Latest Updates

Health:AMFANIN GANYEN TAFASA ( senna leaves ๐Ÿƒ ) DA YA’YANTA GA LAFIYAR DAN ADAM.

Sponsored links

 AMFANIN GANYEN TAFASA ( senna leaves ๐Ÿƒ )  DA YA’YANTA GA LAFIYAR DAN ADAM. 

AMFANIN GANYEN TAFASA ( senna leaves ๐Ÿƒ )  DA YA'YANTA GA LAFIYAR DAN ADAM.

AMFANIN GANYEN TAFASA ( senna leaves ๐Ÿƒ )  DA YA'YANTA GA LAFIYAR DAN ADAM.

Ana amfani da ganye da ‘ya’yan don yin magani. Tafasa maganin laxative ne da FDA ta amince da shi. Ana amfani da shi don magance Ulcer da kuma Cushewar da Ciki Ana kuma amfani da Tafasa ( Senna ) don maganin ciwon Ciki  (IBS), ciwon basir, da Rage Kiba.

shayin Tafasa yana dauke da anthraquinone, wanda aka sani da tasirin laxative mai ฦ™arfi. Wadannan anthraquinone kuma Yana da tasiri sosai a tsaftace hanji, wanda yake da kyau ba kawai don ba da tsarin narkewa Abinci Ba, amma har ma da shirya hanji don hanyoyin kamar colonoscopy.

Tafasa wacce muka sani a kasar Hausa wata karamar bishiya ce dake da ganye launin kore da fure da kananin โ€˜yaโ€™ya a jikinta.

Ita dai wannan bishiyar ana samunta a wurare da dama a kasashen Africa ciki harda Nigeria musamman a jihohin arewa.

A kasar India masu maganin Ayurvedic Herbal Medicines sun dauki lokaci mai tsawo suna amfani da tafasa dan yin maganin wasu kebabbun rashin lafiyoyi kamar haka :

Maganin makanta ko matsalar data shafi ta gani. A baya ga wannan matsala ta barazanar makanta, tafasa na kara lafiyar ido kama daga Yara har zuwa tsofaffi.

A dan haka sai a juri yin miyar tafasa ana ci a abinci.

Wani bincike da wasu masana tsirran itatuwa suka yi sun tabbatar da cewa Tafasa na maganin wasu cutukan da ke shafuwar babbar hanzanya (colon) da kuma taurin bahaya (constipation).

Tafasa tana maganin zafin ciki (internal heat) da kuma wanke dattin ciki da ya cushe.

Tafasa tana rage kiba dan haka wannan wata damace ga masu tumbi wadanda ke bukatar rage nauyi. sai a nemi ganyen tafasa a dake a tare da gero ayi Fura a Sha.

Ana amfani da saiwar tafasa idan suka bushe sai a dake su koma gari dan maganin cizon maciji.

Ana amfani da garin ganyen tafasa dan warkar da gyambon ciki wato ulcers.

Tafasa na maganin tsutsotsin ciki (intestinal worms)

tafasa na maganin cutukan fata kamar su kazuwa da makero da kuraje masu kaikayi ga jiki.

Tafasa na saukar da yawan zafin jiki da hauhawar jini.

Tafasa na dauke da sinadiri mai suna chrysophanic acid da sinadirin anthrone masu kashe kwayar cuta ta fungi ( Wata Cuta Ce Mai Kama Kaji )

Ganyen Tafasa na inganta lafiyar hanta. (improves liver function)

Ana amfani da ganyen tafasa ga yara kanana A lokacin Da Su ka Soma hakora (childhood teething)

ganyen tafasa na maganin zazzabi da ciwon gabobin jiki. sai a nemo ganyen a tafasa ayi surace da ruwan ko ayi wanka dashi da sanyin safiya ko yamma.

Ganyen tafasa na flushin din wasu sinadirran dake gurbata ciki (toxins)

Ya’yan tafasa na maganin cutukan sanyi kamar tari da mura musamman ga wadanda basa Jure sauyin yanayi kamar a lokacin sanyi.

Wanda yaci wani abu ko ya sha wani abu dake da alaka da Guba ( poison ) zai iya amfani garin Ya’yan tafasa insha Allahu ta ke zai amayar Da wannan gubar a cikin lokaci kuma ba zata illata shi ba da amincewar Allah.

Ganyen tafasa na maganin malaria.

Ganyen tafasa na warkar da cutukan jini (blood disoders)

ganyen tafasa na maganin cutukan ciki.

Ana amfani da garin Ya’yan tafasa a markade da mai sai a shafawa A rauni ko kuma kunar wuta.

Mai fama da basir mai haifar da zubar jini (bloody diarrhoea) sai ya tafasa ganyen tafasa ya marmasa gishiri a ruwan ya rinka tsuguno a ciki na mintuna goma ko fiye a duk sanda yaje bahaya.

Mai fama da tari sai ya ya markade ganyen a ruwan zafi ya zanka sha.

Nauyi ko ciwon mara a lokacin alโ€™ada sai ayi amfani da tafasa.

GARGADI

mai fama da gudawa ba zai sha tafasa ba.

Mace mai ciki ta kiyayi yanda ake amfani da tafasa.

Mai ciwon hanta shi ma ya kiyaye..

Dr. Sicey Siliaddeen.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button