Hausa Novels and StoriesLatest Updates

Sahun Keke Hausa Novel Complete

Sponsored links

Bismillahirrahmanirrahim

 

 

 

 

 

Garin Kano

 

Misalin ƙarfe 03:00am…. Dare mahutar bawa,, a duk lokacin da dare ya tsala sahu kan ɗauke kowane ɗan Adam ya killace kansa a makwancinsa domin samawa ruhinsa salama.

a wannan dare yayin da Asbahi ke shirin ƙaratowa daidai lokacin hadari ya fara gangami, cikin lokaci ƙanƙani ya gama haɗowa ya fara sakin iska me ƙarfi gami da walƙiya me tsananin haske ya na wani irin rugugi kamar zai ci babu.

 

Ya ɗan ɗauki lokaci cikin wannan yanayin kafin ya saki ruwa me ƙarfin gaske.

Sai da aka kira Sallar Asbahi sannan ruwan ya tsagaita ya koma yaf-yaf a hankali a hankali, ba shi ya tsaya cak ba sai da gari ya fara haske.

 

 

 

mamakon ruwan da aka sha ya haddasa lullumi gami da wani irin sanyi me matuƙar daɗi.

 

 

 

kasancewar safiyar Lahadi ce ya sa titina har ma da cikin unguwanni babu yalwar jama’a kowa ya nabba’a a gida, tin daga kan ƴan makaranta har ƴan kasuwa, tsirarun mutane ne kurum ke yawo sai ababen hawa na haya su ma ba su gama fitowa ba, domin kuwa yadda ƙasa ta sha ruwa ta jiƙu ga sanyi na ratsa jikkuna ba kowa ne zai so fitowa a irin wannan lokacin ba.

Hajiya Laure ce zaune kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun Falon, ta harɗe ƙafa ta na danne-dannen waya fuskarta ba alamar walwala, ta haɗe cikin leshi ɗinkin Buba ta doka ɗaurin ture ka ga tsiya, adon nata ya ƙara fito da asalin suffarta ta Hajiyoyi, Jiran shigowar Alhaji Salisu kawai ta ke yi don ta sauke masa buhun masifar da ta kwana ta na ƙissimawa akansa.

 

 

 

Yazeed ne ya shigo falon ya na tafe ya na jan ƙafa zagaraf-zagaraf bai bi ta kanta ba ya saita hanyar bedroom ɗinsa, cike da takaici ta ce “Ai ko ba za ka gaishe ni ba ya kamata ka faɗa min inda ka je.” fasa wucewa bedroom ɗin nasa ya yi ya dawo kusa da ita ya zauna idanunsa ƙasa-ƙasa ya ce “Why are u doing this to me?? you’re my mother fa kin fi kowa sanin ba yaro bane ni Mummy, maganar gaskiya kin fiye kishi da ni” tsaki ta doka kafin ta ce “Ubanka ne ya lalata ka ba wani ba, na san ba zai wuce daga biye-biyen ƴan mata ka ke ba, inda zan yi kishi da kai kuma ai ba zan ma haifeka ba yaro, kawai don ba ka son gaskiya ne.”

Taɓe baki ya ɗan yi cikin ko in kula ya ce “Ina Daddy?” a masife Hajiya Laure ta ce “Ka ban ajiyarsa ne?? tin jiya ya yi min alƙawarin zai dawo ya same ni amma ya ƙi dawowa.” “Wani gurin ya je??” ”To ai in wani gurin ya je ma da ƙauna, ya na sashinsa, wai wani baƙo zai yi za su tattauna shine har da ce min kar in sake in zo sashinsa har sai ya dawo ya same ni, to ka ga da bai iya cika alƙawari ba ya ƙi dawowa, sai ka tashi ka je gurin nasa tinda dama ai shi kaɗai ya haifeka ni ƴar karere ce, idan ka je kace masa ya fito ina jiransa.” Dariya Yazeed ya yi gami da cewa “Gaskiya kina da yawan faɗa Mum, ki dinga haƙuri mana Daddy fa ya na da aiyuka sosai ki dinga yi masa uzuri, kuma ba na so in ji ki na cewa ba na martaba ki ɗinnan Please Mum, martaba ki ya zama dole bayan ke ba ni da wata.” taɓe baki ta yi ta juya masa ƙeya alamar ba ta gamsu ba

Tashi ya yi ya wuce sashin Daddy ya na jiyo Hajiya Laure na mita shi kam sai dariya yake don abin nata dariya yake ba shi.

 

 

 

Ɗan madai-daicin Parlor ne wanda ya ji kayan Alatu na more rayuwa, an zuba kuɗi wajen tsara shi da ƙawata shi komai ya ji banda tsiya inji maroƙa.

 

 

 

Banda sanyin AC gami da ƙamshi ba abinda yake tashi.

 

a tunanin Yazeed ya na shiga zai tarar da Daddynsa a Falon ya na karatun Jarida kamar yadda ya saba don haka ya fara cewa “Dad!!! ka na ina? ka shirya faɗa da Mum don kuwa ta yi fus……..” maganar tasa ce ta maƙale a maƙoshinsa, cikin zazzaro ido ya ke kallon jini da ke kwance malala har ya gangaro ƙarƙashin Kujera ya fito kasancewar saitin kujerun a tsakiya suke.

cikin tsananin firgici ya zagaya don ganewa idonsa abinda ke zubda irin wannan jinin haka.

 

 

 

Ihu ya kurma gami da yin tsalle ya yi baya idanunsa kamar za su faɗo ƙasa sabida zaro su da yayi, dandanan jikinsa ya ɗauki wata irin tsuma, zuffa ya shiga karyo masa duk da irin sanyin AC da sanyin gari da su ke kaɗawa.

 

 

 

Baya-baya ya fara yi ya na cewa “No!! wallahi ba dai Daddyna ba, lallai yau na tabbata Jaki, naje na sha giya ta zo tana nuna min Daddy cikin jini haka? Impossible! dole ma in dena shaye-shaye!!” maganar yake cikin fitar haiyaci don kuwa tashin da hankalinsa ya yi ya wuce mizani.

Da gudu ya juya ya koma Parlo ya na ƙwallawa Mummy kira, gabanta ne ya yanke ya faɗi Rimmmm!!!!!!! ta yi saurin tashi ta na cewa “Me ya faru??” Yazeed ya na haki ya ce “Daddyyy!!! zo mu je ki gani, na fara haukacewa!!.” ya ƙarasa maganar ya na jan hannunta, cikin sauri gami da sassarfa ta bi bayansa su ka koma Falon Alhaji Salisu.

 

 

 

Sai da ya danganata da gawar Alhaji Salisu sannan ya saki hannun nata ya koma baya ya riƙe ƙugu ya na jiran ta ce masa ai giya ta sa ya fara gane-gane.

ya na kwance cikin jini ko ina a jikinsa raunin wuƙa ne faca-faca anyi masa wani mugun kisan gilla wanda ko Dabba mutum ya ga anyiwa dole hankalinsa ya tashi bare Mutum ɗan uwansa.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button