Daudar Gora Book 2 Page 180
ni dai tunda burina ya cika damuwa ta kare. An shiga shirye-shiryen biki, yayinda niko keta nokewa kamar bana so dan harda kukana. Sai gashi su Abbie sun zubda makaman su sun koma lallashina. Da wanna salon nai amfani na cinye wasan akan bikina cikin kwanciyar hankali kowa na lallabani. An kawoni masarautar ruman masarauta mai abubuwan kawa da na birgewa. Duk da na tashi a gidanmu akwai kudi sai naga ashe muma yayan malam Shehu ne dukiya na’a inda take. Abu na farko da bai munba shine dole na zauna a kasan ikon Malikat Haseenat mai amsa sunan mahaifiya ga mijina, sai dai kuma babu yanda zanyi dan ta hakanne kawai zan samu yanda nake so. Na hakura na mika wuya anan dan koba komai tana nunamin kauna babu bambanci da yayanta. Abu na biyu shine Ashwaq a matsayin uwargidana wadda kowa ke jingina zamanta Malikat. Na shiga damuwa matuka a kanta tare da neman hanyoyin dakile al’amarin ta. Ban gama da itab ba aka auro Danish-Ara. Wannan shine mataki na farko da ya hada alakata da UWA. Dan tun sanda naji labarinta da dambarwar dake faruwa tsakaninta da Mammah a daura dammarar neman kusanci da ita. Nako sami nasara ta hanyar amintaccen hadimin Haysam, bayan na shaka masa makudan kudade amma ya nunamin har abada bazai ci amanar shugabansa ba, raina ya baci dan haka na koma barazana akan iyalansa, harma na aikata masa a aikace ta hanyar sakawa matarsa ta kawo min diyarsu daya da suka haifa sashena. Na tabbatar masa zan kasheta wanna shine dalilin amincemin badan yaso ba ya hadani da uwa. Na razana a ganin farko dana mata, dan mutumce mummunar gaske, da zaka iya rantsewa badaga yankin wanna kasa ta fito ba koma na dake zuciyata. A ranar batako kulani ba, hasalima korani tai wai ban shirya ba. Naji zafi amma na daure harda dukawa kasa ina bata hakuri akan laifin da ban san nayi ba. Bata dai kulanin ba haka na taso na taho. Na shiga damuwa dan tun daga wanna ranar bata sake yarda mun haduba har tsawon wata uku. A haduwa ta biyu ma dai bata kulanin ba sai da ta mula dan kanta sannan ta dubeni a kaskance da fadin, “Kije ki daina sallar la’asar dan kin shirya kasancewa da Uwa mai share kukan masu kuka”. Na mata godiya na taso. Banyi wani tunani ba na fara bin dokarta har tsawon watanni uku. Kawai wata rana sai gata da dare ayam ta bullomin ta bango. Hankalina ya tashi na tsorata amma tsawar data mun ta sani nutsuwa. Cikin jan tsaki ta furta a haka zaki iya zama tare da uwa kina matsoraciya, Sosai na dake zuciyata wajen bata amsar ni ba matsoraciya bace. Ta sake maimaita min nima na maimaita mata nawa. Munyi haka har sau uku kafin ta kyalkyale da dariya da fadin, (Ke abokiyar tafiya ce. Mike tafe dake wajen uwa?). Cikin matukar farin ciki na qyara zama, na shiga zayyano mata haihuwa nake so, dan ina son zama Malikat bawai Zawjata-almilk ko Ameera kawai ba. Ni wannan matsayin duk yamin kankanta. dariya sosai ta shiga babbagawa har sai da na koa dan haushi amma dai na hakura na shanye. (Lallai ke abokiyar tafiya ce). Ta fada tana nunani har lokacin fuskarta da sauran daiyar. Murmushi nai mata cike da jin dad. Ta cigaba da fadin, (Nice da kaina na hana Haysam haihuwa saboda abinda uwarsa ke mun, idan tana takama ita Malikat ce dan ta haifi Miran mai jiran gado na shirya tabbatar mata komai a gidan nan sai da karfin ikona yake tabbata). Hakuri na dinga bata nidai, dan babban burina kawai bukatata ta biya nidai. Cikin tabe baki ta furta, (Ai kin wanke komai yar gari, indai zaki iya bin sharadinmu ki dauka kece Malikat a wannan karnin).