Latest Updates

Anyita ta kare : ASUU zata shiga yajin aiki, amma na jan kunne na wata guda Read more: https://hausa.legit.ng/news/1455905-yanzu-yanzu-asuu-ta-shiga-yajin-aikin-jan-kunne-na-wata-guda/

Sponsored links

 Bayan dogon zaman da kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU tayi cikin daren Litinin, majalisar zartaswar kungiyar ta amince za a tafi yajin aikin jan kunnen gwamnatin tarayya a amsa bukacinsu.


Vanguard ta ruwaito wata majiya daga cikin ganawar cewa ASUU ta yanke wannan shawara ne don baiwa Gwamnatin Tarayya damar yin abinda ya kamata ko kma su tafi yajin aikin din-din-din.


A cewar majiyar: 


“Kawai muna son baiwa gwamnati dama ne don tayi abinda ya dace domin hana yajin aikin din-din-din. Mu ma fa iyaye ne kuma ‘yayanmu na karatu a jami’o’in amma ba zamu zuba ido harkar ilimi ta lalace a kasar nan ba.”


“Muna wannan gwagwarmaya ne amfanin kowa, dukkanmu zamu ji dadi ida aka gyara. Manyan masu fada aji sun sanya bak amma da alamun gwamnati bata shirya ba. Shugabanmu zai yi bayani ga yan jarida an jima.” Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button