Daudar Gora Book 1 Page 100
Shiko da komai ya faru dominsa babu alamar hakan ya damesa. Dan ko kallon inda take baiba tunda ya fito. Babu ma alamar yasan da ita a ɗakin tattare da shi. Amma abin mamaki sai gashi ya zauna a kujerar da table ɗin ke tare da ita, wanda kuma anan ne Iffah ta ajiye shayin nasa. banbancin ɗanɗano da wanda ya saba sha kamar ɗazun ya sakashi yin tsamm da tsurama shiyin ido tamkar a cikinsa yake neman amsar sanin yaya hakan wai ke faruwa?. A zahiri ko babu wani abu a fuskarsa sai ma glowing da take irin na mai lafiyayyar fatar data jiƙu da hutu da jin daɗi. Yatsunsa biyu ya ɗan kai saman goshinsa ya murza kusan tsahon sakanni arba’in, kafin kuma ya janye yana mai ajiye kofin ya miƙe batare da ya sha ba. Ta can wajen gilashin da kayan barcinsa suke ya taka, hannunsa ya daura akan gilashin sai gashi gaba ɗayan drawer ɗin ta zuge a hankali ƙofa ta bayyana. Takawa yay ya shige, ta maida kanta ta zuge……
Da gaske dai ɓatan Sayeed Khairul-Bashar ya tabbata a cikin masarauta. Dan Iya duk wani bincike babu wata alama ta yana a cikin gidan. Iyalansa sai kuka suke duk sun hargitsa masarautar. (Kamar yanda kukaji a baya Sayeed Khairul-Bashar Aami ne a wajen su Tajwar Haysam, Miran Arshaan, Miran Jasim da dai sauransu. Kaka kenan a wajen Tajwar Eshaan shi kuma. Sayeed Khairul-Bashar da Tajwar Abdul-majeed kakan Tajwar Eshaan ƴan uba ne suma. Kamar yanda a yanzu Tajwar Eshaan ke shan gwagwarmaya a hannun su Miran Jasim haka mahaifinsa Tajwar Haysam yasha wannan wahalar a hannun Aamin nasu irin su Sayeed Khairul-Bashar. Sai dai ko kusa basu ci galaba ba dan Tajwar Haysam ma dai kaifi ɗaya ne kuma tsayayyen mutum kamar yanda kuke ganin Tajwar Eshaan a yanzun. Wannan rashin nasarar tasu akan Tajwar Abdul-majeed da ɗansa Tajwar Haysam ce ta dawo kan Tajwar Eshaan a yanzu, sai dai kuma da alama bazai taɓa ya raga musu ba. A gefe kuma su Miran Jasim na amfani da wannan damar wajen dama garinsu akan Tajwar Eshaan… ALLAH ya sa kun gane ni dai ba ruwana🥱🚶)
Duk bidirin da ake Tajwar Eshaan bai sani ba, dan yau ya fita fada ne a makare. Koda ya isa fada kuma aka kawo zancen da farko bai ɗauka abin na gaske bane, dan haka cikin halin ko’in kula irin nasa ya nuna musu maybe yayi fitar da kowa baya buƙatar ya sani ne. A bashi lokaci a gani. A cikin wasu ƴan majalissar tasa wasu sun gamsu da wannan jawabi, harma aka fiddashi waje dan hankulan mutane su kwanta. Sai dai a wani gefen kuma jawabin Shahan-shan ɗin tamkar samun wani makamine na dukansa da shi ga maƙiyansa na ɓoye dana zahiri, sai dai sun danne a yanzu basuce komai ba suna jiran lokaci……..
Ruɗanin da Barrister yake ciki ya wuce duk yanda mai hasashe zaiyi tunani. Gashi tunda suka maidashi gidan suka sake kullesa a ɗakin babu wanda ya waiwayesa har duhun magriba ya kawo, bayan idar da sallar isha’i ne aka kawo masa abinci. Dan haka ya fuskanci mai kawo abincin da alamar yar yanzu zuciyarsa ta kasa tsayawa waje ɗaya.
“Dan ALLAH ina son magana da ogan ku Akhi. Ina da abubuwan tattaunawa da shi masu yawan gaske da muhimmanci”.
Kamar bazai tanka masa ba sai kuma ya amsa shi da faɗin, “Boss baya nan, ganinsa kuma abune bamai sauƙi ba dan bana jin ma yana ƙasar. Karka damu idan yana buƙatar magana da kai zai zo da kansa basai ka nema hakan ba”. Daga haka yay ficewarsa. Jiki a sanyaye Barrister ya bisa da kallo harya maida ƙofar zai rufe yay saurin faɗin, “Na roƙeka kota wayane ka haɗamu, da gaske maganar da zanyi da shi nada matuƙar muhimmanci, da kuma buƙatar yinta da gaggawa”.
Jimm saurayin yay yana kallon Barrister ɗin daga inda yake, sai kuma ya ɗan rausayar da kansa da faɗin, “Okay duk yanda mukai zan dawo”.