Nihad Chapter 7 Hausa Novel
Throughout the day’s lecture mood din Nihad was so dull, gaba daya she wasn’t her self, Husnah tace “Nihad mu je mu ci abinci ni dai na fara jin yunwa” A takaice tace “I am not hungry” Husnah tace “C’mon babe, wai me ke faruwa ne? Gaba daya you look dull today, don Allah ki gaya min me ke faruwa” Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace “Wai har ni mutumin nan xai ma walakanci ya ajiye ma makulli ya wuce Husnah?” Husnah ta ja wani dogon tsaki tace “Ohh this? Wai wannan ne ya canxa maki mood throughout? Lallai ma, To wai meye abun damuwa, kika sani ko barin aikin ma yayi? Ni na fi tunani ya ajiye aikin ne, ba gashi da kika tambayesa wa ya bar ma motar yace maki masu shi ba, probably yayi quitting ne” Nihad dake ta kallonta tace “Sai ya rasa wanda xai ajiye ma aiki sai ni, me yasa bai kai ma Abba makullin ba, salon ayi xaton ni ce na koresa? dama babu wanda ke considering dina a gidan banda Umma, kawai so yake ya kara ja min bakin jini wajen Mumy” Husnah ta ja tsaki tace “Soo what? Idan ma ajiye aikin yayi ai hakan ke kika fi so, abinda kike ta so ne ya faru fa, karkari su gama surutunsu na kwana biyu su yi shiru, sannan a samo wani driver din wanda xa ki juya yanda kike so, ba shikenan ba?”
Nihad ta taɓe baki ta mike tana harhada material din karatunta tace “Xan tafi gida” Husnah tace “Gida kuma? Da wuri haka? Ke da nace maki xa mu je guest inn din su Bill yanxu, Kai Nihad yau da kike da full control din mota an bar maki kiyi yanda kika ga dama shine xa ki wuce gida da wuri, haba yan mata, ki bari wajajen six ki koma gidan mana” Nihad tace “Ni kawai gida xan tafi duk raina a bace yake” Husnah ta juya ido tace “Toh ai shkkn, bari in raka ki gun motar” Tare suka isa inda motar yake, Nihad ta ajiye jakanta da kayan karatunta a bayan motar, sannan ta zaga ta shiga driver seat, Husnah na tsaye har ta tada motar ta fara tafiya….. Nihad na isa gate din gidansu tayi horn, mai gadi ya fito da sauri ya bude gate din, ta shiga gidan tayi parking, sannan ta kashe motar ta sauka, kallon inda mai gadin yake tayi, ta ga shi kadai ne a wajen, ta nufi cikin gida ba tare da ta dau material din makarantar ta dake bayan mota ba, Mumy na xaune parlor da Nihal, sai Umma dake parlon ita ma duk suna kallo, ta gaida su xata wuce, Mumy tace “Bani makullin da kika amsa wajen driver daxu” Tsayawa tayi cike da mamaki tana kallon Mumy tace “Mumy wa yace ni na amsa makullin?” Umma tace “Atoh, nima dai nace baxa kiyi haka ba, amma shi algungumin yace kin amshi makulli, kuma sun yarda” Nihad tayi narai narai da ido tace “A yaushe na amshi makulli wajensa?
Wllh Umma sharri yayi min” Mumy tace “Ban tambayeki ba’asi ba, makulli nace kawai ki bani, xa kuma mu hade a daki” Nihad ta fashe da kuka tace “Ni wllh Allah ya isa wannan sharrin da yayi min, Allah ya isa tsakanina da shi munafuki kawai, ajiye min makullin fa kawai….” Throw pillow Mumy ta dauke ta jefa mata tace “Tafi ki bani waje, ga ki nan munafuka, wllh tunda haka kika xaba xa mu sa kafar wando daya dake a gidan nan, kuma daga yau kika sake driving da kanki sai dai ki canza wata uwar bani ba” Umma tace “Wai ya kike haka ne Maryam? Shikenan kai da ɗan ka baxa ka ja sa jiki ba komai ya fada maka sai ka karyatasa baxa ka goyi bayansa ba, me yasa kike fiffita bare akan naki? Wannan wace irin rayuwa ce? Ki bar ta tayi bayani ma kin ki sbda rashin adalci” A fusace Mumy tace “Bana son bayaninta, wani bayani xata min sai kace bani na haifeta ba, ko kuma ban san halinta ba, wllh daga ni har ubanki babu me irin wannan mugun hali naki don ma kiji, in har kince ke sai dai ki tuka kanki to wllh ki nemi wata uwar, kuma ai kin saba cewa a baki makullin ba wnn ne karo na farko ba, don haka babu abinda xa ki gaya min in yarda” Kuka kawai Nihad take xuciyarta na suya, ta ajiye makullin motar nan saman kujera tace “Allah ya isa karyan da ya laka min, Allah ya isa tsakanina da shi…” Tashi Mumy tayi, Nihad na ganin haka ta wuce sama da gudu, Mumy tace “Tsaya dai ki min rashin kunya” Mikewa Umma tayi ta fita daga parlon, tana fita compound ta kwalo ma Aminu kira ya taho da sauri, tace “Ina dreban nan yake?” Mai gadi yace “Ya fita ya ɗan amso abu” Tace “Toh xai dawo ya sameni” Daga haka ta juya fuu ta koma ciki. Nihad na shiga dakinta ta sa makulli ta dinga rusa kuka ta dau wayarta tayi dialing number Abba, yana fara ringing ya daga yace “Hello Dear, ina meeting i will get back to you” Ta fashe da kuka tace “Abba ni dai kawai a canza driver din nan, bana son ganinsa kuma, i can’t withstand the sight of him any longer, kawai ni dai Abba ka sallamesa” Abba ya ɗan yi shiru sai kuma yace “Why did u ask him to hand over the key to you da ya kai ki makaranta?” Nihad ta xaro ido tace “Abba wllh sharri ya min, ta yaya xan ce ya bani makulli, wllh karya yake min ni ban ce masa haka ba” Abba yace “Idan na dawo gida xa mu yi magana yanxu muna meeting ne” Daga haka ya katse wayar, kuka ta dinga yi, nobody is getting her banda Umma, wato dawowa gida yayi ya laka mata wannan uban sharrin gashi kowa ya yarda, number Farooq tayi dialing, yana dagawa shi ma ta rushe masa da kuka yace “Lafiya??” Cikin kuka tace “Yaya dama Abba ne ya dau wani sabon driver, yaya tun da ya fara aiki yake laka min sharri iri iri, yana sa Mumy na kara tsanata, wai daxu ya kai ni schl shine ya ajiye min makulli yayi wucewarsa, da ya dawo gida shine ya je yace ma su Abba da Mumy ni nace ya ajiye min makullin” Farooq yace “To ai halinki ne wannan, amsan makulli a wajen drivers kiyi driving da kanki, ke ko wani driver sai kin samu matsala da shi, haka Habibu farkon da ya fara aiki a gidan nan, why are u always having issues with everybody?
yasa ita Nihal bata ce an mata ba” Lkci daya ta hade rai, yace “Shi wannan din yaushe ya fara aiki har kika fara samun matsala da shi Nihad?” Kin cewa komai tayi, yace “Ki min magana ko in kashe wayata” Murya can ciki ciki tace “Sallah xan yi” Katse wayar yayi, ta jefar da nata wayar, wato nobody is even supporting her, then xata dau action da kanta. Tana kwance bayan tayi wanka tayi sallah wayarta ya fara ring, ta jawo wayar ganin number da ke kiranta ta mike zaune ta daga tana wara ido tace “Shine baka ce min xaka dawo ba bayan ko jiya mun yi magana” Yace “How are you?” Ta lumshe ido tace “I am fine, ya hanya?” Yace “Alhamdulillah, yaushe za mu hadu? I will be leaving for Abuja next tomorrow” Tace “Wai yau kake nufi xa mu hadu?” Yace “Toh shikenan tunda ba yau ba” Da sauri tace “Noo ba haka nake nufi ba, i only asked, okay yanxu xan shirya in fito in sha Allah” Yace “Where are we meeting?” Tace “U suggest” Yace “How about Royal park…” A hankali tace “Kasan fa an canza mana driver” Yace “Ohh really, when?” Tace “Kwanan nan” Yace “So u are not use to the new one ko?” Ta taɓe baki tace “Aa wannan dan rainin hankali ne, i don’t think we can eva get use to each other” Yace “To yanxu ya za mu yi? Sbda ke na sauka kano fa” Tace “For now pls mu hadu ko a wellcare ne, dama xan ɗan yi shopping…” Yace “Nahh, baxan iya fita don kawai in je wellcare ba, kina nufin a tsaye xan ganki sannan mu rabu?” Tace “No pls, after today i will plan where we will be meeting, ba kace next tomorrow xaka koma ba” Yace “Karfe nawa xa ki wellcare din?” Tace “Kawai shiryawa xan yi yanxu” Yace “Drivern ne zai kawo ki?” Tace “To ya xan yi shi din xai kawo ni, dama kuma Abba ya bani kudin shopping kawai dai ban je nayi ba ne har ynxu” Yace “Okay idan xa ki fito ki kirani” Tace “Tohm, i will call you” Daga haka ya katse wayar. Sosai taji xuciyarta yayi sanyi duk wani bacin rai dake tare da ita ta nema ta rasa kawai muryarsa da ta ji. Bayan ta shirya ta fito ta tafi bangaren Mumy, Tana tsaye a parlon tace “Abba ya turo min kudin shopping, cream dina da sabulu sun kare, ina son xan je in siya yanxu, sai driver yayi dropping dina a can” Mumy tace “Gobe Nihal xata je shopping xata koma makaranta, sai ki bari ku tafi tare” Nihad da gabanta ya fadi tace “Mumy bani da cream din da xan shafa ne fa, let me get even if it’s just the cream today idan ya so goben sai mu je tare, ina gama siyan cream din xa mu dawo gida” Mumy tace “Allah ya tsare, sannan kuma ki yi masa abinda kika saba, ki tabbatar tare xa ku dawo gidan nan da shi”
dai bata ce komai ba ta juya ta bude kofar dakin sannan ta fita. Tana fita compound taga bata ga drivern ba, ta tambayi mai gadi yace “Yanxun nan ya bar nan, ya shiga can bangarensu…. ” Chalet din ta nufa, ta hangosa zaune saman matakalan dake wajen waya kare a kunnensa, yana hangota ya katse wayar kuma ya ki kallonta, ta karaso babu yabo bbu fallasa tace “Hey idan ka ga dama zaka ajiyeni a well care yanxu yanxu” tana fadin haka ta juya ta bar wajen. Da ido ya bi ta, sai kuma ya mike ya ciro makullin a aljihunsa ya bi bayanta, tana tsaye compound din ta kira Aliyu, ta sanar masa gata nan xata fito, bayan ta gama wayar ta karasa ta shiga bayan motar, sai da suka hau saman titi sannan yace “Kwatance xa ki yi” Ta hade rai tace “Kai ko ina sai kace baka sani ba sai an maka kwatance, baka da Google map ne??” Yace “Ban da” Tsaki ta ja, haka ta dinga gwada masa inda xa su bi har suka iso well care, parking yayi a space da ake parking din, tayi dialing number Aliyu, yana dagawa tace “Are u inside?” Waige waige ta fara yi jin abinda yace, tace “I am also outside, where did u park?” Sauke glass tayi, lkci daya ta hangosa, murmushinsa me kyau ya sakar mata yana kallonta, xata katse wayar yayi saurin cewa “Waitt” sai ta fasa kashewa tana sauraronsa, yace “What if idan an ɗan basa wani abu mu ce ya jira mu a nan, mu je eatry… i am jet hungry” Rasa abinda xata ce masa tayi, don ta ce ma Mumy baxata dade ba, can ta saci kallon Khalil ta ga idonsa a kan Aliyu yake ko kiftawa bai yi, duk da glass din a dage yake, kuma tinted ne ba me duhu can ba, a ranta tace wannan ma yayi kama da wanda xai amshi abu idan an basa, bude motar tayi ta sauka ta nufi inda Aliyu yake, shi dai Khalil bai daina kallon Aliyu ba kamar ya ga wani halitta na daban, tana karasawa gun motar Aliyu dake ta kallonta underneath his breathe yace “Waow, baby kin kara kyau fa, tell me what is d secret” Tayi masa murmushi wanda har dimple dinta sai da ya lotsa, sauke idonsa yayi kasa, can ya zaro dollar 100 a aljihunsa yace “In bashi wannan ya jira mu a nan?” Tana kallon kudin tace “Toh kasan dai ba wai mun saba da shi bane, snn bashi da kirki fa wllh” Aliyu yace “Kudi ne baki fara basa ba shi yasa baku saba ba, yana ganin wannan yanxu xaki ga kun dawo kun dai daita kun saba”
motar yayi ya fito, walking majestically ya nufi motar, Nihad ta bi sa da kallo, Waige waige khalil ya fara yi da sauri, as if looking for an alternative kafin Aliyu ya karaso gun motar, lokaci daya kawai yayi locking motar kafin ya iso, Aliyu na karasowa ya bude motar yaji a kulle, kwankwasa glass din motar yayi, Khalil ya kauda kai duk da Aliyun ba ganinsa yake ba, Sau biyu Aliyu na kwankwasawa kafin ya daga kai ya kalli Nihad, ta buda masa hannu alamar i told u dama, mamaki ne ya cika Aliyu ya dinga kallon motar, can ya sake Kwankwasa glass din, tace “Dear just leave him ka bar wajen kawai, ba nace maka ɗan iskan yaro bane” Aliyu da ransa ya gama baci yace “Who did he think he is, da driving din da yake yi ake biyansa yake takama ko me? Waye shi yana matsayin just driver xai kulle mota yana jin ana kwankwasawa ya ki budewa, kuma ba wai bai gan ni bane” Nihad tace “Ai ban ta6a ganin mutum me karfin hali irin yaron nan ba” Aliyu yace “Look Nihad idan kika shiga school gobe xa mu hadu, i can’t stand here any longer, mood dina ya baci seriously, ba a ta6a ci min fuska irin yau ba” Nihad tayi shiru tana kallonsa duk jikinta yayi sanyi, don kana ganinsa kasan ransa yayi mugun baci da gaske, tafiya ya fara yi kawai ya koma gun motarsa ya shiga ya tada yayi zoom off, da ido khalil ya bi sa har ya hau saman titi, Nihad ta dinga kallon motar tana jin kamar ta rushe da kuka ko xata ji sauki a ranta, mutumin da tayi wata da watanni bata gani ba, shine wannan drivern xai 6ata ma rai har ya tafi?? Ta fi minti biyu tsaye kawai kallon motar take with different thought running her mind ga wani kullutu da ya tokareta a makogwaro sbda bakin ciki da takaici, a duk abubuwan da yake mata bata jin akwai wanda ya mata ciwo ya ta6a har karshen xuciyarta irin wannan, she is trying her best not to cry, don har idonta ya cicciko, kiris ya rage ta fashe da kuka a wajen, Khalil dake ta kallon duk expression da reaction dinta ya shafa kansa, sai kuma ya sauke both glasses yace “Naga kamar kin fasa siyayyan, kuma ga hadari, ni kuma bana tuki cikin ruwa ko in baki makullin in yi tafiyata??” Wani matsiyacin shegen kallo tayi masa, ta bude back seat ta shige motar ta kulle da karfi tana kara danne kukan dake cin ta, tada motar yayi, yayi reverse ya dau hanyar gida, har suka isa gida Nihad danna kukanta take, bayan yayi parking ta bude motar ta sauka ta tafi gun driver seat ta tsaya tana nunasa da yatsa tana huci tace “Sai kayi da ka sanin abinda kayi min yau wllh, kuma ni ce sanadin barin ka gidan nan, banza mahaukaci kawai talaka”