Daudar Gora Book 2 Page 126
Taci gaba da saka masa ido akan hakan amma ba’a sake kuskuren kiran ba,sai dai a wasu lokuta takanji kamshin wani irin turare na mace wanda shine taji a daren jiya Haifah nayi. Ta rushe da kuka mai cin rai da zuciya. Babu abinda Malikat Bushirat keyi sai cika da batsewa, tana matukar son Jasrah a rayuwarta, sannan ga Haifah da ke matsayin kishiya da ma akwai burbushin wani abu a kasan rai na kishin zama da miji daya da sukai,duk da ita shaida ce mijinsu bai taba son Haifah k harva bata taba zama mai wata power a cikin masarautar ba shi yasa tuni bata a cikin jerin wanda suke a gabanta itama, duk da tayi aiki a kanta kamar su Malikat Ashwaq, dan acewar uwa ba’a sakaci da makiyi komai kankantarsa.
Ta tabbata Jasim da Haifah neman juna suke a bakin kowa bisa zancen Jasrah, sai abinda Tajwar Eshaan din yayi yay matukar burge ahalin
masarautar har wasu na saka masa albarka da rage jin zafinsa a zukatansu. Oho shi baima san duk anai ba, dan yana can tare da yar shilarsa suna hutawarsu. Shirunsa kuma na nufin bazai fitoba yau gaba daya kenan.
Kamar yanda Iffah ta bada umarnin gain mai kawo kayan shayin Shahan-shan an isar da sakonta. Bayan sallar la’asar tana tsaka da nazarin littafi aka sanar mata zuwansa ta hanyar wayar landline. Bataso katsewar karatun nata ba, sai dai kuma haduwa da mutumin nada nada matukar amfani dan haka ta tashi ta kimts dazun ta riga ta gama tsara shirinta yanda ya dace, dan sun tattauna da Daneen Ammarah ta kuma bata shawara duk da a farkon bayanin Iffah din jimm tayi na rashin fahimtar manufar hakan. Sai da Iffah tai mata bayani dalla-dalla dai-dai da yanda ta tsara sannan ta gamsu ta Kuma bata goyon baya dari bisa dari.
Hurumin duk wani bako a sashen Shahan-shan iyakarsa falon farko ne, wanda har va tsallake zuwa na biyu ya kai babban bako kam na musamman, balle na uku kuma da a tarihi ma bayan masu hidima Malikat Haseenat da Malikat Bushirat ne kawai suka taba iya tsallake wannan hurumin sai ko Daneen Ammarah da tai dalilin Iffah, dan Tajwar Eshaan fa bai zauna a sashen da mahaifinsa ya rayu ba. Shi da kansa mahaifin nasa yasa akai masa wannan ginin tunkan ya dawo kasar ruman. Hakan yasa har yanzu babu wani mahaluki daya san sirrikan tsarin wannan sashe sai mai shi din.
A kowane falo Iffah na samun gaisuwar girmamawa, dan ta stairs ta biyo ko’a jikinta duk da wahalar hakan, yayinda amintattun Hadiman Tajwar Eshaan da’a ka’ida basa sakkowa ko falo na biyu sai da dalili ke biye da ita. Dattijon mutum da alamu suka nuna shima din dai wani babbane dan babu wata kazamar shiga tattare da shi vav saurin mikewa domin girmamawa ga zawjata-almilk din. Iffah takai zaune tana satar kallonsa ta gefen ido batare da kowa zal iya lura da hakan ba. Rissinawa yay domin gaisheta ta daga masa hannu kawai da masa nun da wajen zama.
Sai da taja kamar minti biyu falon shiru kafin ta nisa. “Na bukaci ganinka nan ne bisa wani dalili da bai gaza biyu ba. Na farko daga yau na dakatar da kawo duk wani ganyen shayi da sunan Maleek a gidan nan. Na biyu akwai aikin da zakamin”.
Hankali tashe ya dan dubeta sai kuma ya rissinar da kansa. “Ranki ya dade ki gafarceni, wani abu ya faru ne?”.
“Komai bai faru ba. An samu sauyin sabon tsarine kawai. Shin kozan iya sanin sunayen abubuwa da ake hada kayan shayin Maleek?”
Ta bashi amsa a takaice. Da sauri ya bude jakkar gefensa ya zaro wani littafi. Da sauri daya daga cikin hadiman ta amso ta kawo mata bayan ta kai har kasa.
A dake Iffah ta amsa babu alamar wani dar tattare da ita ta fara duba littafin Kavance dan babba.
Duk da yasan babu wani abu na cutarwa a ciki tunda a sirrance kuma aka bashi ganyen shayin da ya aiko jiya da dare a tsorace yake, dan harga ALLAH gizagon wannan baiwa da kwarjininta ya cika masa ido matuka har yana jinsa a takure cikin falon ma. Da din dadawa kuma wannan shine karo na farko da akai masa irin wanna kiran ma sabanin da da sai ya hada wani samfur na sabon ganyen shayi yakan zo ya gabatar kozai birge Shahan-shan.
Kusan mintuna biyar Iffah nabin littafin daki- daki har kusan tsakkiyar, dan gajerun bayanai ne akan yanda ake hada ganyayyakin da sunayensu. Rufewa tai tare da dan dagowa ta dubesa. “Uhm komai dake anan kam bashi da wani aibu, sai dai sabaninsa daga yanzu muna bukatar fresh ganyayyakin ne. Kuma za’a dinga noma su ne a cikin masarautar nan”.
“Yanda kike so haka za’ayi ranki ya dade”. Ya fada cikin tashin hankali a bayyane. Iffah da tai kamar bata fahimcesa ba ta mike, “Ka hada duk abinda ya dace a turamin, idan na kammala da nawa shirin zan nemeka”.
“Godiya nake ya Zawjata-almilk. ALLAH ya kara miki lafiya da tsohon rai mai amfani