Daudar Gora Book 1 Page 10
“Yes anyi haka, bayan kwana huɗu ma ta rasu ai. Sai daga baya aka gane ashe saurayintane ya zuba mata wani magani a ciki. Sai dai har yanzu ma ana shari’an, dan a binciken likitoci sudai sunce basuga komai ba, abokinsa kuma da suka ƙulla tare ne ya tona masa asiri, ya kuma rantse sun zuba ɗin dan tare suka sayo maganin”.
Iffah dake saurarenta tace, “Anya kuwa ba abokin na masa sharri bane?”.
“To mudai bamu san dai-daiba sai ALLAH. Grand mother ɗinmu ma ita tace dan ALLAH abar shari’ar tunda UBANGIJI mafi sani ne. Idan anje garesa shi ya rarrabe ƙarya da gaskiya”.
“Uhm gaskiya kam tayi magana mai ƙyau. To amma ni abinda ya bani mamaki, shiko wannan wane kalar maganine haka da har za’ace likitoci sun kasa ganewa, bayan kuma gashi sunce ya kakkatsa mata hanjinta da kansu.”
“K nifa abinda na fahimta kamar an sayesu ne likitocin, kin sanfa ɗan manyan mutanene yaron. Amma abokin nasa ya faɗi sunan maganin sai dai na manta”.
“Komaima zai iya faruwa indai shegun manyan ƙasar nannne, kansu kawai suka sani azzalumai. Amma ina son nasan sunan maganin dan ina son nai bincike a kansa ma ni wlhy.”
“Kedai kawai wani abun adai rufesa kawai. Uhm kina nan da shegen son bincike-binciken nan naki, anya Iffah idan ALLAH ya cika miki burinki na zama ƴar jarida bazaki addabemuba? Dan na kula har hurumin aikin jami’an tsaro zaki dinga shiga tsabar bin kwaf-kwaf ɗinki”.
“Ƴar sa ido naji, nidai kafin a tashi ki tuno sunan maganin inba hakaba zanta addabarkine”.
Ikram tai dariya tana miƙewa. “Indai wannan ne zanyi ƙoƙari. Maganin ma fa ba wani na kirki bane ba ance ana zubama ƙananun ƙwari ne dakan damu mutane a cikin gida a ruwa haka ko abinci, dan basajin warinsa sam ko ami aka zuba sai kiga sunsha ruwa da shi ko abinci.”
“To kinga koda ba bincikeba ai zai mana amfani, dama mu da muke cikin lambu kullum cikin ganin macizai dama halittu masu cutarwa iri-iri dake iya zama a cikin gida haka.”
“Eh gaskiya kuma hakane, zai ko taimaka muku insha ALLAHU”.
Kafin a tashi kuwa Ikram ta cika alƙawarin samowa Iffah sunan magani. Takoyi farin ciki har haƙwaranta na bayyana wajen murmushi irin wanda ta jima batayiba a rayuwarta. Iya kuɗin motarta ne kawai a jikinta. Dan haka ta gama tsara ƙaryar da zatai ta samu kuɗin sayen maganin idan ta koma gida. Koda ta koma gida tun kafin takai zaune ta sanarma Ummu ai an basu wani Assignment mai wahalar gaske. Gashi bata da littafin dazai taimaka mata tayi har sai ta saya. Ganin yanda tai maganar a serious yasa Ummu yimata murmushin kwantar da hankali.
“Karki damu in har ana saidawa anjima sai Hanash ya fita ya saya miki kema, ko kuma ki bincika a kayan karatun su Arfa ƙila ki samu ai”.
“Ummu basu dashi sam, dan kwanaki ma da malaminmu yay maganarsa sannan suna nan ai. Kinga da suna dashi ai da sun bani”.
“Uhm hakane kuma kam. To ki bari Hanash ɗin ya dawo sai ya dubo miki”.
“Ummu ni kawai ki bani yanzu da nayi wanka sai naje da kaina na dubo. Ƙilama daga nan na ƙara ilimi”.
“Kai Iffah kin cika fitina, kin dai san ba son yawan fitarnan taki muke ba ai”.
“Na sani Ummu, insha ALLAHU babu abinda zai faru addu’arku na biye dani, kuma ina suturce jikina idan zan fita”.
Badan hankalin Ummu ya kwanta ba ta yarda tabar Iffah ta fita. dan ta dage akan gobe ake buƙatar sukai Assignment ɗin, idan tace zata jira sai Hanash ya dawo dare zaiyi tunta sunje babbar kasuwar cinikayyar ƙarshen watane ta daular ruman kai kayan lambu. Kamar kullum tai shirinta tsaf tare da rufe duk jikinta sai idanunta kawai da ake gani. Sosai ash color na abayar jikin nata mai adon duwatsu blue masu sheƙi sukai mata ƙyau duk da ba’a iya ganin fuskarta. Cikin nutsuwarta take takunta tamkar wata tarwaɗa. Dan Iffah tun tana yarinya irin yaran nanne masu shegen iyayi da kauɗi. Tun a shekarun baya mutane kance za’ai kallon ƴammata a wajen nan, dan tafi yayunta son kyale-ƙyale da tsantseni irin na ƴan gayun mata masu ji da kansu. Da ƙafa tazo har titi duk da akwai ɗan tafiya a tsakaninsu. Ta tare abin hawa tare da sanar masa inda zai kaita.
A ƙofar katon kantin da ake saida duk wani nau’in magani daya shafi gona dana kauda mugayen halittu masu cutarwa ga mutane dakan shiga cikin gida ya sauketa. Ta biyashi kuɗinsa sannan ta shige. Kanta tsaye ta miƙa takardar data riga ta rubuta sunan maganin dan karta manta. Aka faɗa mata kuɗin ta biya suka bata. Wani irin farin ciki takeji a ranta, tunin karta koma gida babu littafi ta zama abar tuhuma ya sata cema mai abin hawan data hawo ya kaita babban shagon littatafai. Koda suka isa cewa tai ya jirata yanzu zata fito su wuce. Gargaɗi ya mata akan kuɗintafa ya ƙaru, tace babu damuwa tana shigewa.
Ganin babu yawan mutane a shagon duk da ƙatone sosai ba kuma wajen da za’ai hayaniyar da zaka san adadin mutanen wajen bane yasata ɗage niƙab ɗinta yanda zataga komai da ƙyau. Kowanne littatafai da sashensu a rubuce kuma yanda bazakasha wahalar nema ba, maimakon ta nufi inda zataga irin nata kai tsaye saita fara zagaye. Sai da ta gama kewaye-kewayenta tamkar ta manta da wanda ta ajiye a waje kafin ta tsaida hankalinta ga inda zataga littafin daya dace ta ɗauka. Surutun yara takeji kaɗan-kaɗan ta bayan inda take, ta ɗan dudduba taga babu ta inda zata leƙasu sai ta haƙura cikin taɓe baki takai hannu kan wani littafi zata ɗauka. Daga can ɓangaren ma dai-dai an kai hannu akan littafin za’a ɗauka dan duk kanta ɗaya ce, littatafan ne kawai suka rufe wanda ke can baya ganin na nan. Iffah taja, daga can ma aka ja, jin za’a fisge saboda an fita ƙarfi dama tsaho dan ita harda su ɗiɗɗishe saita fisga itama a ɗan fusace saboda gani take wani keson raina mata hankali. Ta cikin ɗan space ɗin data cire littafin ita da shi suka zubama juna idanu, haka kawai taji tsigar jikinta ta tashi duk da ita bama wani ganesa tai da ƙyau ba saboda space ɗin bawai ya buɗe da ƙyau bane. Kamilalliyar fuskarsa da dama babu wani walwala a cikinta ya ƙara tsukewa dan shiko sarai ya ganeta………..✍