Mijin Malama Page 10
Abraham ya zube gaban Uncle Isma’il ya ce “I want to convert to Islam, I want to become a Muslim, how much will I give” Uncle Isma’il da mamaki yake kallon Abraham ɗin, Yaushe ya dawo? Mene ya same shi yaga jikinsa da wannan raunin? Mene ya ja hankalin shi zuwa ga addinin Musulunci duk da sauri irin na mahaifinsa Denial, duk da kasancewar Kakansa Pasto a church ɗin da tafi ko wacce girma.
“Lafiyarka ɗaya? Mene yaja hankalinka zuwa ga Musulunci? Yaushe ka dawo?” Uncle Isma’il ya jerawa Abraham tambayoyin cike da mamakin domin kansa ya riga cushe. Abraham ya kasa cewa komai domin bashi da kalaman da za su iya fahimtar da Uncle halin da yake ciki,
But speaking the truth, he wants to be a complete, pure Muslim. Na gartaccen mutum mai tsafta. Al’amarin daya wakana akan idanunsa sun bashi malam tsoro da tu’ajujji wani abu mai sunun tsoro Abraham bai sani ba. that is the first way he will take to surprise Majeederh.
Uncle ya kalli ko’ina kafin ya tattausa murya ya ce
“Ka bari zuwa gobe sai muyi magana mu shiga ciki” Sai a lokacin cikin gurɓatacciyar Hausar shi ya ce “Uncly, Jee”
“Jee?” Uncle Isma’il ya maimaita kenan bai mance da ita ba?
“Abraham Maminka Majeederh bamu san inda take ba, we lost her” Ya faɗa cikin damuwa. Abraham ya ɗago kansa tare da saka hannunsa ya dafa cinyoyin Uncle Isma’il ya ce
“She slapped me, insulted me, said she hates me, babu ni rayuwarta abada” Baki sake Uncle Isma’il ya ce
“Ita Majeederh? Wait a ina ma ka ganta? Mene ya sanya harta mareka?” Ya ɗaga gajiyayyun idanunsa wanda babu ladama ko kaɗan a cikin su ya ce “Tana wajan Governor na garin, his prvt house” Uncle Isma’il ya dinga jinjina kai yana tunanin abinda ya kai Majeederh wajan His Excellency, mutum mai tsananin karamci da tausayin naƙasa da shi Al’ummar shi yana da tabbacin ba zai taɓa cutar da Majeederh ba. Ya duba agogon hannunsa yaga lokacin ya ja, gashi ance ma baya ƙasar yana Cameron. “dare ya riga da ya yi, gashi His Excellency ɗin ma baya ƙasar da nayi masa waya ina so contact nasa kai tsaye ba shamaki”
“Liar, yana nan infact shi ya sa a kai ni prison, a gabansa Jee ta mareni” Uncle ya yi shiru yana son fahimtar wani abu kafin ya ce “Me kayi mata?” Abraham ya ce
“Wai don na ce ni na bata ciki, am the father of her son, am the one who raped her, na rantse” maganganun Abraham su kayiwa Uncle girma a kunne ya fahimci akwai buƙatar neman Majeederh domin bai taɓa ji Abraham ya yi ƙarya ba, He is a man who stands by his words.
Uncle Isma’il ya ce “Amma me ya sa kayi haka Maminka ce fa?” Ya haɗe rai sosai yana ɓata fuska ya ce “Ni yanzu ban son Mamin, she’s my wife to be pls Uncle I need your help, Dadyna baya understanding my feelings, Jee bata duba feelings nawa” ya faɗa cikin damuwa da murya mai rauni.. “Ka aikata babban kuskure acikin tsarin addininmu na Islam, wanda ya sha bamban da naku Addinin na Christianity mabiya Yesu, a tsarin dokokin Muslunci role and regulations ga duk saurayin daya aikata Fyaɗe bulala ake masa, mai aure kuma jefe shi ake, wannan abin ƙazanta ce ma fi muni, ba zan goyi bayan haka ba Abraham, Maminka?”
Uncle ya faɗa rai ɓace. Abraham was just looking into uncle’s eye’s ya kasa bambance fari da baƙi, yana son fahimtar mene abin kuskure a tarayya da mace? Koda yake shi addinin musulunci ya sha bamban da sauran, komai nasu sai sun kawo hujja, A strong argument.
Ya dubi Uncle a lokacin baka iya gane mai idanun Bad boy ke faɗa sbd launin da suka sauya a taushashe ya ce.
“…. I Just gave her i kissed, i Little kissed on her neck, duk abinda ya faru it was a mistake”
“Mistake?” Uncle asked.
“I…. I… I am sorry Uncle”
Was the first time daya bawa wani haƙuri saɓanin Jee, yana mata abu immediately yake cewa “Sorry Malumana”
“Help” “Sai nayi bincike, idan ya tabbata dole ka amshi hukuncin Islama, bi ma’ana bulala, kuma na kafa maka sharuɗa”
“Accepted alrdy”
Uncle ya ce “Tashi muje, zan kira Dr ya duba ka”
Sai a lokacin ƙarfi yazo masa, da ƙyar ya miƙe kansa na juyawa. Cikin gidan shiru kowa ya yi barci Uncle ya nunawa Abraham wani bedroom, ya shiga ya haɗa masa warm water kana ya ɗakko masa wata jallabiya tare da barin bedroom. A daren Uncle ya kira Dr, kana ya kira Uncle Bello akan yana neman sa gobe by 11Am, daga nan ya turawa Abbu message akan umarni yake bashi gobe yazo yana nemansa.
Daga nan zama ya yi tare da buɗe system nasa ya shiga Gmail ya turawa zuwa ga email ɗin Governor Abu-turab Alƙasim na sirri akan yana buƙatar magana tare da full address da muhimmacinsa wajan Malama Majeederh Abdul’aziz Khan.
Washegari Abraham na zaune watching TV daga shi sai 3gauter da Armless mara nauyi wacce ta haska baƙar fatar jikinsa, gashin kansa sai ya yi kamar an gyara shi yadda ya cukurkuɗe kamar indomie, duk wajan ciwon anyi dressing nasa, idanunsa wanda suke always a haka He is so genius, and so romantic. Kana ganinsa kasan bashi da haƙuri zafin rai da taurin kansa, musamman physquie. Ba komai yake ɗauka ya zuba a brain nasa ba, amma ƙwaƙwalwarsa ta kasa mance ranar, komai ya faru cikin tsautsayi. Unconscious happenings, It is still fresh in his mind, he remembers it every day.
Tsaki ya ja, babu abinda yake so a yanzu kamar barasa ita ce kawai zata ɗauke masa nauyin zuciyarsa.
Jawaad ne ya shiga hannunsa zube cikin Aljihu sai Sona dake bayansa tana cewa “Yaya Jawaad ka fiya ruwa, wallahi ko matarka sai tayi da gaske zata ci kuɗinka, ni mamakin ƴan matan da suke nace maka nake tunda ba komai za su samu ba” Jawaad ya yi murmushi yana zama kusa da Abraham ya ce “Yarinya ai mu akwai kalaman soyayya, mun san ta kan mace da kalma ɗaya take nake sace zuciya, kuɗi kuma ai Abba na zuba miki acct” Sona ta ce “Ni dai ba haka bros kewa sister’s na su ba”
“A’a, ba zan goyi bayan ɓarnatar da kuɗi ba, bayan baku san ciwonsa ba” Was abinda ta ce.
“To don Allah ka bani, just 50k” “Yarinya ko ƙwandala, na aure nake haɗawa” Ta kumbura fuska duk abinda suke Abraham na jin su..
“Yaa Abraham kai bani”
Ya buɗe idanunsa ya kalli Sona, kallon ɗaya kafin ya lumshe idanu ya ce
“Nawa?” “50k”
“Done” ta buga tsalle ta ce “Yes, thank you Yaa Abraham” Jawaad ya kalli Abraham sosai ya ce “Ni ma Yaa Abraham ka bani na siyi new car”
Abraham ya watsa masa harara ya ce “Bana ƙarawa mai…..”
Ya yi shiru yana zaro idanu alamar bai san ƙarshen karin maganar ba. Jawaad ya buga dariya ya ce “Ba a ƙarawa mai ƙarfi, ƙarfi Anji Hausa fa, wai bayan kayi hijara garin Katsinawa ka je ka koyo mana wasa”
“Mene ga hausa, Sometimes there is difficulty in pronouncing some words”