya biyo bayan hakan laifinsu zata gani. Cike da yaƙinin fatan karma wani abu ya faru suka amince. Dan haka tai musu sallama ta koma. Daneen Ammarah da tunaninta nada banbanci da na Malikat Bushirat akan wannan haɗuwa tai murmushi a ranta tana mai addu’ar samun nasara. Domin wannan yaƙi kamar natane ita kaɗai sakamakon itace kawai tasan ɓoyayyen sirrin daba kowa ya sani ba sai UBANGIJIN talikai. Fatanta shine komai yazam yana gangarowane ga faɗan karshe akan maƙiya koda ita zata rasa rayuwartane a yayin gumurzun…
Yau ɗin ce dai ta kasance rana da yake zuwa gaishe da kakarsa Malikat Haseenah. Irin wannan rana kuma tana zuwane sau ɗaya a kowanne wata. Sai dai idan ita ke buƙatar ganinsa ta samesa a sashensa. Amma a kowane wata yanada ranaku biyu na ziyartar kakar tasa da mahaifiyarsa. Malikat Haseena yake fara dubawa a farkon wata, Malikat Bushirat a tsakkiyar wata. Duk da fitace ta dare da ba lallai kowa ya gansa ba ya kasance cikin shiri mai ɓoye ainahinsa, ga wani ƙamshi na isassun da suka isa na tashi tattare da shi. Takunsa da ƙarfin izzarsa ya isa tabbatar maka eh lallai Shahan-shan ne da kansa. Ƙasaita jinin jikinsa ce, kamewa da isa adonsa ce, kwarjini da nutsuwa halittarsa ce….
Duk da farkon dare ne dan kwata-kwata ƙarfe takwas ne, amma masarautar tayi tsit kowa ya nutsu a inda ya dace saboda sanin wannan rana ce da Shahan-shan ke fitowa zuwa sashen Malikat Bushirat. Babu wani Hadimi dake kai kawo sai Ghazi da masu tsaro da suka tsare ko’ina fiye da kullum. Hakama sauran jama’a in ba babba mai faɗa aji ba babu wanda keda hurumin wani kaikawo a irin wannan daren dake zuwa a wannan rana saboda fitowar Shahan-shan……..