Idon Naira 15
Tunda Alh Asad ya dauki damarar inganta rayuwarta abin yaso kawo matsala tsakaninsa da Maryamah Amma bai Wani samuba sbd idan sun inganta rayuwar Zainab to rayuwar Dan su suka inganta Dan kamar itace malamar tarbiyarsa
Malam Sanda shine makusancin malaminsa dayake koyar dashi karatun addini sosai duk da bawasu shekaru ne dashiba Dan bazai wuce shekarunsaba Amma suna tsananin girmamasa kasancewar yanada ilimin addini sosai kusan duk masu kudin anguwar manyan mutane dake shaawar karatun addini Bayan magriba zuwa ishai shine yake zaunawa dasu anan harabar gidan alh Asad suna karantar manyan litattafan addini.
Kokarin janta ajikinsu Alh Asad yafara sbd tasake dasu kaman Yan uwanta Kuma kamar iyayenta musamman Haj maryamah din wadda ita kadaice tata hakama matuqar Basu fara sabuwa da junaba har kauna tashigo ciki tabbas duk ranarda Zainab din tayi aure zumunci da alaqar yankewa zaiyi kwata kwata har gwara yanzu da akwai Aqeel a tsakiya Wanda ya tabbatarda ko sunyi rabuwar aqalar bazata taba rabuwa Dan kuwa Shi agurinsa su biyun iyayensa Babu abinda zaisa ya zaba daya yabar daya idan ya girma.
Duk yanda Alh Asad din yaso ganin sun fara rabar Hadi da Yar sabo da juna hakan bai samuba saima shi data Dan fara sabuwa dashi Tana qara ganin tsananin girmansa Tunda shike janta ajiki da kulawa da kokarin kyautatawa.
Maryamah na lure Amma tayi kaman Bata San meyake faruwaba sbd tasan abinda Alh Asad din yeke tunani bamai yiyuwa bane lokaci daya
Idanma zai yiyu din kenan Dan kuwa sun riga sunyiwa juna wata nisa da tazara Mai girma da bazasu taba sabawa ko shakuwa da kaunar junaba lokaci
Dan haka ta tattara ta sake maida hankali kan aikinta tareda kokarin mantar da shi zancen kwata kwata ta hayar kulawa da tarairayarsa,…ta manta da tarairayar ‘dan data Haifa Wanda takasa tsayawa ta tarairaya.
Aqeel yayi girma da wayan dazai fara zuwa makaranta Dan haka dana addini suka fara sai Tunda yaqara wayo dashi Dadynsa yake fitowa karatun Daren kafin daga baya Malam Sanda din da Kansa yake koyarda Zainab da Aqeel din.
Tafiyar kwanaki biyar ce ta kamasa zuwa daya daga cikin manyan kamfunins na shinkafa dake Lagos,
Ranar dazai tafi har Rana Yana tareda Dansa Aqeel a palonsa Yana jansa da fira cikin tsananin kauna da kulawa har saida Zainab takawo Masa abincin Rana ta jera a kan dining yaci tareda Aqeel din kafin ya kirata tazo ta tafi da Aqeel din shikuma ya wuce tareda Maryamah data dawo Dan kaisa airport din da kanta.
Bayan tafiyarsa Hakanan daga ita har Aqeel suka koma sanyi sanyi dasu karshe dai shi Aqeel din harsaida ya kwanta zazzabi Mai karfi na kwana biyu kafin yasamu sauki a ranarda Alh Asad din yacika kwanaki biyar cif da tafiya ya dawo Amma saiya sauka Maiduguri sukai wani daurin aure daga can motacin Sauran Aminansa dasuke tareda securities ya biyo zuwa dawowa gida a hanya suka samu mummanan accident din daya dauki rayuwarsa.
Zainab da ke riƙe da AQEEL sun iso cikin falon ne daidai da lokacin da Maryamah ta zube a ƙasa da waya a hannunta batareda tagama sauraron bayaninda Alh Yusuf qanin Mahaifiyaru Alh Asad yake Mata ba Dan kuwa zancensa na farko tuni ya nauke numfashinta daga fitowa ta zube qasa a some.
Da wani irin gudu Zainab ta isa gareta tana jijjigata da hannu ɗaya, ɗaya hannun Kuma ta kasa sakin Aqeel dayake kallon mahaifiyarsa jikinsa a matuqar mace Dan kuwa har lokacin lafiyar Bata Gama dawo masaba.
Zainab ganin lamarin ya girmama yasata tashi da gudu ta dauko ruwa a fridge tadawo Tana tsoro da shakkar zubawa Antyn tata Amma Kuma batada zabi sbd Maryamah din kamar bama wani sauran Rai a jikinta Dan haka jiki na rawa ta zuba Mata ruwan.
Wani tunani ne ya haska cikin kan Zainab na cewa ko Umma ne aka bugo waya ta rasu?
Mummanan faɗuwa kirjinta yayi take ta sake shiga firgicin dayafi na farko sbd idan umma ta rasu ita shikenan batada Wanda zai tsaya Mata a rayuwa Koda kuwa Babu so Babu kulawa kamar umma.
Ba shiri ta sakewa Maryamah ragowar ruwan da ke hannunta Tana kallonta hannuwanta na rawa batama San tafara tambayar Maryamah din waye ya rasu ba.