Daudar Gora Book 1 Page 117
Da taimakon masu tsaronsa bisa umarnin ogansu da tun a ganin farko da yay masa bai sake ganinsa ba sai ta waya tun a yammacin ranar suka fara tattara abubuwan da zai basu kariya wajen fita da su Babiy duk da basu zo hanunsu ba har yanzu. Sai dai a daren ranar su Sayeed Harun Al-rashid sukai alkawarin danƙasu hannun Barrister, duk da ya nuna musu shifa yana jin tsoro su bari komai ya kammala sannan suka nuna masa suna tare da shi da kuma tsaro na musamman duk da kuwa ƙarya ne a baɗini.
Zancen kam nasu ya tabbata, dan a daren ranar ƙarfe kusan tara na dare aka damƙa Babiy da Hanash a hannun Barrister Abdallah Aas matsayin Barrister Akeem da zukatansu su suka ɗauka. Daga gani kasan sun jigata matuƙa, sun rame sosai sunyi duhu. Ga rashin ƙarfin jiki da zaman waje ɗaya harma da ƙarancin abinci dana iska mai ƙyau. Hankalin Barrister ya tashi matuƙa, ya dinga share hawayen tausayinsu. Ya sake tabbatar da mutanen nan da suka kamashi mutanen kirki ne a yau, dan ana iso da su Babiy hanunsu sai ga likitoci, dan-da-nan suka duƙufa kansu da kulawa kai kace dama a shirye suke da hakan….
Duk da ƙarancin shekarunta ALLAH ya bata basira irinta masu hangen nesa. Tun bayan gama wayarta da Miran Jasim zuciyarta bata aminta da yarda su gana fuska da fuska ba. Dan haka ana idar da sallar magrib ta tura masa saƙo kamar haka duk da ita ba sallar zatai ba tana fashi.
_Na amince mu tattauna, sai dai bata haɗuwa ba, muyi magana ta video call._
Miran Jasim ya karanta saƙon yafi sau ashirin, takaici kam ba’a magana ga ɗunbin mamakin basirar ƴar ficikar yarinyar. A take ransa duk ya jagule, ga boka Barbushi ya tabbatar masa haɗuwa da yarinyar fuska da fuska yafi fa’ida. Dan kwarjininsa da suddabaran da ya basu zai sakamata tsoronsa mai tsanani ya dinga yanda yaso da ita har zuwa sanda itama zasu ɓaddata bayan ta cika musu aikinsu. Gashi yanzu guri ya ƙure, bazai yiwu masa ba zuwa ga Barbushi ɗin dan zai iya rasa wannan damar da bokan nasu ya tabbatar musu itace ranarsu mafi Sa’a akan yarinyar kasancewar tana fashin salla, tana kuma cikin ruɗanin da ba komai yake iya banbancewa yanda ya kamata ba zasu iya sarrafata a duk yanda sukaso musamman akan Shahan-shan. Duk da sallar isha’i data gama gabatowa haka ya miƙe ya fice a masallacin bayan yayma Miran Arshaan alama da ido. Bai jima da fita ba kuwa yabi bayansa….
Miran Jasim ya sauke idonsa akan Miran Arshaan mai maganar yana mai jan tsaki. “Wane kwanciyar hankaline da ni inba gani nai komai ya daidaita ba Arshaan. Yanzu ma ƴar iskar yarinyar nan ce wai fa ta turamin text message bata yarda mu haɗu fuska da fuska ba sai dai video call”.
“What! Waini wace irin hatsabibiyar yarinya ce wannan? Nama fahimci kallon sa’aninta take mana”.
“Ka barta karka damu, zata yabama aya zaƙinta ta dai gama mana aikinmu. Anan zata gane ko wanda ya ajiyeta a gidan bai isa ba balle ita karamar halitta. Ni yanzu damuwata ma shine Barbushi ya tabbar mana da wannan ranar ta sa’a, haɗuwarmu kuma fuska da fuska wani babban cigabane garemu.”
“Komai ya kwaɓe kam, sai dai ni a wannan gaɓar ina masa kallon mai sauƙi. Kaga dai a yanzu bamu da isashen lokacin komawa wajen Barbushi, na biyu barin wannan damar ta wuce a garemu kuskure ne. Dan haka kawai mubita a yanda take so ɗin, da sassafe mu nufi Barbushi”.
Ajiyar zuciya mai nauyi Miran Jasim ya sauke domin gamsuwa da zancen Miran Arshaan ɗin, daga haka basu koma masallacin ba sukai zaman kulla yanda zasu tunkari Iffah bayan sun tura mata saƙon amincewa ayi video call ɗin.