Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 93

Sponsored links

sai jiya dai da ƙyar ta ce min akan matarka ne, tace ka saketa amma ka share ko zancen baka sake tadawa ba, ta nema iso gareka ance ka shige ciki a jiya after isha’i. Ni dai na bata haƙuri da nuna mata abi komai dai a sannu kodan abubuwan da suka faru na rasa matanka da kai idan kuma akace ka saki wannan haka ɓakatatan ba’a kai ƙarshen case ɗin nan ba maimakon ita da bata da gaskiya sai a koma zarginka kai. Ta nuna kamar taji ma wuce, amma sai banyi barci cikin nutsuwa ba dan nasanta da saka abu a rai, shine ana idar da sallar asuba nazo dan gaisheta na sameta a ƙasa babu alamar rai tattare da ita. Na nemeka amma baka ɗaga ba, dole nai kiran amintacciyarta dan ta sanar da Mammah. Sai da ma sukazo ne muka iya ɗagata a ƙasan ni da Nina Ammarah da ƙyar, kafin a kira Doctors sukazo kanta har dai ALLAH yasa ta farfaɗo suka sake maidata barci dan tanata zabura kamar wadda ke a firgice. Sun tabbatar jininta ya hau ƙololuwa har yanama zuciyarta barazana ma. Amma dai yanzu data farka Alhamdullah Dr Aliyah tace jinin ya ɗan sauka bakamar ɗazun ba”.

 

Idanu ya kafe Malikat Bushirat ɗin kawai da su na wani tsawon lokaci, kafin ya furzar da iska cikin damuwa ya furta, “Why Ammie? Why zaki jefa kanki irin wannan haɗarin saboda ni. Kina tunanin idan wani abu ya sameki zan iya yafema kaina? Haba Ammien na, ki tausaya mun karki maidani maraya gaba ɗayana babu uwa babu uba mana. Yayin da na rasa Abbie sai nake kallon fuskarsa tare da taki a waje ɗaya, hakanne ke samun nutsuwa na share hawayen da suka kwaranyo min kafin su zubo a kowane lokaci saboda kewarsa. Banƙi biyayya gareki ba, sai dai ina son kareki da ga abinda zai iya zuwa ya dawo game da umarninki gareni. Yarinyar nan tabbas mai laifi ce, laifin data ambata da bakinta ta aikata. Sai dai kuma ni shugaba ne, tanada hakkin da zan bata kariya a yayin da akai yunƙurin cutar da ita itama akan dalilai biyu. Ita ɗin MATATA ce….” wani irin rumtse idanu Malikat Bushirat tayi, kalmar matata ce ɗin na mata wani irin sukar mashi a ƙirji, ya cigaba da faɗin, “Akwai haƙƙoƙinta a kaina dolen dole. Sannan ni Shugaba ne, banda hurumin yanke hukunci cikin fushi ga talakawana har sai nayi bincike. Sannan ma abu na ƙarshe da kike zargin ta aikata ba’ita bace ba. Zaki tabbatar da hakan kuma a zaman shari’a na uku gobe insha ALLAHU. Nayi miki alƙawarin gaggauto da sake zaman shari’ar gobe kodan mukai inda kike buƙata. Fatana dai yanzu ki kwantar da hankalinki, ki sama ranki haƙuri Eshaan ɗin ki na tare da ke ɗari bisa ɗari, mai kuma bin umarninki ne a duk sanda kika bashi, bazan taɓa zama mai bijirewa ba in har ba’a taɓa hurumin UBANGIJINA ba”….

Sam kalamansa babu abinda suke kara mata sai suka a zuciya, Amma sai ta dake ta daga masa kai kawai tana dan murmushin karfin hali. Tare da kai hanunta saman fuskarsa ta shafa da fadin, “ALLAI yay maka albarka”. A hankali.

 

Murmushi ya mata shima a karo na biyu yana mai lumshe idanunsa da budewa lokaci guda ya ce, “Amin nagode Ammie, ALLAH ya kara miki lafiya da tsohon rai mai albarka” akan lips dinsa. Da ga haka ya dauka shayin da ya samu Jasrah a bata ya cigaba da bata da kanshi. Sha take tana kallonsa tare da kara tabbatar da zancen uwa. Dan kuwa babu abinda kake gani a tattare da shi sai nutsuwa da tarin cikar kamala. Fuskarsa kam sai shining take da daukar idon tabbatar da shi ango ga duk mai iya kallonsa. Ga wani kamshi da take i can kasa-kasa a cikin nasa da ke bata tabbacin na mace ne. Hawayen da ke sake taso mata take dannewa, dan yanzu kam tama fi bukatar kowa ya fice a barta ita daya saboda tana bukatar ganawa da wa. Dole ta samu mafia, dan bazata taba barin yaronta daya tilo ya sake kusantar mafi zama makivarta kololuwa ba. Ko zatai vawo tsirara sai taga bayan yarinyar nan, sai taga banda ya tsaya mata, sai taga yar ban wacece ita, mita taka ne haka da zata zamewa cikar burinta barazana, burin data dauka tsahon shekaru tana ginawa da kauda duk wanda ya nema shiga gabanta koda a kuskure ne.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button