Latest Updates

Bakon Lamari 17

Sponsored links

Ko ina na jikin Amatullah rawa yake gaba ɗaya tsoron Ummanta ya gama mamaye mata Ilahirin jikinta bakin ta ya Rufe ruf ta kasa furta koda kalma Guda ɗaya, Maganar Ummah ke tashi cikin ƙaraji wadda ta cika ɗakin baki ɗaya.

“Wallahi tunda kika kaso auren ki kika dawon gida Ni ba zan cida ke ba kuma ba zan sha dake ba Kuma ba zan miki rainon ƴaba Kuma ba zaki zauna mini a ɗakina ba, Ga ɗakin itace can na kusa da ƙofar Shigowa ki tattara ki koma can bana Buƙatar ki a kusa dani Tunda zaman gidan kike so ai gaki gashi nan yunwar Cikin kima ta ishe ki”

Tunda Ummah ta fara maganar Amatullah ta kafe ta da ido yawun bakin ta ya ƙafe hawayen ma ya daina zuba tabbas Bada ban tana da wayo Ummah ke goyata ba ada Kafin haihuwar su Hassan da tabbas tace ko Ummah ba mahaifiyarta bace tana ƙoƙarin Buɗe baki tai magana Ummah ta daka mata tsawa akan ta tashi tabar mata guri batare data Ji yadda sukai da Imran ba.

Jikin Amatullah na rawa ta ɗauke Kayanta da Iman tabar ɗakin.

Ɗakin da Umman ta umarci ta kwana aciki shita buɗe wanda yake duk ƙura ga itace aciki na girki, Ga duhu haka ta sanya zaninta a ƙasa ta kwantar da Iman wadda ta daina Kukan sai ajiyar zuciya.

Zama tai a ƙasa tana kaɗewa yarinyar sauro sabida anyi ruwa an ɗauke sauro ya sami damar Ƙyanƙyasar ƴaƴan sa.

Har akai asubah tana zaune idanunta sun bushe babu alamun Bacci Kiran sallar assalatu yayi daidai da tashin Iman wadda duk zazzaɓi ya rufe Yarinyar sai kuka take.

Da ƙarfi Ummah ta turo ƙofar tana haska Amatullah da fitila tana cewa.

“Ki sami tsumma ki toshewa ƴarki baki duk ta cika mana gida da kukan ta na jaraba sannan ki fito ki gyara Babanki daga yau na daina yi masa komai dan bazan kashe kaina ba”

Daga haka ta juya tabar ɗakin.

Amatullah ta ɗaga Iman wadda ta lura hannunta ke mata ciwo da alama faɗuwar Jiya ta saka ta bugu haka ta tura mata Nono abaki wanda yarinyar taƙi amsa sai ma gantsare war da take tana Kuma canyara kukan azabar zafin da hannunta ke mata.

Rashin sabo ga yarinta ga haihuwar ta fari ce yasa Amatullah saɓa ta a baya ta goyata wanda hannun ƴar ya kuma matsuwa azaba ta saka Iman baccin dole.

 

Haka ta fita tai alwala Batare datai sallah ba sabida Jinin biƙin dake zubo mata wanda yau suke kwanaki ashirin da biyar bai ɗauke mata ba.

 

 

 

Daga nan ɗakin Baba ta nufa taje ta gaishe dashi sannan ta fara gyara masa ɗakin wajan shidda ta kammala gyaran baba sannan ta sami Koma wa ɗakin da Ummah ta ware mata nan ma gyara wajan da zasu zauna da ƴarta tayi sannan ta fita Wajan Murhu ta nufa zata ɗora ruwan zafi.

“Lah Anaty yaushe kika zo?”

Cewar Nana dake fitowa daga ɗaki.

“Jiya da daddare”

Ta faɗa batare da sakin fuskarta ba ruwa zata ɗora mai ɗan Ɗumi dan tai wanka sai dai Fitowar Umma ta dakatar da ita wajan Ɗora ruwan wanda ta tura mata wani kurofeti tace ta dinga Duk abin da zatai na girki akai kada ta kuma taɓa mata nata takaici yasa Amatullah ta rushe da Kuka tana cewa.

“Nifa Ummah Imran ba sakina yayi ba dan kawai yace nazo gida sai ya neme ni shine duk zaki bi ki tsanan kamar bake kika haifan ba”

Wannan maganar ta fusata Ummah wadda ta ɗauki mujiya tabi Amatullah a guje wai zata duketa.

Da gudu tai ɗakin itace ta rufo ƙofa tana silalewa a ƙasa tana kuka!

“Dan ubanki ki kuma gayan wata magana akan auren ki in banyi ƙasa ƙasa dake ba Yanzu haka bashi na lafto da Yawuna zan biya daman na saka rai Imran zai mana aiken ƙarshen wata kin tashi kin kaso aurenki da bazar wa nake rawa inba ta Imran ɗin ba”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button