Sababbin Kalaman Soyayyar Zamani na 2023
Sababbin Kalaman Soyayyar Zamani na 2023
Barka Sarakunan So Da ƙauna
Yana da matukar mahimmanci masoya su iya furta kalamai masu dadi. Ba lallai iya kalmomin da aka saba furtawa ba ko kuma aka saba jinsu kamar: ina Sonki, ina kaunarki – a’a, iya magana ta yadda dadin hirarki ko hirarka kadai ya isa ka sace zuciyarta ko kuma ki sace zuciyarsa. Kamar Kalamai masu dauke hankalin masoyi ko masoyiya ta yadda zai tattara hankalinsa gareki ko kuma ta tattara hankalinta gareka. Wasu sukan rasa abin cewa yayin da suke kiran masoyansu, wasu ma sukan fara da hirar kwallo ko ta biki, wanda a fannin soyayya masoya sun fi son zantuka masu dadi da hira me dadi irin ta masoya ba hirar gari ko kuma ta fim ba. Bayyana mata yadda soyayyarta take gareka, yaba kyawun halittarta ta yadda za ta ji tamkar babu wata wadda ka taba gani ‘ya mace face ita. Ban ce a yi karya ba, amma dai a yi kalaman da za su kwantar da zuciya ta yadda ko an tuno su yayin da ake cikin bacin rai zai yi sanyi
Shawara Ga Samari ‘Yan Soyayya
1. Yi ammafani da kalaman soyayya masu
dadi da inganci a lokacin da kake
gwagwarmayar samun amincewar zuciyar
dukkan wata yarinya da ka gani kana son
mallakarta.
2. Kasance mai lissafawa tare da tauna
dukkan wata magana kafin ka furta ta ga
masoyiyarka bayan ta nuna maka
amincewarta a soyayyarka.
3. Karda ka kasance mai takura wa tare da
matsantawa a kan dole sai ta yi wani
abu da ta nuna maka bata son yi a zahiri
ko ta nuna maka alamun hakan, domin
kuwa hakan zai sanya ta fara gajiya tare
da kosawa da kai.
4. A dukkan lokacin da kake son ta yi
maka wani abu to ka gabatar mata da
bukatar ka cikin siyasa da zolaya amma
idan ka nuna mata dole to kuwa ba zaka
samu yadda kake so ba idan ka samu
an yi ma kenan.
5. Kasance mai yin dukkan wani abu da ka
san zai faranta mata ka kuma guji yin
dukkan wani abu da ka san zai kuntata
mata. Yi mata kyauta a lokacin da bata
zaton samun hakan daga wajen ka, yin
hakan zai sanya ka burgeta zai kuma
kara sanya soyayyar ka a cikin zuciyar ta.
6. Karda ka cika yi mata kyautar kudi ko
bata wasu abubuwa barkatai domin kuwa
yawan yin hakan zai sanya ka kasa
banbance cewa soyayyar gaskiya take yi
maka ko kuma kudin ka take so.
7. Mace ba ta son takura, ba ta son kafiya,
da maimaita mata abu daya, kuma ta
son ka cika kushe wani ko wata a
gabanta. Haka zalika ba ta son a duk
lokacin da kuke tare ka rika nuna kulawa
ko fifiko ko nuna wata ta fita kyau ko
wani abu makamancin haka. Mata suna
son ka rika yabon kyawunsu.
8. Sannan ka kasance mai bayyana mata
cewa ita kyakkyawa ce a duk lokacin da
kuka yi waya ko kuma kuke tare, ka rika
bayyana mata cewa muryarta na da dadi
sosai, kana samun nutsuwa a duk
lokacin da ka ji sautin muryarta, ka nuna
mata cewa ta iya kwalliya kuma tana da
tsafta.
9. A duk lokacin da kuka hadu a hira a
waya ko a zahiri ko sako ka tura mata to
lallai ka bayyana mata kana sonta kafin
ku rabu.
Na miji jigon Rayuwa!
- Burinki ki Auri namiji
- Kinyi wanka domin namiji
- Kiyi bleahing domin namiji
- Kin chanza tafiya don kinga namiji
- Kinje wajen malam domin namiji
- Kinje wajan boka domin namiji
- Kin Rame domin namiji
- Kin kasa bacci domin na miji
- Kinyi ado duk saboda namiji
- Kin Haukace akan namiji
- Ohhh Allah nagode da kayoni namiji.