Shugaba kasa buhari ya yarda da kuduri hukuma maizama kanta inec
Shugaban Buhari ya amince da dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima da za ta ba da damar yin amfani da na’urar tantance sakamakon zabe a zaben 2023 a wani yunkuri na yi wa zaben garambuwal.
Kuri’u a Najeriya na fuskantar zarge-zarge saboda ikirarin magudin zabe da kuma kalubale daga kotu tun bayan da kasar ta koma kan mulkin farar hula a shekarar 1999.
Kudurin dokar ya baiwa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) damar ba da izinin watsa sakamakon zabe da kuma rijistar sunayen masu kada kuri’a ta hanyar amfani da na’urar yanar gizo domin hana magudi.
“Akwai tsare-tsare da suka cancinci yabo da za su iya kawo sauyi ga zabuka a Najeriya ta hanyar bullo da sabbin fasahohin zamani,” in ji Buhari yayin rattaba hannu kan kudirin.
“Wadannan sabbin fasahohin za su tabbatar da ‘yancin da tsarin mulki ya ba wa ‘yan kasa damar kada kuri’a da kuma yin hakan yadda ya kamata.”
Rikici kan yadda za a yi amfani da na’urar tantance kuri’u ya barke ne a majalisar dattawa a shekarar da ta gabata a yayin muhawara kan dokar, lokacin da jam’iyyar APC mai mulki ta ce INEC ta dinga tafiyar da harkokin musayar kuri’u tare da hukumar kula da harkokin sadarwa ta kasa kawai.
Hakan dai ya sa ‘yan adawa su fusata, inda suka ce matakin zai gurgunta ‘yancin kai na INEC. Daga baya majalisar dattawa ta kada kuri’ar amincewa ta bar INEC ta yanke hukunci.
Buhari, wanda aka fara zabarsa a shekarar 2015, tun farko ya yi watsi da sabuwar dokar kan shigar da ‘yan takara a zaben fidda gwani, yana mai cewa za ta saba wa dokokin jam’iyya da kuma haifar da rashin tsaro a lokacin zabe.
Tun da Buhari ya ce zai sauka ne bayan ya yi wa’adi biyu na shekaru hudu, tuni shugabannin siyasa suka fara magudin shiga takara kafin zaben watan Fabrairun 2023.
Babu wani takamammen dan takara da ya fito da zai maye gurbin Buhari, amma jam’iyyar APC mai mulki na da masu fata da dama ciki har da fitaccen tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC ta sha suka bayan sake zaben Buhari a 2019 kan ikirarin da aka yi cewa zaben bai bayyana sakamako a fili ba.
‘Yan adawar sun kalubalanci sakamakon a gaban kotu.
Buhari dai ya samu kashi 56 na kuri’un 2019, sai dai abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya shigar da kara a kotun koli game da sakamakon zaben.
Saurari karin bayani a cikin rahoton Umar Faruk Musa: