Daudar Gora Book 2 Page 96
DAUDAR GORA…
Zaune take kan gado tun bayan idar da sallar magrib da Jasrah ta taimaka mata tayi kafin ta wuce. Idanunta tsaye suke kyam a waje
guda alamar tayi matukar zurfi a tunani, dan sam hankalinta ma baya a cikin duniyar mutane,
ya tafi ga yanda zata shawo kan uwa ne kwai da kuma gusar da Iffah datai kane-kane a cikin
rayuwar danta, dan tasan abinda uwa ta fada babu fashi bazasu taba canja sharadinsu ba inhar bata karasa cika alkawransu ba. Ita mai bada labari ce akan bijirewar da surikinsu
(Tajwar Abdul-majeed) yay da abinda ya biyo bayan hakan, dan har yanzu hukuncin uwa na biye da su daki-daki wanda shine ma
makasudin komai akan kanta yanzu haka da tushen faruwar komai akanta. Tun dazun gaba
daya hankalinta a tashe yake. Tana ta kokarin kiranyen uwa amma babu alamar zata ziyarceta,wannan shine mafi zama kololuwar tashin
hankalinta a yanzu. Motsi da kamshinsa ya sata dago manyan idanunta farare tas da a yanzu
launinsu gaba daya ya koma jazur har baka iya gane bakin ma da kyau. Duk da fushin da take
da shi bai hanata jin sanyi da ganinsa ba a cikin ranta, dan da gaske shine abu mafi kololuwar
soyuwa a gareta a kaf abinda take ganin ta mallaka a diniva KAfesa tai dA kallo rike da so da kauna, sai dai tana kokarin dannewa a zahirance. Wani irin harbawa zuciyar Iffah da girarta ta dama sukayi a lokaci guda, tai saurin ja ta tsaya da kokarin son janye hannunta da ke a cikin nasa. Amma sai yaki sakinta har sai da suka isa gaban Malikat Bushirat da sai yanzu ta lura da Iffah da ke faman boyewa a bayansa
Hannunta ya jawo a hankali ta dawo gabansa idanunsa akan Malikat din dake wani irin
kallonsa. Sassanyan murmushi ya saki kadan dai-dai yana sakin hanun Iffah’r da kaiwa duke
ya kamo na Malikat Bushirat ya saka na Iffah ciki sannan ya ja da baya zuwa bakin gado ya zauna
abinsa tamkar baiga kallon da Ammien tasa ke masa ba. A wani zafi Malikat Bushirat ta yarfar
da hannun Iffah’r tana watsa mata mummunan kallo. Iffah da kanta ke wani irin yamutsawa tun
shigar hanunta cikin na Malikat Bushirat din ta bude idanunta da suka kada jajur. Amma sai taki
kallon kowa a cikinsu tama risinar da kanta da fadin “Ammie ina yini?”.
Ta fada ranta a matukar bace tana maida kallonta ga Tajwar Eshaan maimakon amsa war da Iffah tai mata. Shiru kamar ba Adi ba, ran Malikat Bushirat ya kara sos matuka, duk da sanin halinsa ne dama hakan. Sai da ya mula dan kansa sannan ya dubeta yana dan guntun murmushin daya sake harzuka Ammien tasa. A hankali ya motsa lips dinsa yana lumshe idanu da budewa. “Ammie! Munzo mu baki hakuri ne, ta kuma dubaki.
“Hakuri? To nace mata ina bukatarsa ne.Saiful-malik ka fita idanafa ko. Ka fita idona karka bari akan yarinyar nan mu samu matsala da kai. Ita bata kai matsayin da zata zama kO abin kallona ma balle har a saurari wani abu daga bakinta. K! Tashi ki fitar min anan, karna sake ganinki a cikin idanuna, inba hakaba sai kinyi nadamar sake maimaita wanna kuskuren.