Kalaman Soyaiya Masu Kashe Jiki
Kalaman Soyaiya Masu kashe Jiki
Babu abinda ya fi soyaiya dadi duk duniya, domin ita kanta duniyar ta ginu ne akan soyaiya, wanda idan badan soyaiya ba da duniyar ba zata zauna lafiya ba. Wanda duk ya rasa Mai son shi ya yi asara mai girman gaske. Idan kana da masoyi ka samu komai. Sai dai Kuma Yana da kyau ka jajirce domin kaga cewar masoyin naka bai kubuce maka ba. Akwai hanyoyi da ake bi domin dauwamarda masoyi a wuri days, a cikin hanyoyin akwai Kalaman Soyaiya.
Masoya da dama su na zurfafa a cikin bege da shaukin juna, wani lokacin ma har sukan rasa abinda za su fada wa junan Su.
Wannan dalilin ne yasa muka zo maku da wannan qayataccen rubutu domin qara maku hikima da azanci wurin furtawa masoyan ku kalamai masu dadi.
Yanzu an wuce zamanin da mutum zai Kama ganin lefin masoyi ko masoyiyarsa. A misali idan budurwar ka ta maka laifi, Kar ka qullace ta azuciya ko ka hukunta ta akan wannan dalilin. Kana iya kace
” Darling, a zahirin gaaskiya ban ji dadin abinda kika yi mini ba. Hakan ya 6ata mini rai sosai. A matsayin ki na masoyiya ta, hakan Sam bai dace ke ba. Zan wañnan ya zama karo na qarshe da Zaki mini irin wannan laifin. Bai kamata wani Abu ya shiga tsakani na da ke ba na rashin kyauta ta wa.”
Wannan bayani zai sanya jikinta yayi sanyi, sannan Kuma qima da darajar saurayi zata qaru a wurin budurwar. Domin kuwa ita kanta tasan da cewa ka girmamata sannan Kuma ka daraja Soyaiyarku ba tare da ka so kanka ba.
Hakan ake so a samu tsakanin masoya ta kowane bangare.
Mu hadu a Kashi na biyu domin cigaban wannan mas’alar