Mijin Malama Page 6
His Excellency Abu-turab ya dubi P.a ɗinsa Hammad ganin yadda jikinsa yake ta rawa kamar wanda aka ce masa ba zasu ƙara samun mulki ba. “Your Excellency abun nan yana neman girmama, mu sanar da securities na Government house” Abu-turab dai bai ce komai a hankali ya ci gaba da takawa har zuwa tsakiyar compound na gidan nasa, ya shiga ware idanunsa akan securities ɗinsa da aka harba wanda suke kwance a ƙasa. Ya ɗaga kai ya dubi wanda yake tsaye ya juya masa baya, cikin nutsuwa ya shiga ƙarewa yaro ko matashin saurayin kallo.
Cikakken namiji ne a tsaye, ya riƙe ƙugunsa da hannu ɗaya, ɗaya hannun riƙe da bindiga ga jini yana zuba daga hannun, baƙi ne irin sosai ɗin nan fatarsa har sheƙi take gabaɗaya wuyansa zanan tattoo ne kamar wanda aka zanawa macizai, sumar kansa a cure take ta wani murmurɗe kamar indomie ta sauka har wuya, wani irin crazy jeans ne a jikinsa wanda ya yayyage ga wata Armless ɗin riga tayi fata-fata a jikinsa, siffofin mahaukaci bayyane a jikinsa. “Who are you?” Abu-turab ya tambaya cikin kakkausar murya fuska ba wasa.
Wanda aka kira da Mahaukaci gabaɗaya ya juyo, kyakkyawar bugawa zuciyar Abu-turab ya yi in his whole life zai iya cewa bai taɓa ganin kamar shi ba, zubin idanunsa ma daban yake musamman yanzu da idanun suka sauya launi babu mai iya fassara abubuwan da suke nunawa, wanda ya yi masa mugun sani shi ne zai iya me yake ji ko me yake buƙata. Sosai yake da gashin gira a cunkushe, duk baƙin da yake da shi lips ɗinsa jajir yake. Ya lumshe idanu ya buɗe akan Abu-turab,bai ce komai ba ya ci gaba da ƙare masa kallo sai kawai ya ɗauke kansa.
“Ma ka ke buƙata?” Still bai magana ba. Sai a lokacin Hammad ya ƙara so wajan suka dinga kallon mahaukacin kafin P.a Hammad ya ce
“Hi crazy man, who are you, What do you need?”
Nan ma ya daɗe yana kallon su still bai ce komai ba, Hammad ya kalli Abu-turab ya ce
“Your Excellency Wallahi Mahaukaci ne”
Abu-turab ya jinjina kai yana ƙoƙarin juyawa cikin gidan ya ji saukar muryar mahaukacin ya ce “Hhhh kai… I want my Jee back, and my son” Hammad da His Excellency Abu-turab suka kalli juna kafin Hammad ya ce
“Who’s Jee?” Yaƙi cewa komai sai ƙirjinsa dake ɗagawa. “Your Excellency na faɗa maka Mahaukaci ne, da alama ba a son ya hauro ta kadanga ba” Abu-turab ya yi jima kafin ya ce “Call securities” yana faɗin hakan ya juya zai koma cikin gida wajan Majeederh. Da sauri Mahaukacin ya sha gaban Abu-turab yana ƙare masa kallo idanunsa jajir kamar gauta cikin gurɓatacciyar Hausar shi ya ce
“Ina so Jee, i want my babe” “Are you mad? Kai ma haukaci ne?”
Shi dai babu abinda yake cewa sai “Ina so Jee, i want my Jee back babe na” His Excellency ya dubi sauran jami’an tsaron ya ce “Ku fita da shi” kafin su kama shi idanun Mahaukacin ya sauka akanta, tana riƙe da jajirin kamar kullum jikinta rufe da hijabi ya zaro dara daren idanunsa waje ya juya da sauri cikin ɗaga murya ya shiga faɗin “Jee, Jee!”
Tazarar dake tsakaninsu ya sa sam bata ji ba. Ya ƙara sauri kamar zai kifa, yana ƙoƙarin haure motar da ke parking lot aka cilla masa igiya ta ƙafa ya faɗo ƙasa, kafin ya yunƙura an sake cilla masa igiya ta harɗe hannayensa, maimakon ya yi ƙoƙarin dukan securities ɗin sai ya fara buga kansa da tarazon wajan yana faɗin
“Bebe, Jee, Malumana”
Ya dinga faɗa yana buga kansa cikin ƙaramin lokacin jini ya wanke masa fuska ya fara gani dishi dishi.
Majeederh na shirin ƙara sawa tsakiyar parking lot ta ji anyi saurin kama hannunta tare da janta baya, a tsora ce ta juya suka haɗa idanu da Abu-turab baki buɗe take kallonsa, daman shi ne? daman Gwamnan jihar su ne ya taimake ta? “Me ki ke?” Ya faɗa speaking calmly. Ta janye idanunta tare da kame kanta tana son ɓoye fuskarta ta tuna ai bata da wata sauran ƙima da daraja sai kawai ta ɗan ja baya ya tattausa murya ya ce
“Baki da lafiya Jiddo, kina son hutawa” ta juya ta kalli yadda Hammad ke kallon su haka kawai jikinta ya bata akwai wani abu ta ce
“Ni za a kashe?” Ta furta cikin kamilalliyyar muryarta. His Excellency ya buɗe ido ya ce
“No, wa zai kashe Jiddo, na samu baƙi ne da zamu yi meeting koma ciki ko?” Haka kurum ta ji ta yarda da shi kuma ta san waye shi yana kyakkyawar mu’amala ta juya shi kuma ya bi bayanta, tana ɗaga ƙafa zata shiga ƙofar ta ji an ce “Malumana” cak ta tsaya ƙirjinta na bugawa zuciyarta na harbawa a ranta ta ce “Little Son”
Zata juya ya yi saurin faɗin “Meke faruwa?”
Ta ɗan yi jam can ta ce
“Na ji murya” ya ce “A voice?” Bata saurare shi ba ta juya shi ma ya juya har ya sha gabanta ya ce “Akwai jama’a, mu koma ba wata murya, ba wanda ya san kina ciki” ya lallaɓata tayi cikin gidan tana shiga ya rufe ƙofar ya sanya securities a jikin door ɗin.
Yana komawa ya samu ana dambe da shi ya yi jina jina da jikinsa “Duk sanda ya ƙara zuwa shoot him, kuyi masa duka” shigowar wata mota ya sa suka tsaya wasu ma’aikatan asibiti suka fito da wani dattijo wanda yake sanye da ƙatuwar sarƙa mai zanan kurus. David ya haɗe hannu alamar apologies ya ce “Sorry” Abraham sosai ya gane David domin shi ne babban Pasto ya jinjina kai kawai. David ya ce “His name is Abraham Daniel David, My grandson ya samu depression har ya zama taɓin hankali, na yi mamakin yadda na’urar jikinsa ta nuna mana nan, duk yadda akai akwa abinda yake nema, baya zuwa waje babu dalili duk haukansa”