Latest Updates

Daudar Gora Book 1 Page 71

Sponsored links

Iyyani ta faɗa idonta akan kwanikan gaban Kaka da ya gama cin abincin data kawo masa bayan fitowarsa wanka. Kai ya jinjina mata da sakin murmushi a karan farko tun bayan shigowarsa gidan. “Alhamdulillahi wanda naci ya wadatar dani”. Kai kawai ta jinjina masa jikinta na ƙara sanyaya. Duk wanda zai sam mijinta a bayanta yake, ta san murmushin sa ba yana nufin farin ciki bane na tsantsar damuwa ce…..

“Yaya jikinta?”.

Ya katse tunaninta da abinda taketa zumuɗin san ji a bakinsa. “Alhamdulillahi da sauƙi”.

“ALLAH ya ƙara afuwa. Bara na ganta”.

Ummu na zaune shiru ta tsurama waje ɗaya idanu suka shiga. Har suka kai zaune gefenta babu alamar tana san da zuwan nasu. Kaka ya kafa mata idanu na wasu sakanni sai kuma ya kauda kai. Taɓata Iyyani tayi, ta kawo nannauyan numfashi da ɗan zabura na ganinsu a ɗakin dan da gaske bata san da shigowar tasu ba. Kaka ta kalla idanunta na cikowa da ƙwalla, sai kuma ta duƙar da kai ta fara gaishesa. A hankali ya nisa kafin ya amsa a taƙaice kamar yanda tai gaisuwar.

“Jumaimah!”.

Ya kira ainahin sunanta.

“Na’am Baba”.

Ta amsa akan laɓɓanta.

“Damuwa ko ƙuntata kai bata sauya ƙaddarar bawa. Juriya da tsantsar jarumta baya hana ƙaddarar zuwa. Haƙilo ko nuna ƙarfin iko baya ture ta a lokacin da aka so. Rauni ko rashin tawwakali bazai dawo maka da abinda dama can ba naka bane ba. Haƙuri shike samar da komai koda kuwa a zahiri yafi ƙarfin ƙarfinka”.

“Hakane Baba”.

Ta faɗa cikin rawar murya.

Murmushi ya saki da matsawa kusa da ita sosai. Ɗa a gaban iyayensa baya girma koda ace yayi furfura a saman kai. Kaka ya riƙo hanun Ummu cikin nasa, ɗayan kuma ya shafa kanta. “ALLAH yayi miki albarka. Yasa ƙaddarar su ta zama kaffara a garemu baki ɗaya.”

“Baba mun rasa su suma ko?”.

Ummu dake dubansa idanu cike da ƙwalla ta faɗa. Murmushin ya sake sakar mata. Sai kuma ya girgiza kansa da kwanto da kanta bisa kafaɗarsa. “Bamu rasa su ba, ba kuma mu fidda rai da samunsu ba”.

A hankali hawayen da suka kasa fita a idonta tsahon kwanaki suka fara sauka a kafaɗarsa…….

Mummunan mafarkin da ALLAH ya bata ikon cin galaba a cikinsa ta farka a zabure, cikin amincin UBANGIJI harshenta ya ambato addu’ar tashi daga barci kamar yanda musulinci ya ɗoramu akai. Ajiyar zuciya ta sauke da saka gefen bargon data lulluɓa ta yarce gumin da yay ma goshinta jalab, sai kuma ta sake lumshe idanu jin sautin kiran salla da take ƙyautata zaton a masallacin cikin masarautar ne. Hasken ɗakin ta kai hannu ta ƙara, ta bi ko’ina na cikinsa da kallo tamkar zataga munanan halittun data gani a cikinsa a mafarki. Rashin ganin komai a zahiri ya bata ƙarin gwiwar sakkowa a gadon ta nufi toilet. Bata damu da rashin ganin Tajwar Eshaan a ɗakin ba duk da taji Malikat Haseenat ta ambata nan ɗin matsayin ɗakin barcinsa na daren jiya. Ƙarancin shekarunta da wautarta yasa bata ɗauki tsallakewar komai ba. Abinda kawai zuciyarta ke mata kaikawo a rai shine ta tsallake daren na jiya dai koma yaya ne, ta tsallake tarihin mutuwa a daren kwana turakar dodon matsafa. Dalilin tsallakewar, ko barinta da yay da ranta ne bata sani ba, ba kuma tasan tayaya ya kamata ta sani ba. Abinda kawai take da damar yi shine buɗe kunne da idanuwa taga mizai biyo baya ga kowa da kowa. A yanzu ɗin ma tayi zaton ganin jinin kamar jiya dai, sai dai babu alamar hakan har ta kammala uzirinta tayo alwala ta fito. Tana idar da salla wani irin nannauyan barci ya dinga fisgar idanunta. Dakewa tai cikin dauriya tai zaman yin azkar, da ƙyar ta iya kammalawa barci yay mata baban fisga a wajen dole takai kwance tana ambaton sunan ALLAH. A hankali ta fara sauke numfashi alamar barcin nata mai nauyi ne….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button