Daudar Gora Book 2 Page 151
ne kawai bata tashi mana ba, dan su kam an tabbatar mana sai dai was basu ba. Eshaan bai mutu ba, ita kuma ta samu nasarar barin kurkuku, sannan mun neman Barrister
Akeem daya jagoranci kashe mana iyayenta mun rasa. Tun daga lokacin komai ya rikice mana, wasan ya fara sauya salo. Koda muka tunkari Barbushi sai ya kwantar mana hankali da cewar ya samo wata mafitar. Zai kauda mana yarinyar cikin sauki, zai kuma kwantar da Eshaan ciwo da komai sai dai a masa. Dolene a lokacin a yarda daya da ga cikinmu ya zama Shahan-shan. Wannan shine dalilin samun kaimi da ga kowannenmu na ganin ya kuma kada dan uwansa kasa. Yayinda muka cigaba da kulla makirce-makirce ga Eshaan ciki hard kashe Sayeed Khairul-Bashar da haddasa zanga-zangar mutanen kasa, da tada bomb a cikin motar Barrister Abdallah Aas, da hada videon yanda yake kashe mutane da tsafi muka Bama matarsa da tunanin zata yada duniya ta gani, amma sai duk batai haka ba…
Wata irin hayaniya ta tashin hankali ce ta tashi a kotun, musamman iyalan Sayeed Khairul-Bashar. Babban dansa yay wani irin daka tsalle sai gashi a gaban su Miran Arshaan din. Shaka ya hadasu ya kai musu, take yan uwansa suma suka iso. Da kyar aka kwaci Miran Arshaan da Miran Jasim a hannun yayan Sayeed Khairul-Bashar, dan sai da Shahan-shan ya tsawatar da kansa. Sai dai shima karfin hali kawai yake, duk da kuwa yasan abubuwa da yawa da Miran Arshaan din ya fada a yanzu ta dalilin bibiyarsu da ya rinkayi, akan su Bably kuwa randa Iffah tai masa rakon nan na ya binciko mata iyayenta a matsayin Ajmaal a ranar ya fara bibiyarsu har ya gano sune, shine kuma ya kubutar da Barrister Abdallah as da ga tashin waccan nakiyar da har yanzu mutane da yawa suke dauka ya mutu. Kisan Sayeed Khairul- Bashar ne kawai bai gama tabbatar da wanda yayisa ba sam sai yanzu da suka fada. Bayan kotun ta natsa da kyar, masu kuka nayi, masu tsine musu nayi Sayeed Hanifud-Din da gaba daya jikinsa yay sanyi ya dubi Miran Arshaan din da fadin, “Ita kuma Ameera Haifah minene alakarku kenan?”
Kallonta Miran Arshaan yay, ganin yanda ta kakkafesa da idanunta ya sashi sakin murmushi. “Duk abinda na lissafa maka anan harda ita a ciki, alakarmu ta fara kasancewa a tare ne bayan mutuwar Haysarn Akhi. Sai dai ita da Jasim tun kafin shigowarta masarautar nan suke tare. Dan ta kasance ma tarkar matarsa ce a yanda yake tarayya da ita a duk sanda ya yaso…
*Tsinanne kaima ai naga kana tarayyar da ita, kuma garama ni kafin tai aure ne, kaiko a cikin gidan nan tana matsayin matar Haysam din kake tarraya da it…
“Karya kake gatalalle, ban taba kusantar Haifah ba sai da Haysam ya rasu, ita kuma ta kawo min kanta da kanta bani a gayyato ta ba. Idan karya na mata gata nan ta misalta mana…….
Wani irin mahaukacin buga guduma Tajwar Eshaan yayi, sai da kowa ya zabura a cikin kotun har Miran Arshaan din da ya karbe Miran Jasim a fusace. Tabbas da ace idanunsa ba cikin gilashi suke ba babu abinda zai hana juyewarsu firgita kowa da ke a wajen. Sai dai fuskarsa fa tayi masifar sake tsukewa,